Breaking News

MIJIN AMMINA NE SILA 35-36

 


✨MIJIN AMMINA NE SILA✨

(A heart touching story)


ELEGANT ONLINE WRITER'S📚✍


✍written by noorEemaan


page 35-36


cikin madaukakin mamaki shima Nadeem ya kai kallonsa zuwa gareta, tabass wanna rahilat ce, duk da ta kara shekaru akan d'a sai de tayi rama, ta wani bangare kuwa yaji  dadi da Allah ya kaddara saduwarsu, domin matarsa bata da damuwa kullum sai na tilon kanwarta da yarta, cikin sauri suka saka ta a back seat kana ya bawa motar wuta...


cikin motar ya kalli matarsa dake kuka yace "kiyi hakuri, in sha Allah zata farfado ba wani bugewa mai yawa tayi ba, dan haka zamu kaita gida mu kira doctor ya bata taimakon gaggawa" jinjina kai tayi yayinda hawaye ya cigaba da zuba a idanunta...


bayan sun isa gidan, direct part dinsu suka yi  da ita, yayinda Nadeem ya kira family doctor dinsu, cikin mintuna kalilan ya iso, taimakon gaggawa ya bata kana ya daura mata trip hadi da basu tabbacin normal zata farka in sha Allah, godiya mai yawa suka yi masa kana ya fice...



da misalin karfe shida'n yamma ammi ta farka, a hankali ta fara bude idanunta, ganinta a wani hada'ddan bedroom ya dan tsorata ta ahankali komai ya shiga dawo mata har hatsaren data yi, hawayen tausayin kansu ne ya zubo mata, ita yanzu ko wani hannu ta fada kuma?... tana cikin wanna tunanin ta ji ance "sannu Rahilat, kin tashi ya jikin?" ware ido ammi tayi cikin sauri, jin muryan da bazata taba mantawa da ita ba, murza idanunta tayi domin tabattar da abinda ta ji kuma ta gani "yaya Raheenat! kice nake gani ko gizo idanuna ke min"

ammi ta fada cikin muryan mamaki, murna, hadi da kuka...


"nice Rahilat kanwata, nice nan a gabanki, ga yaya Nadeem nan ma" yaya Raheenat ta fada tana nuna Nadeem dake gefe yana kallonsu, yayinda kwalla ta cika idanunsa.


"yaya nadeem!" 

ammi ta kira shi, sai kuma ta fashe da kuka tana rungume yayarta, ita ma yaya raheenat kukan take, kukan murnan ganin tilon yar'uwarta.


son dau tsahon lokaci suna kukan, kana Nadeem ya rarrashesu suka yi shiru, yaya raheenat na shirin yin magana suka ga an turo kofar, wani magidanci mutum ne me kama da yaya nadeem da wata mata agefensa da alama matar wanna magidancin ne, sai wani kyakyawan saurayi black beauty daga bayansu, sallama dauke a bakinsu bayan su ammi sun amsa,  wanana magidanci yace


 "Munji shigowarku tun da dadewa Nadeem, sai kuma bamu kara jin motsinku ba shiyasa muka leko muga ko lafiya?".


"hmmm yaya alkasim yau dai Allah ya hada ni da kanwata Rahilat" yaya raheenat tace cikin murna.


"babban magana matar magidancin nan ta fada ke ce mu zauna maganar babba ce"

ta fada tana kallon ammi.


"ai kuwa dai"  yaya raheenat ta fada.

 

bayan sun zauna, da gaisuwa daya wakana a tsakaninsu yaya Nadeem yayi gyaran murya hadi da cewa "da farko zamu so sanin meye ya kawo ki garin abuja, ina kuma sajeed da Abrar? amma kafin nan bari na gayamiki silan namu zuwan abuja...


"TUNA BAYA"

Wanna sunan shi yaya alkasim yayana ne wanna kuma matarsa ce anty ni'imah wanna yaronsu ne sunanshi Adam, yayana ya kasance babban kasuwa anan garin abuja, tun a cameroon ya sha zuwa akan na dawo nigeria amma naki, acewa na, nafison zaman kasata bayan wasu shekaru ya sake dawowa akan na dawo nigeria domin girma ya fara kama shi ga kuma company's dinsa na bukatar wani daze tsaya a madadinsa, ga kuma dansa adam na yin nashi aikin so baya da lokacin kula dana mahaifinsa, da taimakon yayarki dai na amince zan dawo, anayi gobe zamu tashi muka fara sauka niger domin yimiki sallama, sai de muna shigowa gate din gidan muka hadu da mahaifiyar sajeed wato surikarki, take tafara zagi hadi da ci mana mutunci, bamu yi zuciya ba muka bata hakuri akan sallama muka zo yi miki, amma matar nan taki barinmu shiga ita bata son dangin matsiyata suna shigowa gidanta, kema kina daf da barin danta da dai sauran maganganu marasa dadi haka,  ganin haka yasa muka bata number akan ta baki idan kin kira mu zamuyi miki bayyanin komai, tadai warci takarda bamu dai sani ba ko ta baki? cikin kuka ammi tace "wallahi bata bani ba"... jinjina kai yayi kana ya cigaba, haka dai muka nufo nigeria cikin rashin jin dadin ganinki da bamuyi ba, nan muka cigaba da rayuwarmu yayinda nake taimakawa yayana akan business dinsa, amma kullum yayarki bata da damuwa sai taki, bayan wasu shekaru muka sake komawa nijer a tunanin mu zuwa wanna lokacin ta sauko sai dai abun mamaki muna zuwa taki bari a budemana gate hadi dacewa ai baku gidan, bata san inda kuke ba, dan haka mu daina zuwa muna takura mata da tsiyarmu, hakika munyi matukar jin ba dadi, haka muka dawo muka cigaba da fawallawa Allah komai muna fatan wata rana mu hadu, gashi kuma Allah ya hada mu, alokacin da bamuyi zato ba wanna shine takaitacen abunda ya faru bayan rabuwarmu, dan haka munajinki yaya Nadeem ya karasa yana sakin ajiyar zuciya...


kuka dayayi matukar taba dukkanin zuciyoyinsu ammi ta fashe dashi yayinda ta ce "ni na rasa ta yanda zan fara bada labari bayan rabuwarmu, domin babu komai a ciki sai tarin, nadama, son zuciya irin tawa, a taikace basan tayaya zaku dauki labarin ba" ammi ta fada tana jan majina.


"haba Rahilat yaya zaki ce haka idan baki gaya mana ba tayaya hankalinmu ze kwanta, domin kafin motarmu ta bige ki bakya cikin nutsuwarki ki sani cewa babu dan adam daya wuce kuskure a rayuwa, dan haka gaya mana kin ji kanwata" ta karasa cikin lallama.


wani majinan ammi ta kara ja yayinda ta fara basu labari tun daga mutuwar sajeed har izuwa korar da mahaifiyar sajeed ta musu, da zuwansu cameroon, da zuwansu nigeria haduwarta da alhaji Shettima har  ma da aurensu, kukan ta ne ya karu tuno ranar da abrar ke sanar da ita cewa alhaji Shettima ya keta mata haddi amma taki amincewa, ajiyar zuciya ta sauke kana ta shiga basu labarin komai da komai babu abinda ta boye musu har izuwa yau din data kubuta a hannun alhaji shettima....


sallati suka sanya adakin gaba daya, yayinda yaya Raheenat ta shiga yiwa ammi fada sosai kamar zata kai mata bugu, kuka ammi take domin tasan ta cancanci fiye da haka, yaya Alkasim  ne yace "yi shiru haka raheenat fada baya gyara komai, a gaskiya kin tafka kuskure babba na rashin sauraran yarki, alokuta da dama yaya'yanmu kan zo mana da magana me muhimmanci, maimakon mu nutsu mu sauraresu da idon basira mu kuma yi bincike, sai muyi tsabanin hakan, yanzu ba lokacin mayar da magana bane lokacine daya kamata mu san hanyar da za mu bi domin sanin halin da yarmu take ciki... bayan mu samo yarmu zamu maka shettima a kotu domin ya sakeki, domin ba mijin aure bane, kuma koton  ta bi wa Abrar hakkinta, mu zamu tafi sai gobe in Allah ya kaimu dan haka ki huta, ki samu bacci tunda bakya jin dadin jikinki" yaya Alkasim ya fada yana mikewa yayinda matarsa ta mara masa baya, shima saurayin nan mai suna Adam ya mike ya bi iyayensa cikin tausayawa halin da ammi take ciki...



"kai fa manu ka samu matsala, ina wanna yarinyar da oga ke nema ina wanna? sam basa kama kawai kaga mutum da matarsa kace ita ce, da alama dai yau ka sha da yawa" inji kwaro


kai dallah karka raina min hankali akwai wanda ya kai ka shan giya, ni yau kwalba daya kawai na kwankwada kuma karka manta wanna yarinyar nine na saceta daga dakin datake asibiti sosai na kalleta domin baby'n tayi min dan dai kawai kayan oga ce shi yasa na yi a'yane ka gane ai na daga mata kafa"


cikin fada shima kwaro yace "toh wallahi in dai mun karasa wajen ba ita muka gani ba sai na karta maka akuyanci"....


wani kallo manu ya aika masa kana yace 'eh naji muje idan kuma itace wallahi ni oga ze bawa tsoka mai yawa cikin share dinmu" balle murfin motar suka yi suka fito sai de sam ba alamun motar Aaban awajen....

"ka gani ko? kawai ka jaza mana asara da tuni mun huta da bulayin nemanta"

nan suka shiga zage -zagen junansu...


a hankali ya riko hannunta bayan ya daidai ta sayuwar motarsa a parking lot,  ganin tana dingishi yasashi jin ba dadi har zuciyarsa, dole kafar tayi zugi ace kafar tagama tsami aka sake fama ta ai dole, a akan ma ya ga juriyarta, ahankali yake bi da ita har suka karasa cikin main falon ta dukkaninsu na zaune a palour, daddy na kallon news a tv yayinda Amal da Hanan ke danne-danne a tsadaddiyar wayarsu, mummy kuwa shiru tayi cikin tunanin sallamarsa ce ta katse musu abunda sukayi, amsawa duk sukayi, yayinda Abrar ta buyo abayansa, "abokina ina kuka je da safe haka" 

k'ura mata ido yayi kana ya sauke ajiyar zuciya hadi da cewa "dad ashe tayi tardage da dadewa ban lura ba, har kafan tayi tsami shine na kaita wurin me gyara" 

"ayya sannu Allah ya kara sauki"

ameen dad.

sanina cewa bata yarda da kowa yasa Hanan kin tashi daga zaunen tace cikin tausayawa 

"sannu bestie Abrar Allah ya baki lafiya"


mikewa mummy tayi ta nufo su yayinda duk suka bita da kallon mamaki, abrar kuwa cikin tsoro ta kara shigewa jikin Aabaan....



Share and comment pls...✔✔

Edit❌❌


NoorEemaan ce


 in sha Allah kafin magrib gobe zan sake muku sabon post.

No comments