Breaking News

HAYATUL MAHAYAT 49-50

 


🌸 *HAYATUL MAHAYAT* 🌸

         🦚🦚🦚🦚

               🦚🦚

                 🦚

_Story and written_

            ```By```

*NPEEDY A AJI* 


_Dedicated to_

*My yar amana*



```My Novels 

1-NAYI RAYUWA DAKE

2-SANADIN ACCIDENT

    2019

3-SAKAYYAR CUTA 

4-RUFAFFIYAR ZUCIYA

5-FURUCI MURDADDIYAR SOYAYYA

 HAYATUL MAHAYAT

         typing......✍🏻```


 *_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*




🅿 49 & 50


Murmushi Momy tayi tafuskance shi sosai tace " haba  Ibrahim tayaya kake tunanin bazan amince da ka 'kara aure ba karka manta harga Allah kaida Sumayya duk d'aya na d'aukeku dan haka kadena tunanin zan hanaka 'kara aure dan kana auran 'yata kai mijin mace 4 ne idan zaka'iya adalci dan haka ina matu'kar farinciki Ibrahim nide fatana Allah yabaka ikon sauke hak'kin ko wacce wacece sirikar tawa ? " 


Seda Ibrahim yaji fad'uwar gaba amma yayi saurin dakewa yace " Momy Islam ce " Islam Momy tasake maimatawa sekuma tayi Murmushi tace " masha Allah kagakuwa duk gidane kuma nasan rashin jituwa bazai shiga tsakaninsuba sabida sun sha'ku sosai kuma yaranka zasu samu natsuwa sabida Islam tana matu'kar jidasu Allah yatabbatar mana da alkairi zan sanar da maimartaba semuji yaushe za'aje jin magana tunda abin duk gidane base antsaya wani bincike ba Allah yayi muku albarka " 


Ameen yaya Ibrahim yace yami'ke cikin jin kunyar Momy yafita binshi da kallo Momy tayi tanajin farincikin irin biyayyar da Yaya Ibrahim yakeyi mata 


Bakinshi d'auke da sallama Muzaffar yashiga cikin bedroom d'in  ganinta a kwance gayara sefaman hawa jikinta sukeyi yayi saurin 'karasawa d'aukarsu yayi amma suka saka kuka ahankali Rayhana tabud'e idanunta dan ganin waye ganin Muzaffar yasata tamke fuska sosai cikin 'bacin rai tace 


" ka'ajemin yarana kafita bamason ganinka kafita tace tafashe da kuka cikin kid'ima daganin kukan nata ya sauke yaran komawa sukayi gurinta suka lafe ajikinta suna kallon shi mamaki sosai Muzaffar yakeyi maiyasa yaran suke gudinshi yau kodan yayi 2 Weeks bayanan ne zafi yaji zuciyar shi nayi sabida kukan datakeyi 'karasowa yayi yazaune hannun shi yad'aura saman kanta cikin sauri yadubeta sabida yadda yaji jikin nata yayi zafi sosai agigice yace 


" ya Allah pretty zazza'bi ko ? sannu barinakira Aunty Sumayya tadubaki " sake fashewa dakuka Rayhana tayi hakan yasashi saurin tashi yafita had'uwa yayi da Momy zata shiga cikin bedroom d'in kallon tuhuma tayimai saurin cewa yayi " Aunty Sumayya zankira tadubata sabida naji jikin nata zazza'bi ne sosai " 


Bai jira mai Momy zataceba yayi gaba shiga ciki momy tayi zama tayi bakin bed ta'ba jikinta tayi cikin tausayawa tace " sannu Raihan kiyi ha'kuri kinji banji dad'in abinda Muzaffar yayi mikiba amma inda nagode ma Allah  shid'in mijinkine amma badan hakaba danayi mugun ba'kin ciki amma ko yanzu senayimai hukunci fiyeda tunanin shi sabida baiyi abu cikin tsariba k...... " 


Murmushin 'karfin hali Raihan tayi tace " a'a Momy  banaso asanadina kiyi fushi dashi kiyi ha'kuri  " girgiza kai Momy tayi tace " hmmm Raihan dole yasan yayi badedeba kinji karki damu bari nahad'o miki tea kishi zaisa kiji 'karfin jikin ki " girgiza kai Rayhana tayi alamar a a sake dafata Momy tayi had'ida yin Murmushi tami'ke zuwa akawo mata tea d'in Muzaffar yana shiga parlour Aunty Sumayya yasameta zaune itada Islam suna hira batare dajin komiba yace 


" Aunty please kizo kidubamin Raihan zazza'bi ne jikinta sosai kwance take " wani irin kallo tayimai tace " kamarya maiye silar zazza'bin nata? " 'bacin rai Muzaffar yaji dawannan tambayar tata yace " idan kikaje kika dubata zakiga dalilin zazza'bin nata " rai 'bace Aunty Sumayya tami'ke tace 


"wato ni zakazauna kanagayama irin haka ko lalle Muzaffar me yace dahar yazama nazafi ay gaskiya yafad'a idan kika dubata sannan zakisan maiye silar ko ? cewar yaya Ibrahim dayafito daga cikin bedroom  afusace Aunty Sumayya tace " kaga Abban Amfal kabarni dashi shi yasan maiya aykata wato kana gud'in akira wata tasan abinda ka aykata ko ? to kasani bazan duba Raihan ba  sede kasa Mu'azzam ko kanemo wato ayni wallahi Muzaffar idan har bazaka abince da auran Islam ba to mundinga ta'kun sa'ka dakai kenan sannan kabani mamaki dahar ka'iya ma'kalema yarinya 'karama harka afka mata batareda aure ba hmmm wato kaima hashiga sahun masu 'bata sunan masarautar HAYAT to kasani wannan maganar sena kaita har gaban maimartaba Muzaffar   "


" ya isa haka Aunty Sumayya  kisani har abada babu aure tsakanina da Islam dan idan nakirata Aunty babu matsala dan tana gaf dazama haka sannan kisani Raihan mata take agurina tahalak baizama dole kiyarda dahakan ba nanemi kidubata ne sabida ke macace bazan iya yarda Mu'azzam yadubamin mata ba kodayake d'a'uwa agareni sabida inada matu'kar 'kishi akan Raihan amma ayanzu kema bazan iya yarda kidubataba sabida ke ma'kiyiyar tace zaki'iya cutar min da'ita Aunty Sumayya idan kintashi sanarda maimartaba kisanar dashi agaban duk wani wanda ke cikin masarautar HAYAT  idan kikayi haka zakisani yin matu'kar alfahari sabida kinsa kowa yasan munzama d'aya nida Raihan  wallahi har kauta zanyi miki sabida kinyimin abinda nike matu'kar so nabarki lafiya dan Allah ki gaggauta yin hakan kinji my lovely Aunty " 


Juyawa yayi yabar parlour komawa aunty  Sumayya tayi tazauna tana mamakin maganganun Muzaffar tarasa gane inda wasu maganganun nashi suka dosa cikin neman 'karin bayani tadubi yaya Ibrahim kafin tayi magana yasakar mata Murmushi yace " duk abinda yafad'a gaskiya ne ammafa bazakiji koki daga gareniba dan haka kisakeyin nazari " shima fita yayi yabarta anan cikin mugun 'bacin rai da d'aurewar kai tadubi Islam tace " mai Muzaffar yakenufi da idan yakiraki Aunty baiyi lefiba ? " 


Murmushi Islam tayi tace sabida yasamu labarin zan auri d'an uwana I'b kuma kinga sunan su d'aya da abban Amfal shiyasa yace haka nakasa sanar dakene sabida yadda naga kinayin 'ko'kari wajan ganin na auri Muzaffar amma abin yagagara kiyi ha'kuri Aunty Sumayya Allah yakawo sauyi cikin rayuwata ki d'auka damacan Muzaffar ba mijina bane inada tabbacin Raihan bazatabar Muzaffar ya'iya kallon wata mace amatsayin mace ba na'kara tabbatar dahakanne ayau duk da irin soyayyyar da Muzaffar yayima Nabila bai ta'ba mayer miki damagana akantaba amma segashi yamayar miki da maganganun masu saka zuciya cikin zafin tunani akan Raihan kemafa kenan dakike Aunty inaga ni bare Aunty Sumayya naha'kura da auran Muzaffar kuma zan koma gida yau dan amsar auran yaya I'b karkiga lefina akan amincewata da auran yaya I'b koda ana gaba kid'auka haka Allah yatsara kuma nasan zakiyi farinciki " 


Daga haka Islam takoma cikin bedroom  dan had'a kayanta zama Aunty Sumayya tayi tamarasa irin tunanin dazatayi shiko Muzaffar yanafita yad'aga waya yakira wata doctor 'kanwar abokin shi babu jimawa ta'iso sosai Muzaffar yaji d'ad'in zuwanta akan lokaci jagora yayi mata har cikin parlour Momy ganin babu kowa se hadimai yasa yabata umarnin shiga cikin bedroom d'in


Cikin sallama suka shiga zaune Momy take bakin bed tanabama Raihan tea d'in dakanta sabida yadda jikinta yakeyin rawa cikin tausayawa Muzaffar yake kallon Raihan gawata irin tsantsar 'kaunarta dake sake shigar shi cikin mamaki Momy tadubi doctor  karima tace 


" lalle Karima yau kece  agidan namu nalura tunda kikayi aure bakison ziyara wai nikam ina d'ana misbahu kwana dayawa shima yadena zuwa gaidani " Murmushi doctor karima tayi tace " ayi ha'kuri Momy  nikam aykine yayi min yawa shiyasa shikuma yaya misbahu bayanan yatafi wani ayki Nigeria amma yakusa dawowa yaya Muzaffar baisanar dakuba ashe ? " Murmushi Momy tasake saki tace " ay kinsan halin yayan naki badai yasanar dakowa abinda yashafeshiba " Jinjina kai doctor karima tayi tayi tace " gaskiya kam gashi har yasake yin wani auran amma bamusaniba nasanma yaya misbahu shima baisaniba " 


" hmmm kawai Momy tace sannan tami'ke tace " zo kidubata karima barinaje nayi sallar issha'i idan kingama kijirani d'aukar yara tayi suna kuka amma tafita dasu dan kar suhana adubata da kyau bayan fitar Momy doctor karima tashiga dubata sosai cikin mamaki tadubi Muzaffar tace " amma yaya kad'an takura dayawa amma babu wata matsala zanyi mata allura yanzu zatasamu bacci sosai idan tatashi jikin nata zaiyi 'karfi zakuma taji dad'in jikin sosai amma yaya dan Allah a d'an lalla'bata zan rubuta wasu maganganu asiyo mata tasha bayan tatashi taci abinci " 


Jinjina kai Muzaffar yayi cikin tsoro Raihan  tace " nikam banason allura dadyn haidar please kar ayimin allura ganin yadda tafurgice yasashi yin mamaki sosai 'karasowa yayi har bakin bed d'in rungumota yayi sosai da'kyar akasamu tayarda akayi allurar sallamar doctor karima yayi tafita bedroom Momy tanufa shiko Muzaffar  kasa sakin Raihan yayi sake rungumeta yayi sosai itako rashi  'karfin jikinta yasata ha'kura da rungumar dayayi mata cikin sanyin murya yace 


" pretty bazan dena baki ha'kuriba dan Allah kiyimin afuwa karki d'aukeni tamkar marar tausayi bayin kaina bane natsinci kaina cikin wani yanayi namatu'kar gigita ne shiyasa nakasa saurara miki  please pretty kiyarda dani ina matu'kar sonki j......" jin shasshekar kukanta yasashiyin shiru cikin damuwa yashiga lallashin ta cikin kuka tace " banason jin komi daga bakinka kariga kacutar dani dan haka bazan yarda daduk wani furucin kaba idan kaciba dayimin magana bazan dena kuka ba " 


Dole Muzaffar yayi shiru yana tunanin yadda zaiyi Raihan tayarda yana matu'kar sonta babu jimawa bacci mai nauyi yayi gaba da ita  gyara mata kwanciya yayi yazubamata Idanu yanajin tsananin 'kaunarta cikin zuciyar shi dede lokacin Momy tashigo tamke fuska Momy tayi tace 


" Muzaffar banason sake ganinka cikin part d'in nan daga yau sabida Raihan batason ganinka kariga kayimin ba dede ba dan haka dole ka amshi hukunci " 


Cikin damuwa Muzaffar yabud'e baki zaiyi magana Momy ta'katse shi dafad'in tashi kafita dole yami'ke yafita cikin sanyin jiki zuciyar shi babu dad'i cikin ranshi yace 


" babu komi amma nida matata ahanani ganinta kai tsaye part d'in shi yanufa aranar da 'kyar yayi bacci washe gari duk innahirin ahalin masarautar HAYAT suka hadu cikin babban parlour sarki dan yanke hukunci akan su Ummi dasauran maciya amana cikin damuwa Muzaffar yake hange ko zaiga Raihan amma bata gurin sabida har yanzu jikin babu dad'i sosai ga yanayin tafiyar ta shiyasa ta'ki fitowa 



Please kuyi ha'kuri nima ba'a son raina kukejina shiruba har yanzu sun'ki sakar mana wuta kunga kuwa waya babu caji ay babu maganar typing amma dukda haka iname baku ha'kuri nagode da kulawar ku gareni sosai ana tare 🤝🏻


Daga Al'kalamin....🖊


NPEEDY A AJI 🌸🦚🌸


Comments and shine please

No comments