Breaking News

HAYATUL MAHAYAT 55-56

 


🌸 *HAYATUL MAHAYAT* 🌸

         🦚🦚🦚🦚

               🦚🦚

                 🦚

_Story and written_

            ```By```

*NPEEDY A AJI* 


_Dedicated to_

*My yar amana*



```My Novels 

1-NAYI RAYUWA DAKE

2-SANADIN ACCIDENT

    2019

3-SAKAYYAR CUTA 

4-RUFAFFIYAR ZUCIYA

5-FURUCI MURDADDIYAR SOYAYYA

 HAYATUL MAHAYAT

         typing......✍🏻```


 *_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*




🅿 55 & 56


" Wannan Kalmar taka tanunamin cewa dagaske aure zakayi ? " Sosai ran yaya Ibrahim ya'baci yace " amma gaskiya sumayya wani lokacin hankalin ki yana tafiya yawo ko kina nufin momy zatayi miki wasane " to gaskiya ne zanyi aure kuma babu fashi dan haka kigayamin duk abinda kike bu'kata zanyi tafiya zuwa wani ayki amma se bayan zuwan amarya dan senafi samun natsuwa idan nad'anci  angonci kafin natafi idan kuma naga zaki takurama 'kanwar taki to senatafi da'ita kawai dan babu mai shiga cikin farincikina " 

Cikin fusata Aunty sumayya tace " dadyn Amfal kishiya ni !!!! wacece wannan mai ganganci da rayuwarta ? " murmushi yaya Ibrahim yayi yace " koda nagayamiki bazaki fahimtaba zakifi ganewa idan kika ganta alokacin da matsayin ku yazama d'aya ina nufin idan tasan waye Ibrahim nima nasan wacece ita 'kilama idan Allah yasa nabuga ball a seti yakasance akwai 'kaninsu Amfal wato new baby woooow Allah kanunamin wannan ranar akwai kwasar shaku shaku 🕺🏻😜


Daga haka yaya Ibrahim yami'ke had'ida rufe system d'in shi yabar parlour fad'awa Aunty sumayya tayi kan cushion tadafe kai tanajin zafi cikin zuciyar ta afili tace " lalle koma wacece zatayi kuskuran auran mijina to wallahi zansa tayi nadama mafi muni cikin rayuwarta " 


Cikin harabar skul d'insu yayi parking jawota jikinshi yayi sosai yarungumeta yanasha'kar kamshin jikinta kamo fuskarta yayi bakinshi yahad'e danata yashiga yimata kiss dandanan yafara shiga wani layi cikin dabara Rayhana tajanye jikinta danashi cikin muryar lallashi tace 


" My Noor kayi ha'kuri nakusa makara kaji " cikin sanyin jiki yamaida hannun shi kan mararshi yace " pretty kingani ko amma shikenan please idan kindawo kicema Momy zakikoma gurin mijin ki " zaro ido Rayhana tayi tace " karufamin asiri Allah bazan iyaba kai kasanar da'ita " murmushi muzaffar yayi yace " naji amma idan nasanar da'ita idan har ta tambayeki kina bu'katar hakan zakice eh ? zaro ido Rayhana tayi ta girgiza kai had'ida cewa " dan Allah kabarni nashiga lecture " ajiyar zuciya Muzaffar yasauke yace idan kinfito kikirani zanzo nad'aukeki dan banaso driver yana zuwa d'aukarki dan kinsan mijin naki akwai kishi "


Fita Rayhana tayi tanasakin murmushi binta yayi da kallo har tashiga ciki tada mota yayi yatafi yanajin zuciyar shi tayi sanyi wata hidimar yatafi ba gida yanufaba cikin dan damuwa mahaifiyar Islam tace 


" gaskiya badan maimartaba ne yanemi auran Islam dakanshiba kuma mahaifin ku ya'amince da gaskiya bazan yarda da auran ba sabida Sumayya zataga kamar munci amanar tace " 


Ta'be baki Aunty Zaliha tayi wato 'kawar Aunty Sumayya tace " wane cin amana kuma umma shifa Ibrahim shine yace yanasonta dakanshi bamune muka tura Islam akan tasa yasotaba hasalima ita Sumayya ita tanemi Islam akan taje tazauna gurin ta kuma ita dakanta tace duk namijin dayasami Islam matsayi mata gaskiya yamore to kinga zataso mijinta yamore ko umma " harararta Umma tayi tace " rufemin baki angayamiki idan za'ayima mace kishiya tana duba dangantakane ayko da cikin zuri'ar sune tofa sekinga tayi kishi kodan ke bakida ita shine zakice haka tobari mugani idan Isma'il yace zaiyi aure zakice yamore dan haka kitanadi irin amsar dazakibama Sumayya aranar dataga Islma matsayin matar mijinta "


Murmushi Aunty Zaliha tayi tace " Umma in sha Allah ni baza'ayimin kishiyaba kuma inada masoshi masu yawa wa'inda zanbama Sumayya kude kawai mucigaba da hidimar biki kuma kar wanda yabari Sumayya tasan maganar auran nan har se ranar da Islma tashiga matsayin mata " 


Girgiza kai umma tayi tana tunanin wannan lamarin zaune Samha take a parlour hannunta ri'ke da Apply sefaman zuyashi takeyi takasaci cikin mamaki muzalbil yake kallonta 'karasowa yayi yazauna kusada ita hannu yasa yashafi cikinta sannan yazauna rungumota yayi cikin tattausar murya yace 


" haba baby har yanzu kinkasa cire wannan damuwar ? kina zaune har lokacin fita aykinki yakusa wucewa amma kina zaune " ajiyar zuciya Samha tasauke sannan tace " inaga zan ajiye ayki tunda bakaso " sosai yafuskanceta yace " haba baby na kibar wannan maganar duk komi yawuce na amince da aykin ki sabida nasan banida shakka akanki dan haka tashi kishirya mufita idan ka saukeki  nise driver ya'karasa dani Office " 


Murmushi Samha tayi tami'ke cikin zuciyar ta tace ayanzu nagamsu barrister yana sonan nima yakamata nabashi kulawa


Kayane aketashigowa dasu part d'in momy set d'in akwatina 4 masu matu'kar tsada sosai Momy take mamakin irin wannan kaya cikin sanyin jiki aunty sumayya tashiga parlour zaro ido tayi sannan takalli momy kafin tace komi  muzaffar yashigo parlour kallon momy yayi ya'karasa gurinta cikin farin ciki yace 


" Momy kinga wannan kayan set  3 na  akwatinan daduk kayan ciki na Raihan ne 1 kuma gudummawata ga yaya Ibrahim kinga seya kawo nashi ahad'a akai gidan amarya dan na'kosa Raihan tasamu Aunty mai 'kaunar ta kuma momy anjima za'a shigoda set 2 nakoma  na d'aki daya naki Momyna seki za'bi irin  color dakike so d'aya na Raihan inaso acanza komi na part d'inmu nakima haka Momy se asa hadimai sufito dakomi nacikin part d'in bana bu'katar komi duk na kwashe abubuwana masu mihimmanci sauran bana bu'katar su masu saka kayan musamman suke dasu za'a kawo kayan kafin suzo se'a kwashe komi "


Farin ciki momy tayi sosai kanshi tadafa tace " Allah yayi maka albarka Muzaffar " Ameen yace cikin farinciki yafita yanufi part d'in kaka cikin damuwa aunty sumayya tace 


" Momy gaskiya muzaffar bayasona wato hadda had'a lefe wai gudummawa hmmm wato kishiyar tawa zaiyima set d'in akwati ciki dakayan lefe lalle " zama tayi rai 'bace 


Murmushi Momy tayi tace " Sumayya ay kece kika nemi 'kiyayya gurin muzaffar amma badan hakaba ay duk cikin 'kannan naki muzaffar yafi jidake amma kika takura rayuwar shi har kikasa yatsaneki kinga kuwa kece kika nemi 'kiyayya dakanki amma ko yanzu zaki'iya dawo da darajarki gareshi musamman idan kikaso Raihan " 


'Kara had'a fuska Aunty sumayya tayi jin  momy ta ambaci Raihan itako momy ko lurama batayiba sema kiran hadimai datayi akan suje susanar dasu ummi umma mamy dayaran suzo ganin lefan Raihan


Babu jimawa kowa yahad'u cikin parlour momy bud'e akwaitinan akashigayi sosai kowa yayi mamakin irin kayan da muzaffar yazubama Rayhana ciki hadda keys d'in manyan motoci guda 2 da kyautar ma'kudan kudi zuwa saban Account d'in dayabu'de mata kowa yana mamakin irin wannan dukiya da muzaffar yakashe akan Rayhana akaf tarihin masarautar HAYAT babu wadda akata'bayima lefe irin na Rayhana cikin zuciyar Arfat tace " tabbas muzaffar mallakin Raihan ne Allah kabani zaman lafiya nida mijina "


Kafin wani lokaci tuni anshiga had'a part d'in momy dana muzaffar da kaya masu matu'kar kyau da tsada kallon wayarta Zahra takeyi se faman ruri takeyi amma takasa d'agawa akaro na 4 sannan tad'aga  dagacan 'bangaran Aliyu yasauke ajiyar zuciya yace 


" haba Zahra kiji tausayina mana wallahi ina sonki har cikin raina banida burin dayawuce naganmu atare akodayaushe nayimiki al'kawarin ajeki cikin saban gidan dana gina ba cikin masarautar muba dan Allah zahra kiceci rayuwata " 


Ajiyar zuciya zahra tasauke tace " zanyi tunani " sosai Aliyu yaji dad'in kalmarta yasake cewa mai kika haifamin kuma yaya sunan shi ? " seda tayi Jim sannan tace " namiji kamar yadda kabu'kata sunan mahaifin kane ina kiranshi da Sayyid " nata gama fad'ar haka takashe kiran kallo Aliyu yabi wayar dashi wani irin sassanyan murmushi yasaki yanaji kamar yabud'e ido yaganshi gaban Zahra da Sayyid d'inshi " 


Cikin farinciki muzaffar yashiga parlour momy kallon parlour yashigayi sosai yayi matu'kar kyau shiga cikin bedroom d'in momy yayi zaune yasameta sefaman lallashin su Farooq takeyi saurin 'karasawa yayi d'aukarsu yayi cikin farinciki yace " gaskiya part d'in ki yatsaru sosai bari muje mu d'akko Momyn su takirani yanzu semun dawo momy " fita yayi tabishi da kallon farinciki 


Please kuyi ha'kuri da wannan nasan kuna jirana sosai amma dan Allah kuyimin uziri kunsan halin rayuwar kuma kunsan da bahaka abin yakeba Allah ya'karemu da lfy Ameen nagode sosai da irin kulawar dakuke bani 🤝🏻


Daga Al'kalamin.....🖊


NPEEDY A AJI 🌸🦚🌸


Comments and shire please

No comments