KIBIYAR AJALI 6
BABI NA: 6_*
Mahaifin sa kuwa dama ya manyan ta, Bai da wasu sauran yan
uwa, Sai kanwar baban sa, Ita kadai ce tayi ragowa tana can cikin kauyen nan
wajajen rijiyar badamasi, Kuma ta manyanta ko gani bata yi sosai.
Baffan mu yace ya hadu da Umma ta ne a birnin, Acan gefen
gari suke. Yace hakika Umma ta tafuto daga tsatson babban gida, Domin gida ne
na malaman addinin musulunci, Domin har makarantar islamiyya suke da ita a
kofar gidan. Ba dai masu arziki bane, Amma suna da wadatar zuci. Yayan mamana
yana da makarantar allo ta almajirai. Shi dai Baffa na abunda ya kai shi birni
alokacin neman kudi yaje, Ya fara sana’ar wankau, Daga nan ya dena ya koma
sana’ar gini. Inda yake leburanci yana debewa ma’aikatan dake gini ‘kasa da
kuma ruwa. A rijiyar gidan su Umman mu yake debo ruwa, Kasancewar akwai samari
a layin, Sai ya zamto Baffan mu ya fara wanke takalma (shoe shiner) Yakan wanke
musu takalman su ya kuma goge musu har da dinke wa. Har Allah ya hada jinin su
da Yayan Ummah ta, Suka fara abota. Ta sanadiyyar yayan umma ta, Baffa yasan
Umma. Inda suka fara zumunci na yaya da kanwa, Domin abotar su da yayan umma ta
ta kara kulluwa sun zama aminai.
Umma ta tafara boko har aji biyar, Bata gama ba suka fara
soyayya da Baffa na. Baffa ya nemi auren ta aka bashi. Ya kasance Baffa yace da
yazowa da yan uwa da yan karkarar nan maganar auren sa sai suka soki zancen,
Kan ya za’ai ya auro yar boko? Bayan ba bokon yai ba? Kuma yar birni masu abun
kunya. Baffa ya toshe kunnuwan sa da surutan mutane yai biris da zancen su. Ya
auro Umma na suka dawo nan Durbun da zama. Baffa yace sam bata kyamace shi ba
ba kuma ta kyamaci yan kauyen nan ba. Suka zauna cikin lumana da kaunar juna,
Kafin ta haife ni ta haifi har jarirai uku duk suka rasu, D’aya kuma bai zo da
rai ba. Sai daga baya Allah ya azurta ta da samun ciki na, Baffa yace tasha
wahalar ciki na, Domin Sai da suka yita zuwa birni a asibiti ana kara mata
jini. Allah yasa ta haife ni lapia. Kuma tunda ta haife ni, Shikenan tayi
sallama da lapiar ta, Yau tana Lapia gobe tana gadon asibiti. Ina shekara shida
Allah ya mata rasuwa..
Malama Mardiyya ta zare tagumin da tayi tana matsar hawaye,
Nima hawayen nake. Na Kasa cigaba Sai da Malama Mardiyya ta sake tambayata
cewar,
“Kiyi hak’uri
Khadija, Allah ya jikan Umman ki da rahama, Allah ya dubi maraicin ki ya baki
miji nagari. Yanzu yan uwan mahaifiyar ki suna ina? Shin ba sunan halin da kike
ciki bane? Ko dama can mahaifin ki nada wata matar?”
Saurin girgiza kai nayi, Na fyato kakkaurar majina na katse
da wani kara a gefen kafar Malama Mardiyya kafin na cigaba da cewa,
“Yan uwan Umma ta na
can birni, Kuma duk maza ne Ita kadai ce mace a dakin su, Bayan tayi aure Baffa
yace iyayen ta sun rasu daga baya kafin a haife ni. Amma su hudu ne a wajen
iyayen su, Maza uku, Mace d’aya, Ita kenan. Akwai Kawu Hashim, Kawu Kabiru, Da
Kawu Isma’el, Sai ita Umma ta mai suna Jamila. Sun taba zuwa su duka ukun da
wata sallah, Suka bani kudi da yawa da kaya, Lokacin Baffa na ya auro Gajiyalle
walle ta kwace komai. Kinsan fa Baffa na tsoron ta yake wallahi, “Yan uwan
mahaifiya ta gaba ki dayan su ba wuri d’aya suke zaune ba, kowanne yana wani
gari shi da iyalin sa, Shi Kawu Isma’el shi kadai ne a birni inda kuka zo, Sai
Kawu Hashim shi yana garin legas, Sai Kawu Kabiru Shi kuma yana garin Jos. Duk
kanin su kowanne a tare yake da iyalin sa, Kowanne da irin aikin sa, Domin Kawu
Hashim shi malamin makaranta ne bangaren arabi a jami’ar Legas. Sai Kawu Kabiru
shi ma babban malamin sunnah ne yana kuma da makarantar kansa a garin na Jos,
“Sai Kawu Isma’el shi yana Birni. Kuma Baffa yace min babban
dan kasuwa ne shi da ake ji da shi a birnin. Wallahi da suna kula da ni fushi
sukai daga baya. Sunce Baffa ya bar musu ni yaki. Kuma yazo ya auro Gajiyalle
da wayo na sunzo ta musu rashin mutinci har ta juyewa kawu Isma’el ruwan randa
a kayan sa. Shine tun daga lokacin ba su sake zuwa ba. Amman nace idan na zama
babba walle sai naje birni wajen kawunni na..”
Malama Mardiyya ta kada kai kafin ta sake cewa,
“Yaushe aka auro
Gajiyallen?..”
Na bude baki zan bata amsa, Sai ga Malam Auwal akan mu yana
zare idanu,
“Ke tashi kije aji..”
“Zatazo Malam afuwan.
Magana muke yi mai matuk’ar muhimmanci, Kuma nima free period ce dani. Amana
hak’uri.”
Kada kai yayi ya koma Aji, Ni kuma dadi ya mamaye min kriji
jin ance bazan koma ajin ba sai anjima. Dama duk dan zaman da nayi acan ya
gundure ni, Takashi na sai ciwo yake. Cike da farin ciki na cigaba da cewa
Malama Mardiyya,
“Bayan rasuwar mahafiya ta, Na zauna a hannun Kanwar kakana
ta wajen uba. Wadda nace miki tana can b’angaren rijiyar badamasi? To na zauna
acan na tsawon shekara d’aya. Daga nan yan karkarar nan suka damu Baffan mu da
maganar ya kara aure, Ya kasa samun wadda zai aura, Shine aka hada shi da Gaji
sunanta Salamatu. Amman fa ta taba aure, Wai auren tane ya mutu, Kuma mijin
yana nan wallahi kwanaki ma ya auro wata yar kasan layin mu. Wurin gidan su
Tsalha...”
Malama Mardiyya ta kada kai tana bi na da kallo, Na sakuto
hanci na na goge a rigata kafin na cigaba da cewa,
“Toh sai baffan mu ya
auro ta, Daku na uku ne a gidan mu, D’aya dakin babu komai cikin sa, Bayan ya
auro ta sai tace wai kar ya dakko yar sa dan ba zata rike ni ba, Awajen Baba
Ladingo naji( Kanwar Kakana.) Dakyar dai Baffa ya dakko ni ya dawo dani gidan,
Shine itama ta karbo dan ta a gidan tsohon mijin ta. Tazo dashi gidan, Ya girme
mini sosai, Sunan sa Mudi. Tunda tazo gidan mu ta gaje gidan, Dakuna ukun dake
gidan mu biyu suka zama mallakin ta, D’aya nata , D’aya na Mudi. D’aya kuma na
baffan mu. Harabar gidan kuma ta mai da rabin sa turke ta zuba dabbobin ta.
D’aya dakin kuma dakin girki ne na abinci. Dake babba ne sai ta raba shi biyu
d’aya ta zuba kajin ta da zabbin ta da sauran abubuwan kiwon ta. Rabin dakin
kuma aciki nake Kwana da taburma ta,
“Tunda Baffa ya auro Gajiyalle na shiga kuncin rayuwa, Gaba
d’aya bansan farin ciki ba, Kankanuwa ta dani anman damuwa ta mun yawa, Ta
kassara Baffa na sam bashi da jarin kansa, Duk yan kadarorin sa ta cinye.
Tanata bunkasa harkar kiwon ta Shi kuma yana kara talaucewa, Har takai ta kawo
gonar sa guda d’aya ce tai ragowa, Itace yake samu yai noma mu samu na
abinci... Wannan shine takaitaccen tarihi na malama!”
Malama Mardiyya taja doguwar ajiyar zuciya ta sauke tana
girgiza kai cike da damuwa,
“SubhanAllah! Lalle
Khadija kina ganin jarabawar rayuwa kala kala. Shysa tun sanda na ganki nake
kokonton anya a hannun mahaifiyar ki kike? Ubangiji Allah ya shiga cikin
lamuran ki Khadija. Babu komai Kowa da irin tasa jarabawar kinji? Da’din ta na
gaba, In Allah ya yarda kuwa, Zaki tuno munyi zancen nan. Kina zuwa Islamiyya
kuwa?”
Nai saurin kada kai alamun a’ah! Nan ma kai ta sake girgiza
cike da tausayi murya na rawa ta sake cemin,
“Kenan baki iya
karatun addini ba Khadija?”
“Ban iya ba Malama,
Har sallah dik banayi Malama. Makarantar allon garin nan maza ne kawai keyi.
Islamiyyar kuma can alfindi masu kudi ke kai yayayen su suyi. Toh yanzu nema
mai gari yace zaku dinga koya mana ko Malama?”
“Insha Allahu kuwa!
Da yardar Allah zamu koya muku. Kisa a ranki kuma zaki iya Khadija. Da yardar
Allah kanki zai waye da komai. Duk abunda baki gane ba ki rika tambaya ta
kinji! Ki kuma dauke ni tamkar yayar ki. Kinji ko?”
“Eh Malama. Nagode Allah ya saka da alkhairi..”
“Amin.. Muje na raka ki ajin kinji? Cikin satin nan kuma zan
baki uniform kyauta da takalmi, Da kayan wanka. Kinji?”
“Nagode Malama.”
Bayanin asambuli ta min, Dama sauran abubuwan da suka shafi
harkar rubutu, Sannan ta riko hannu na, Ta raka ni har aj. Malam auwal ya zabga
min harara nima na rama harda karin gatsine gatsine.
“Wallahi karkaryaki zan yi dan bana daukar rai ni. Kizo nan
kuma ki zauna ta yadda in kinyi ba dai-dai ba in zaneki.”
Ya yi maganar yana nuna min gaba, na kalli karshen ajin naga
babu kowa kuma Uwande tana gurin tana siyar da yajin masau, can nake son na
zauna amman mutumin nan yana neman ya kwafsa min. Na rike kuguna ina cizon
leban kasa tamkar wace take shirin yin dambe.
“Ina jin dai baki ji abin da nace miki ba ko? Khadija ki
shiga hankalinki kar kisa musa kafar wando daya da ke, zo ki zauna nan gurin.”
Ganin yadda ya kafe sai akan dole sai na zauna a gaba yasa
naje na zauna ba dan zuciya ta na so ba. Yaci gaba da koyar damu gaba daya bana
fahimtar abin da yake cewa, dan tunani na da hankali na duk suna gurin Uwande
dake sai da kayan kwalam da makulashe.
“Ke Khadija tashi ki karanto min abinda na koyar daku
yanzu.” Na dafe kirji ina zaro idanuwa nace,
“Ni kuma malam! Na shiga uku ni Dije yo me naji kana
koyarwa?”
Da alama yaji matukar haushi duba da yadda ya tsuke fuska
yana min kallon tsana dan ina da tabbacin na rashin son zamana a ajin ne. Ya
sake canza min guri ya maida ni kusa da kujerar da yake zama idan ya gama
zazzagawa cikin ajin, saboda wai tsokanar na kusa dani da nake yi shine ya
hanani sauraran bayanansa. Yaci gaba da nanata mana A to Z, sauran yara suna
fada dai dai sabanin ni da wasu da muke fadin. Ah be ch dh eh af gh.. Shec ai
de ke al af-af, daga wadannan harrufan duk bana iya fada dai dai, amman daga O
zuwa karshe duk ina iya furtawa yadda suke.
“Very good Siyama, zan baki kyauta don yau kinfi kowa kokari
zoki karba.” Ya kira Siyama ya mika mata alayoyi da biskit.
“Malam nima fa nayi da karfi.” Nayi magana hankali na a
tashe ganin an bada kyauta.
“Rufe min wannan kazamin bakin naki, kinyi da karfi kina
wani Ah be. Sai ki bari idan kin iya cewa A b sai asan kin yi koda a hankali
ne.” Da zumudi nace.
“Da gaske idan nayi dai dai gobe zaka bani nima?” Ya fara
hada littattafansa yana cewa....

No comments