HAYATUL MAHAYAT 53-54
🌸 *HAYATUL MAHAYAT* 🌸
🦚🦚🦚🦚
🦚🦚
🦚
_Story and written_
```By```
*NPEEDY A AJI*
_Dedicated to_
*My yar amana*
```My Novels
1-NAYI RAYUWA DAKE
2-SANADIN ACCIDENT
2019
3-SAKAYYAR CUTA
4-RUFAFFIYAR ZUCIYA
5-FURUCI MURDADDIYAR SOYAYYA
HAYATUL MAHAYAT
typing......✍🏻```
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
🅿 53 & 54
Zama muzaffar yayi ya rungumota cikin sigar lallashi yace " karki damuwa sena kaiki skul d'in kinga Momy zatayi zaton tunda kika fita skul kika tafi "
'Dan hararar shi tayi tace " wannan shawarar batayiba bana tafiya skul sena sanar da ita se kawai yau taji haka gaskiya kanemo wata shawarar ba wannan ba " murmushi muzaffar yayi yasake cewe to idan nakaiki skul d'in idan kindawo seki dawo part d'inki kinga shikenan kin dawo wajan mijin ki "
turo baki Rayhana tayi tami'ke tace ' duk cikin shawarar ka babu mai amfani hanyar fita tanufa kallon bayanta yayi yayi saurin shan gabanta yace " pretty kinga kuwa yadda kike tafiya tabbas idan momy taganki zatayi tunanin wani abu " dafe kanta Rayhana tayi tace " waiyo Allah yaya zanyi kenan ? "
Dede lokacin wata hadima tashigo risinawa tayi ta gaidasu sannan tace " dama Momy ce tace farooq yana kuka kuma ya'ki yarda ni nakawoshi " wata irin faduwar gaba Rayhana taji juyawa tayi ta kalleshi tashagwa'be fuska tace " kenan momy tasan tasan ina nan ? "
Murmushi muzaffar yayi yace alamu sun nuna hakan kije karki nuna wata fargaba zan shigo yanzu nakaiki skul da kaina cikin sanyin jiki Rayhana tafita daga part d'in kalllo muzaffar yabita dashi yanajin wani sanyi yana ratsa cikin zuciyar shi
Ciki a sanyaye tashiga parlour momy zaune suke itada Aunty sumayya Farooq yana hannun momy se kuka yakeyi yana ganinta yarafa mi'ka hannu amsar shi tayi cikin jin kunya tanufi bedroom murmushi momy tayi har cikin ranta taji dad'in yadda Rayhana tabi mijin ta dan tasan yana bu'katar kulawar ta
Bayan shigar Rayhana ciki Aunty Sumayya tata'be baki kafin tace komi momy tace " Sumayya ki saurareni da kyau kuma bana bu'katar hauka dan nasan halinki bakibin komi ahankali Sumayya kinsan dacewa namiji mijin mace 4 ne idan har zai'iya adalci dan haka baharamun bane dan namiji yayi mace samada 1 shi yasa nike " to amma momy mai yasa kike tunamin duk wannan bacin nasan banacikin masuzama da kishiya " sabida mijinki bazai iya adalciba ? Momy tamayar mata da tambaya shiru Aunty Sumayya tayi tana tunanin ina maganar momy tadosa
Cigaba dayin magana momy tayi " Sumayya Ibrahim zai 'kara aure nanda kwanaki 10 in sha Allah Dan......." mi'kewa Aunty Sumayya tayi cikin matu'kar gigita tace " ina momy badai Dadyn Amfal ba ni kad'aice babu wadda ta'isa tana 'karashe fad'ar haka tafita afusace kallo momy tabita dashi tana mamakin irin halin Sumayya
Cikin mamaki Zahra tashigo cikin parlour momy zama tayi kusada momy tace " momy yaya Ibrahim zai 'kara aure amma abin damamaki shigowar muzaffar yasa zahra yin shiru cikin ladabi muzaffar yagaida momy batare danuna komiba ta amsa gaidashi zahra tayi cikin sakin fuska ya amsa kauda kanshi muzaffar yayi yace zahra kicema Raihan tafito lokaci yana tafiya "
Tashi Zahra tayi tanufi bedroom d'in itako Momy yitayi kamar batajishiba zahra tana shiga ta iske Rayhana zaune bakin bed tana tunani zama zahra tayi tadafata tace " lafiya kuwa Aunty Rayhana ? " murmushi Rayhana tayi tace " lafiya lau " Murmushin itama zahra tayi tace " yaya muzaffar yace kifito kutafi zaro ido Rayhana tayi tace " ya Allah yana cikin parlour nanne momy fa ? " dariya zarah tayi tace " yana ciki kuma momy tana zaune
Rumtse ido Rayhana tayi " tace nabani yaya zan iya fitowa nabishi momy tana kallo " dariya zahra tasakeyi tace itakam momy ina ruwanta dashiga tsakanin miji da mata kinga kitashi yakaiki karki shiga skul amakare dankam ni yau banida lecture " cikin sanyin jiki tami'ke bag d'inta da gyale ta d'auka tayafa tasaka wani had'add'an takalmi kallon Farooq da haidar tayi daketa bacci ajiyar zuciya tasaki tace nagode Allah sunyi bacci dayanzu senayi dabara kafin nafita "
Fitowa sukayi itada zarah kallo muzaffar yabita dashi harta isa gaban momy cikin sanyin murya tace " momy zan tafi skul su Farooq sunyi bacci " murmushi momy tayi tace " Allah yabada sa'a Allah de yasa yau bazaki dad'eba kinsan yanzu sunkoyi rigima da 'kiwa "
Murmushi Rayhana tayi tace in sha Allah juyawa tayi ganin muzaffar a zaune yasata mamaki 'karasawa tayi kusadashi tace " dadyn Haidar 10:30 fa " kallonta yayi yace ay kinfasa zuwa " zaro ido Rayhana tayi tace " kamarya hannu yasa yakama gyalanta yace " idan har dawannan zaki to sede kifasa "turo baki tayi tana niyyar yin shagwa'ba nuni yayi mata da Momy cikin sauri tanufi bedroom cire gyalan tayi tasa hijab tafito sallama sukayima momy suka fita binsu momy tayi da murmushi itako Zahra dariya tayi tace " Momy wallahi yaya muzaffar da Aunty Raihan sunyi matu'kar dacewa dan Allah momy kibashi matar shi "
Hararar ta Momy tayi tace " cemiki sukayi nice nari'kesu ga hanyanan Allah yabasu zaman lafiya " dariya zahra tayi tace " a'a momy kinsan Aunty Rayhana bazata iya komawa part d'in suba se idan kince " sake harararta momy tayi tace yanzu dataje nice nace taje kinga tashi kibani guri ina Sayyid wato kin baroma hajiya shi yadameta ko ? "
Kafin zahra tayi magana wayarta tad'auki ruri kallon momy tayi takashe kiran cikin tuhuma momy ta kalleta tace " zahra duk abinda zakiyi kisani akwai auran Aliyu akanki dukda bama tunanin komawarki wajan shi amma dole ki kiyaye tunda auranku yananan " cikin mamaki Zahra tace " Momy taya kikasan aurena da Aliyu yana nan ? "
Kallonta Momy tayi sosai tace " mahaifin shi yakira maimartaba akan cewa Aliyu yamayar dake kuma shima Aliyu yakira shi amma maimartaba yace " bazaki komaba garama ya sauwa'ke miki kawai to shine daganan basuzoba kuma basu sake kiraba muma bamu nemesuba dama munaso ki haihu ne tukun asan abinyi kicigaba da kallon kanki matsayin matar aure har zuwa lokacin dazamu yanke shawarar abinda yadace nima bangoyi bayan ki komaba sabida inda Aliyu yana sonki da yazo gidannan yafi a 'kirga amma babu shi babu alamar shi kuma ansanar ma iyayen shi haihuwar ki amma ko barka balle suzo gani jariri kinga kenan har yanzu suna nan akan bakarsu "
Daga haka momy tami'ke tabar parlour shigowar text cikin wayarta yasata maida dubanta kan wayar text d'in Aliyu ne kamar yadda tayi tsammani tamkar bazata dubaba kamar yadda tasaba sekuma tabud'e
_Assalama alaikum my dear ina fatan kin tashi lafiya dan Allah ina ro'konki kiyafemin zahra wallahi ina matu'kar sonki ina kuma farinciki da abinda kika haifamin dan nasan izuwa yanzun kin haihu amma dan Allah ina ro'kon ki kisanar dani abinda kika haifamin bana BIHAR ina Cameroon ayanzun tun washegarin danazo gurinki kuma kece silar tafiya na sabida bazan iya zama cikin 'kasar BIHAR batare da zahra ba ina matu'kar sonki daga mijin ki nahar abada Aliyu Yazeed_
Shiru Zahra tayi tana tunanin kalamanshi " kenan ma shi baisan maiye na haifaba danni yabar 'kasar shi da iyayen shi harma da aykin shi to ina matar shi ? "
Afusace Aunty Sumayya tashiga cikin parlour ta zaune tasamu yaya Ibrahim yana ayki cikin system tsaye tayi akanshi tace " Dadyn Amfal " dagowa yayi fuskarshi d'auke da murmushi yace " na am uwar gidan Ibrahim " zaro ido Aunty Sumayya tayi cikin girgiza da kalmar shi
Daga Al'kamin....🖊
NPEEDY A AJI 🌸🦚🌸
Comments and share please

No comments