Breaking News

MIJIN AMMINA NE SILA 53-54

 


✨MIJIN AMMINA NE SILA✨

(A heart touching story)



ELEGANT ONLINE WRITER'S📚✍


Page 53-54

........salatin da su Mummy suka sanya ya sa shi saurin bude idanunsa, hankali tashe kana kuma a firgice ya nufi ta, cikin zafin nama ya manna ta da kirjinsa yayinda zuciyar sa ke wani mahaukacin bugu, hawaye ke zuba kan kyakyyawar fuskar sa, duk jarumtar sa ya kasa daurewa, saboda tsananin tausayinta, daga karshe ma fashewa yayi da kuka mai sauti, ya kara kamkame Abrar a kirjinsa, gaba daya ya rasa abinda zai yi domin kwakwalwar sa ta tushe.....




Cikin karfi hali Daddy yace "abokina me kake yi haka ne? Ka bata taimakon gaggawa mana"




Sai a lokacin yayi tunanin hakan, da mugun gudu yayi hanyar saman bene ya dauko box din treatment din sa, kwanatar da ita yayi kan kujera three seater yayin da ya shiga bata taimakon gaggawa hawayen fuskar sa ya gagara tsayuwa....





Amal kuwa matsanancin nadama ne ke cin zuciyarta, ta kasa tsayar da hawayen fuskar ta, haka zalika Mummy son Abrar, tausayinta, dama nadama, su suke yi wa zuciyar ta dabaibayi, tana ji kamar hannu agogo ya dawo baya ta goge tsanar da ta yi wa Abrar ta kuma nuna mata, dan ma bata cikin hankali ta a lokacin, da da wani ido zata kalleta? gaba daya mamakin tsantsar rashin irin imani da son zuciya irin  na alhaji Shettima suke yi....




ta kai kusan awanin 4 ba ta farfado ba, kana ta fara bude idanunta, hawaye ke bin gefe da gefen fuskarta..., a cikin awanin nan  sallah kadai ke ta da su Daddy daga falon, da zarar sun iddar zasu dawo su zauna domin ganin farkawar ta...





"sannu ya jikin?"  gaba daya suka hada baki wurin fadin haka, yayinda suke yi kanta, jinjina musu kai tayi, still hawaye na cigaba da zuba kan kyakyyawar fuskar ta  da yayi fayau tashi daya, sosai kuma kanta ke mata ciwo tamkar ana buga mata guduma...




gyaran murya daddy yace"hakika Abrar kin ga rayuwa, ta SILAN MIJIN AMMINKI, mun yi matukar tausaya miki, kuma kaddarar ki ce ta zo da haka, domin mutum baya kaucewa kaddarar sa, sai dai ina so ki sani cewa babu wanda ya kai uwa son danta ko yarta a duniya, duk da Amminki ta yi kuskuren rashin sauraren ki, wanda iyaye da dama na aikata hakan, idan yayansu sun kawo musu wata magana mai muhimmanci maimakon su tsaya su yi wa maganar duba na tsanaki, amma sai su yi watsi da maganar...(izinah garemu iyaye) da wanna nake cewa kada ki yi fushi da Amminki, nasan a yanzu tana cikin matsananci damuwa da kuma kewar ganin ki, sannan idan an kwana biyu zamu je can gidan inda Ammin taku take aure kin ji ko? ".... daga kai tayi alamun "toh" yayinda take take kokarin bude baki tayi magana, amma ta kasa, girgiza mata kai Daddy yayi alamun ba sai tayi maganan ba, wayar Amal ce ta fara ringing "sweet Adam" ta gani a rubuce, dagawa tayi ya sanar da ita cewa yana jiran ta a waje domin su tafi gida, a sanyaye ta mike ta yi salama da su Mummy tana waiwayon Abrar ta fito...






"Amma Daddyn'su bai kamata a bar dan iskan mutumin nan haka ba fa, domin irinsu a cikin al'ummah masifa ce" Mummy tace cikin tafarfasan zuciya, domin ji take kamar ta ga alhaji Shettima gabanta tayi ta kwada masa lafiyayyun maruka...





Murmushi irin nasu na manyan Daddy yayi a ransa yana fadin duk shekarun mace, toh ba shakka  namiji ya fita kaifin tunani "relax mana Mummyn'su komai a nutse ya kamata mu bi shi"...


Jinjina kai tayi kawai tayi,  ba dan haka ta so ba, kallonta ta kai ga Aaban da ke ta fama hargitsa sumar sa hadi da cije tattausan labbansa, cikin tausayinsu tace " son, ya kamata ku je daki ku kwanta haka, domin tara saura" ta fada tana duba tsadadden agogan dake makale a jikin bangon dakin...



Bai ce kala ba ya nufi sama cikin sassarfa ba tare da ya ko kalli inda Abrar take ba, da kallon Abrar ta bishi yayinda hawaye masu suka cigaba da gudana a fuskar ta, gani take kamar ya daina sonta ne...



cikin tausayin ta Mummy ta kamo ta hadi da mikar da ita tsaye, kana ta kaita har saman bangaren su kana ta sauko... a hankali ta dora hannunta kan handle din kofar, ta tura ta shiga a hankali, zaune ta gan shi kansa na kasa, dauke idanunta tayi ta nufi toilet, alwala ta dauro kana ta fito ta shimfuda sallaya ta shiga rama salollin da ke kanta....



bayan ta iddar ta ninke sallayan ta ajiye in da ya dace kana ta nufi in da yake a zaune kuma har yanzu kan sa na kasa, tattausan hannuwanta ta dora a kan fararen kafafun sa, cikin kuka tace "I knew it! I knew it that zaka daina sona idan ka ji labarina, domin nasan cewa babu wanda zai iya rayuwa ko auren na a haka pure heart, babu mai auren ragowan mijin Ammina...."


Cikin sauri ya toshe mata baki ya ce "shhhh" kana ya rungumota izuwa jikinsa, yayinda ya fashe da kuka tamkar mace, ita ma Abrar kukanta ne ya karu domin har wani sama sama numfashin ta ke yi... 




Sun dau tsahon lokaci suna kukan kana ya yi karfin halin bubbuga bayanta, sosai fuskarsa ta yi jaa abunka da farin mutum, daidaita muryan sa ya yi yace "kada ki kara tunanin cewa zan bar ki ko zan rabu da ke, domin ke din rayuwa tace, ko a wani yanayi ko a wani hali na same ki, ina sonki a haka ko da maza dari ne suka keta miki mutunci ina sonki, it's you i love not your body, dan haka kada ki kara tunanin wanna maganar, abu daya nake son  ki sani cewa ina matukar kishin ki fiye da tunanin ki".... ya kara sa fadin haka yana kara rungumeta




"Ba zan kara ba, ina sonka nima, ina matukar son ka pure heart "...



Murmushi mai tafe da hawaye ya saki, matsanancin sonta, tausayinta na ratsa shi...


"ya kamata ki kwanta ki huta haka" ya fada yana mikar da ita tsaye hadi da kwantar da ita kamar jaririya, kallonsa take, kallon so da burgewa hure mata ido yayi yace "sleep" murmushi tayi kana ta rufe idanunta ba dan tana jin bacci ba, sai dan cika umarnin sa kawai.....




Bayan kwana biyu Mummy, daddy, Aaban, Hanan, Abrar suka shirya tsaf domin zuwa gidan alhaji Shettima, mota biyu su ka yi, yayinda hawaye ya kasa barin fuskar Abrar tunda suka bar gida... Bayan sun isa gidan Alhaji Shettima dake maraba, driver ya danna horn aka wangala musu yalwataccen gate din suka shiga kasancewar yau asabar suna da tabbacin cewa masu gidan na nan, kukan Abrar ne ya karu ganin ta cikin gidan, take komai ya shiga dawo mata daki daki.....



Zaune alhaji Shettima yake kan daya daga cikin kujerun falon,  ya dan yi  rama kadan, baka hango komai sai tulelen tumbinsa, yayinda ya yi  tagumi cikin damuwa, domin tun bayan barin Ammi gidan kwanciyar hankali ta kauran masa, yasa anyi nemansu, amma babu wani kyakyyawar labari har yanzu... Sallaman daya daga cikin ma'aikatan gidan ya ji, dago kansa da suka shige loko yayi ya zuba wa mai aikin nasa


"ranka ya dade kayi baki"


Cikin mamaki yace "baki?"


"Eh! suna waje nace su shigo, amma sun ki shigowa"


"Toh toh bari na fito" alhaji Shettima yace


"A fito lafiya Alhaji" mai aikin nasa ya ce yana fitowa...


Sanar da su Daddy yayi cewa alhajin na zuwa, kana ya koma bakin aikinsa... tun daga nesa ya hango wata uwa Abrar,  murmushin farinciki ya fara saki sanda ya tabattar da cewa  ita din ce "daddy's girl kece? kin tayar mana da hankali, sannu bayin Allah ku ku ka taimaki wa  diyarmu ta dawo garemu, mun gode kwarai, naji dadi tunda kin dago gida Alhamdulillah!" yace cikin damuwa yayinda yake kokarin tunkarar ta...


"Dakata! ka da ka yi tunanin yaudarar kanka Malam, domin mu ba shashashun bane irin ka da zaka rainawa hankali, a gidan uwar uwa ta zama yarka? Da yar cikin ka ce da baka yi tunanin ta ba mutuncin ta ba, dalilin daya ya sa mu ka shigo cikin gidan nan, albarkacin Ammin Abrar da a kotu zamu hadu"... Mummy tace a zafaffe kamar zata kai masa bugu, Abrar kuwa rawa jikinta ya dauka domin gani take kamar abinda ya faru da ita a baya zai Sake faruwa, cikin tausayin ta Aaban ya riko ta izuwa jikinsa yayinda yake jifan alhaji Shettima mai tumbin kosai lolz😜😂 da mugun kallon tsana da matsanancin kishin sa.



kame kame ya fara yi domin ya lura cewa sun riga sun san komai, kuma kallon daya ya musu ya tabbatar cewa su din masu hannu da shuni ne, sannan sun yi masa kwarjini ainun. 

Fuska ba alamun wasa daddy yayi gyaran murya kana yace



 "ina mahaifiyarta take?"


"uhmm...wato... uhmm.... ta..." wani mahaukacin tsawa Aaban ya yi masa yace "kana bata mana lokaci ina Ammi take!?"... sosai Abrar ta tsorata da tsawar tasa, kamkamesa tayi, shi kan shi bai yi tunanin cewa ya iya tsawa har haka ba, kokarin rarrashen kansa yayi kana ya shiga bubuga bayan Abrar, gaba daya ji yake kamar yana cikin dajin domin daga mai gidan zuwa gidan gaba ya tsane su...




wani kishin Aaban ne ke sukar alhaji Shettima, amma ya kasa nunawa saboda wani mugun tsoran Aaban din  yake ji...


"ta...ta gudu, ban san inda take ba" alhaji Shettima yace cikin rawar murya hadi da in- in -na.


Sai a lokacin Abrar ta dago kanta,  ta rushe kuka mai ta ba zuciya.


"Kai kada kayi kokarin raina mana hankali, domin kana daf da shiga hannun hukuma, ka gaya mana gaskiya ina take?" Inji Daddy



"Wallahi summa billahilazi ta gudu, za ku iya tambayar ma'aikatan gidan su gaya muku, nan ya shiga basu labarin komai.... Domin sosai alhaji Shettima yake cikin tashin hankali wanda bai yi tunanin ba



Salati suka sanya duka yayin da kukan Abrar ya zarta na dazu muryan ta har dishewa ya yi " Ammi kada kiyi nesa da ni, ki dawo mu cigaba da rayuwar mu,  ki dawo gareni Ammina!!!" ta zube kasa ta na cigaba da kukan...



Ganin cewa Abrar na cikin matsanancin damuwa yasa Daddy cewa su tafi, kana ya  kalli alhaji Shettima yace "ka saurari sammaci daga kotu....



mu hadu a gobe dan ji yadda zata kaya masoyan littafin MIJIN AMMINA NE SILA...



SHARE✔

COMMENT✔

VOTE✔

EDIT❌

No comments