KIBIYAR AJALI 2
*©️®️ZAFAFA 5 2021*
(PAID NOVELS)
*BABI NA 2*
Na karbe da sauri tare da gyara tsayuwa saboda naji banza ta fadi, dan dama Nafisa ba wani cikakken wayo ne da ita ba. Turo kallabi na nayi gaban goshi tare da kama kugu ina girgiza jiki nace mata.
“Idan karya kike min wallahi duk randa na ganki sai na fasa
miki hanci, kinsan ni fa bana san alkawarin yan nefa.”
Cikin raunin murya Nafisa ta kwaso rantsuwa ta dire min tare
da kallon cikin ido na tana cewa zata bani da gaske, sannan ne na matsa mata ta
wuce nima na tafi ina dukan cinya tare da cewa.
“Hahahaha hooo ni Dije..., Dijan gala ta mai gari bazan auri
talaka ba... Kodan bakin cikin Gajiyalle matar uba.”
Nayi dariya kamar ina kusa da wani sai dai babu kowa
hasalima kowa harkar gabansa yake yi ba ruwan wani da kowa. Gaskiya chakulat
akwai dadi, tunda nasa ta a baki na naji ina neman rasa harshe na, duk a zato
na ma harshe na ya tsinko daga cikin baki na saboda zaki, tabbas ina son dadi
gashi Allah be yo ni a gidan da ake cin mai d'an maiko-maiko ba.
Kai tsaye wajan mai siyar da kan kifi naje na siyo na naira
biyar, na tsaya a gurin na dangwali yaji na cinye. Daga nan naje na siyi yajin
masau shima na naira biyar ya rage sauran goma, na hango rumfar mai gasa zabi,
wayyo Allah garin daɗi yana nesa, miyau na ya tsinke sai kawai na girgiza kai
tare da tsayawa gurin mai rogo na siyo na goma. Gefe guda na samu na zauna na
cinye tas sannan na samu randar da ake zuba ruwa, duk mai bukatar amfani da
ruwa indai bashi da kudin siyan wanda ake kulawa a farar leda to wannan ruwan
shi zaka sha, almajirai, yan garuwa, masu walda da dai sauransu duk da shi suke
amfani, haka nima naje na dauki abin diba nasha, aikuwa na saki wata katuwar
gyatsa kamar naci duniya da abinda ke cikin ta.
Kwanaki biyu da yin alkawarin mu nida Nafisa naji shiru bata
kawo min ba, bayan na gama share tsakar gidan mu da Gajiyalle ta sanya ni nayi,
na dauko mayafi na naci d'amara kamar yadda na saba yi. Da gudu na fita dan
karma ta kuma sa ni wani abun daman ga wanke-wanke nan ba'a yi ba kuma idan har
ta ganni sai ta ce ni zanyi, dan haka kai tsaye gidan su Nafisa naje, tana
zaune a tsakar gida ita da kawayenta suna wasa, gani na da tayi yasa ta saurin
mikewa ta shiga dakin Umman su. Ko tsoro banji ba haka na tsaya ina faman
girgiza kugu alamun akwai tsantsar rigima a tare da ni, can sai gata ta fito
rike da kankarar madara tana zuwa ta miko min jikinta yana rawa tace dani.
“Dan Allah Dije kiyi hakuri, tun jiya na siyo zan kawo miki
gida aka hanani fita. Gashi nan Umma ce tasa miki a cikin kankarar zobo shi
yasa ma bata narke ba har yanzu.”
Nan da nan na saki jiki tare da karɓa ina yake baki, har
cikin rai na naji dadi dan tun kwakin da Gajiyalle ta damka min a hannu ban
sake saka komai a cikin baki na ba. Na zauna wajan su muka ci gaba da wasa,
amman fa nice na zama shugaba a cikin su, domin sai naga dama ma zan bari a
taba kayan wasan kuma babu mai ce min dan me? Tun daga lokacin kuma muka zama
kawaye sosai da Nafisa, kullum ina gidan su muna wasa har ranar da Baban su ya
siyo musu talabijin ina gidan akai ta murna kansila ya siyo talabijin da
janarato.
***A duk lokacin da
naji mahaifina yana sauraron radio ko kuma idan muka je gidan su Nafisa wato
ƴar kansilan mu muna kallo a talabijin, na kan yi mafarki da kuma hasashen nima
ina ciki ana damawa dani. Babban abin da yake daure min kai shine ta ina
mutanan radio suke shiga suyi magana har a jisu radau kamar yadda muke ji? Abin
sake daurewar kan kuma shine, wadanda nake gani a talabijin, kuma kullum cikin
shiga ta alfarma, na kan ce ko a ina suke samun kaya tsala-tsala haka? dan naga
basa maimaita su idan suka sanya.
Kasan cewar baki na baya iya yin shiru akan duk abin da nake
son sani, Hakan yasa na ke yawan tambayar Bello yayan Nafisa cewar.
“Wai dan Allah Bello ya za'a yi nima idan na girma zan iya
irin wannan aiki?”
Sai ya galla min harara irin ta wulakancin nan yace min.
“Ke dalla gafara yiwa mutane shiru, uban waye ya gaya miki
jahili ko jahila suna iya yin aikin jarida? Tafi ki bawa mutane guri keda ko
fensir baki iya rikewa ba bare shiga aji d’aukar darasi.”
Ya kamata inji haushi idan ya furta min haka, amman ina wata
irin k'ek'eshasshiyar zuciya Allah ya bani da ba komai ke bata min rai ba,
musamman irin wannan da nice na tambaya. Sai na yatsina fuska na taɓe baki ina
jujjuya idanuwa, a rai na na kan ji tabbas zan iya aikin jarida koda kuwa zan
riƙewa ma'aikatan abin da suke magana dashi. Idan na koma gida na kan tambayi
Baba na.
“Shin Baffa ya zanyi na zama ƴar jarida?”
Ya kalle ni yana dariya irin tasu ta masu hangen nesa, ya
gyara zama yace dani.
“Ummi na zaki iya amman sai kin yi ilimi na zamani da na
addini.” Lokacin ina cikin duhun kai, sai na ce dashi.
“Toh Baffa a ina suke ilimin zamanin dana addinin yanzu naje
na debo san rai na?”
Baffa ya yi dariya cike da ganin wauta irin tawa.
“Ummi na kenan, su ai ba shukawa ake yi ba, kuma ba a kasuwa
ake sai dawa ba bare kije ki siyo. Karatu ne na boko dana islamiya, su zaki yi
sai ki zama ƴar jarida ko likita ko lauya da sauran su.”
Ina jin haka a lokacin nace da Baffa.
“Kai! Aradun Allah bani ba yin karatu, kullum kana zaune
cikin wani ɗaki, na taɓa ganin yadda ake zama a wani fim da muka kalla gidan
kansila, wallahi Baffa bani ba zama guri gudu kamar akuya a daure.”
Sai na tashi nayi tafiya ta na barshi a gurin, nasan yana
tausaya min kawai babu yadda zai yi min ne,
na tafi nayo faɗa ko na siya sai na samu abin da zan sawa ciki na.
<<<<>>>>> <<<<<<>>>>
Ranar wata laraba da safe misalin karfe takwas Kauyan mu ya
samu halartar wasu mutane daga can birni, su kusan goma sha huɗu suka zo a
mota, yan garin mu suka cika kofar gidan mai gari kasan cewar anan bakin suka
sauka. Mune yan sahun farko a wajan kallo, mun kasa mun kuma tsare kamar
wadanda aka tilastawa zama. Suka zauna akan tabarma suka korawa mai gari
jawabin da yake tafe dasu akan cewa za'a zo a buɗe makarantar boko a kauyan
saboda yara su samu ilimi. Tunda jama'ar kauyen mu suka ji wannan al'amarin
suka fara bijirewa suna tsinewa wanda ya bada shawara da umarnin cewa azo a
gina makarantar bokon.
”Gaskiya bama so, mu ba arnaye bane.” Na faɗa da karfi yadda
kowa sai da ya juyo yana kallo na.
”Ke! You're very very stupid, kinga sa'anninki a cikin
maganar da ake yi?”
Cewar wani mutumi da yake sanye cikin kotu (suit) sanye da
gilashi fari a idanunsa. Yadda naga yana hararata ya tabbatar min da cewar
ransa a ɓace yake da furuci na, dan haka na yi fari da ido na tare da turo baki
na gaba ina kun-kuni. Kalmar sa ta very stupid ta tsaya min a zuciya tana sani
jin wani nishad'i, duk a zato na kalmomin farin ciki ne. Mai gari ya gyara zama
ya kalli manyan dake zaune dashi wato mai unguwa, liman da dai sauransu yace.
”Ku duba wannan zancen nasu, ya kuke ganin za'a yi. Shin mu
yadda da umarnin gwamnati ko kuwa dai a barshi ba sai an yi ba tunda ba wai
sabawa mukai da irin karatun ba?”
”Beri sutufid....!”
Na faɗa bayan mai gari ya kai maganar sa karshe.
Duk suka buɗe baki suna kallo na da tsantsar mamaki a
fuskokin su. Ni kuwa ban gane ba na ci gaba da ƙirgar duwatsu ina sawa a cikin
ramin da na yi ina kirgawa. Wani saurayi da yafi kowa kankanta a cikin bakin ya
taso yazo gurina tare da kafe ni da ido yana yatsina fuska tamkar yaga kashi
yace.
”Ashe baki da mutunci?”
”Aramma da na yi maka me?”
”Ohhh! Bama kisan abin da kikai cewa mai gari ba ko? Saboda
baki da mutunci kinga saanininki a can gurin?”
Ya faɗa yana nuna da'irar da suke zaune, na gyada kai alamun
a'a ban ga sa'ana ba.
”Toh ki sake magana a gurin nan ki gani, sai na turmushe
wannan dogon hancin naki mai kama da yatsun kaza.”
Yana gama faɗa ya koma gurinsa, ya yin da yaran gurin suka
saka dariya saboda tanka min hanci da ya yi, ni kuma na dinga shafa hancin nawa
dan gano ko da gaske yake yi irin yatsun kaza ne. Haushi ya kamani da na gano
cewa rashin mutunci kawai ya yi min. Daga cewa very stupid kawai zai tanka min
halittar da Allah ya yi min. Na sake dubansa tsab daga sama har ƙasa naga shi
sam bama shi da hancin har yake tanka nawa, haushi ta ishe ni na yi kwafa dan
bani da abin cewa kuma. Can kuma ana ta kai ruwa rana tsakanin jami'an birni da
namu na gargajiya sun kafe kan cewa ba za'a kawo musu wata makaranta ba indai
ba ta addini ba, a ganin su zuwan boko zai sanya al'adun mu da tarbiyar mu zasu
lalace. Da kyar da sidin goshi Allah yasa suka yarda suka amince.
Bayan bakin sun tafi mai gari yasa aka kirawo mutanan gari
ya shaida musu duk abinda suka tattauna tare da sharaɗin cewa indai aka kammala
gina makarantar, dole kowa zai kai ɗan sa ko ƴar sa dan a koyar da su karatu.
Hmmm Ina daya daga cikin yaran da basu son makaranta, Baffa na ya kira ni ya yi
ta lallashi amman fur na ce ba zan yi boko ba dan bazan je nasha wahala ba.
Ci kawai nake ina shaƙewa saboda rashin ruwan da zan kora
dashi, gashi sai loma nake dan kara Gajiyalle ta shigo ta kwace. Sai da naci
kusan rabi na ajiye ragowar ba dan na koshi ba, a'a tausayin Baffa naji dan nasan
shi zai zo yaci shima ya kwanta. Na sake lallaɓawa na leko tsakar gidan naga
babu kowa sannan ta yi wuf na shige inda nake kwana tare da jigawa jikina kayan
wankin Gajiyalle ta yadda ba zata gane ina ciki ba. Kamar dama ɗan lokaci Allah
ya aramin sai kuwa naji muryar ta a tsakar gida tana masifa ita kadai.
”Wato wannan shegiyar yarinyar ba zata dawo gidan nan ba ko?
Daman ta saba zama a titi dan haka yau idan ta kwana a can ba wani abin tashin
hankali bane, ja'ira kawai da fuskarta kamar kwallon kwakwa.”
Ni dai tun daga nan ban sake jin muryarta ba kasan cewar
bacci mai nauyi da ya ɗauke ni. Kiran sallar farko naji an kwaro min ruwa mai
wari da doyi a jikina, gashi sanyi karara dashi, na tashi a firgice ina neman
hanyar fita.
”Ina zaki munafuka? Yau mai rabani dake a gidan nan sai
Allah dan kuwa sai na yi miki jina-jina da fatar jikin ki.”
”Dan girman Allah Gajiyalle kiyi min rai, dan Allah karki
doke ni wallahi na dena bazan sake yi miki gardama ba, kiyi hakuri.”
Wata irin bulalace da ko kaɗan bata karyewa da ita Gajiyalle
take doka na duk sanda taso. Da yake ba mutunci da tausayi gare ta ba, haka ta
zage ta dinga labtar min jiki kamar ta samu jaka. Baffa ya fito daga cikin ɗakin
sa yana son ya kwace ni amman Gajiyalle ta haɗa dashi wajan dukan tamkar wasu
ya'yanta. Sai da ta gaji dan kanta sannan ta rabu da mu. Baffa ya rungume ni a
jikinsa yana shafar baya na, duk da bai yi magana ba a zahiri, baɗininsa a bace
yake, gashi ba zai iya yi mata hukunci ba, shi kanshi wani lokacin shakkarta
yake yi.
”Gobe ma na kuma saki aiki kiyi min rashin kunya, wallahi
sai na dinga lallasaki a gidan nan marar kunya kawai. Kuma ki tashi kije ki
debo ruwa dan ko na wanke fuska ba zaki samu ba a cikin gidan nan. Tashi nace
ko nazo na sake zaneki a nan gurin.”
Baffa ya sake ni da sauri, ganin haka da nayi ne yasa ni
kuma fashewa da kuka ina tuna mahaifiya ta. Nasan da tana raye ba zata bari ayi
min wannan wulakancin ba, duk yadda za tayi sai ta sanya ni farin ciki, ba zata
zuba min ruwan dauda mai wari ba bare har ta sanya bulala a jikina, uwa akwai
daɗi duk lalacewar ta tasan muhimmancin abin da ta haifa. Na sosa cikin idona
zuciya ta na sake tsagargarewa na kalli Baffa sannan na dakko mayafi na wani
baki da kullum shine a jiki na tamkar na gado, na yi damara tare da nufar kofar
gida. Sai da nayi kamar zan ɗauki abin dibar ruwa sai kawai na ruga da gudu na
bar musu gidan.
”Bazan debo ruwan ba wallahi sai dai ayi kuli-kulin tara
sisi dani, an mai dani jakar gidan ko? Toh sai dai a yanka ni aradu dan na dena
wahala a gidan uba na, kiji ni da kyau Gajiyalle.”
Ina gama faɗa na tsaya a kofar gida, Baffa sai kira na yake
amman nayi shiru dan idan na amsa mai dani zai yi ta doke ni ba iya cewa komai
zai yi ba. Duk da cewa duhu ne garin masallacin kofar gidan liman ana ta assalatu
da yake akwai farin wata sai ban wani ji tsoro ba, haka na fara tafiya ga sanyi
saboda a jike nake iska na sake hurani naje na zauna a kofar gidan Aramma
Auwalu, da yake akwai buhun-hunan taki a wajan. Zuciya ta ce take ta hasashen
yadda zan yi na samu kuɗi yadda zan wulakanta Gajiyalle domin rashin su ne yasa
ta mai dani tamkar wata bola abar zuba datti. Ina nan zaune har Aramma Auwalu
ya fito ya wuce masallaci ba tare da na bari ya ganni ba, a gurin bacci ya kuma
ɗauke ni duk da irin iskar da take shiga jiki na.
—

No comments