Breaking News

HAYATUL MAHAYAT 21-22

 


🌸 *HAYATUL MAHAYAT* 🌸

         🦚🦚🦚🦚

               🦚🦚

                 🦚

_Story and written_

            ```By```

*NPEEDY A AJI* 


_Dedicated to_

*My yar amana*



```My Novels 

1-NAYI RAYUWA DAKE

2-SANADIN ACCIDENT

    2019

3-SAKAYYAR CUTA 

4-RUFAFFIYAR ZUCIYA

5-FURUCI MURDADDIYAR SOYAYYA

 HAYATUL MAHAYAT

         typing......✍🏻```


 *_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*




🅿 21 & 22



Bayan fitar Aliyu Sarki Yazeed yami'ke yafara safa da marwa cikin parlour afili yace " dole na lalla'baka Aliyu dan nasan kai ba'ayima dole ina bu'katar yaron dake cikin Zarah gaskiya "


Shiko Aliyu cikin zuciyar shi cewa yayi Allah yasa Sarki yadawomin da Zahra kodan sauke wannan azababbiyar bu'katar tawa akanta ammafa badan sontaba "


Jirgin su muzaffar yana sauka muzaffar yaji wani irin fad'uwar gaba itama Rayhana hakan take haka suka fito kowa zuciyar shi cike take da matsanancin fad'uwa Sudees yana sa'be saman kafadar shi shikuma Shureem yana rungume a 'kirjin Rayhana 


Bai kira kowaba dan zuwa d'aukar shi se alokacin yad'aga wayar shi harya latsa number mu'azzam yayi saurin katsewa sabida shifa har yanzu fushi yakeyi da mu'azzam badan komi sedan marin dayamai akan matarshi kuma ya yarda  dazai iya aykata haka 


Number muzalbil yakoma yakira adede lokacin muzalbil yana zaune cikin office yakwantar dakanshi saman kujerar tunanin halinda mahaifinsu yake ciki yaketayi gawani irin mugun ciwon kai dayakeji jin 'karar ringing d'in wayar shi yasashi d'agowa ahankali ganin number muzaffar yasashi  saurin  d'aukar wayar yana d'auka  muzaffar yace 


" kazo kad'aukemu muna Airport " 


Yana fad'in haka yakashe wayar shi cikin mamaki muzalbil yami'ke fita yayi cikin Sauri kiran wayar momy yayi yasanar da ita  cikin farin ciki tace 


" bari atura motoci daga nan seku isa tare badan mahaifin ku dake kwanceba da haddani zamu tare muzaffar Allah Sarki 'kila raban suganane da shi dan wannan ciwon na maimartaba yana bani tsoro matu'ka "


Jin tana shirin sakashi kuka yasa yayi saurin kashe wayar cikin mamaki muzaffar yake kallon motocin gidan su sabida ko wacce mota tanada tambarin sunan HAYAT ajiki mi'kewa yayi kafin yayi komi motar muzalbil ta'iso mai d'auke da tambarin HAYAT m3 wato muzalbil wata motar  yagani tasakeyin parking yana ganin tambarin HAYAT m2 yaji wani irin 'bacin rai afili yace


" wato seda muzalbil ya gayyatomin mu'azzam ? hmmmm "


Cikin sauri mu'azzam yayo gurin shi yana sakarmai murmushi shiko muzaffar tamke fuska yayi shima muzalbil 'karasowa yayi yana bayyana farinci saman fuskarshi cikin fad'a muzaffar yace 


" maiye haka muzalbil ? nakiraka kai d'aya amma shine kayimin gayya to sede kukoma ku duka  aturo driver na yakawomin mota "


Murmushi muzalbil yayi yace 


" haba my brother Momy ce taturosufa  wannan yaranfa muzaffar ina kasamo wannan kyakkaywar yarinyar haka ? "


Tamke fuska muzaffar yayi yace 


" itad'in matatace kuma wa'innan yaran yaranane sannan ka'iya bakinka wajan yabamin mata kasan inada mugun kishi " 


Cikin mamaki mu'azzam yace " mata kuma muzaffar ? harda yara naga datafiyarka yau 5 months kenan amma wa'innan yaran sun kusa shekarafa muzaffar ? "


Afusace yace 

" amma nata'ba yima 'karya na auri Rayhana bayan aurena da Nabila da 1 Months lokacin danaje Pakistan yin wannan aykin iyayenta sune suka hanani tahowa da'ita sabida tayi 'karama dayawa shiyasa bansanar dakowaba dafatan kun'kire wannan jawabin dan kuyima sauran mutane shi sabida nikam banida lokacin 'batawa wajan gabatar musu da Rayhana "


Daga haka muzaffar yayima Rayhana nuni da ido alamar sutafi cikin motar muzalbil yashiga itama tashiga shima mu'azzam mi'kama wani dogara key d'in motar shi yayi yashiga cikin motar muzalbil d'in shiga muzalbi yayi yatada mota zuciyar cike da mamakin abinda muzaffar yazo dashi wasu motocin sukafarayin gaba se tasu se wasu 


Momy kuwa tuni tasa akafara shirin tarbar muzaffar cikin gaggawa itama Zahra zuciyar ta cikeda farinciki haka sauran  yayyan shi itama Aunty Sumayya farinciki takeyi musamman dan tahad'a shi da Islam wadda takeson ya aura tunkafin auran shi nafari Islam 'kanwar Aminiyar Aunty Sumayya ce  


Hadda ita aketa shirya komi bayansu babu wanda yasan da dawowar muzaffar  kafin wani lokaci ansa an'kara gyara part d'in muzaffar dukda cewa kullum cikin gyranshi akeyi yadda akaga motoci sunata shigowa kowa yasan wani ba'kone mai mihimmanci akaje d'akkowa 


Anyin parking security da dokarawa suka firfito har rigerige sukeyi wajan bud'e musu 'kofa ganin fitowar muzaffar yasa kowa mamaki tuni masu bushe bushe da alkaita sukafara masu kirarima sukafarayin nasu 


" barka da dawowa Yarima zakin fama sawun giya kake takena ragumi tafiya dake dole idan anason samun amincin masarautar HAYAT sadauki kake baka tsoro jarima kake baka gudu cikin dubban abokan gaba zaki tarwatsa miyagun namun daji k......... "


Dakatar dasu muzaffar yayi tahanyar d'aga musu hannu part d'in momy yanufa kai tsaye   yana shiga momy  tami'ke rungumarshi tayi tana sauke ajiyar zuciya yuyawa yayi ya amshi Sudees sannan yakamo hannun Rayhana suka 'karasa cikin parlour itako Rayhana se yanzu tasan tayi kuskuran shigowa cikin gidan nan wannan irin abu haka ay dole asamu d'inbin ma'kiya da munafukai musmman akan muzaffar dukda batasan yadda aka d'auki sauran 'yan uwan nashiba amma ta tabbatar shid'in d'ane mafi soyuwa acikin wannan masarautar gashi taga alamar anajin mugun tsoranshi 


Zama tayi kan cushion itako Rayhana zama tayi a'kasa cikin girmamawa tafara gaida momy fuska dake momy take amsa gaisuwarta juyawa tayi kansu Aunty Sumayya da yaya Abubakar shikam yaya Ahmad bayanan wata irin harara Aunty Sumayya tasakar mata shiko yaya Abubakar fuska sake ya amsa 


Tasowa Zarah tayi cikin girmamawa tagaida muzaffar da Rayhana amsar Shureem tayi ayko tana d'aukar shi yasaka kuka dole ta ajeshi cikin mamaki muzaffar yake kallon Zarah ganin tsohon cikin jikinta cikin zuciyar shi yace 


" sabida rashin hankali dawannan cikin tazo gida amma bari zuwa anjima senaji dalilin wannan zuwan nide bansanar makowa zuwanaba ballle asanar mata "


Mi'kewa Muzaffar yayi yace 


" mom bari naje gurin maimartaba dan namatsu inganshi Zuciya ta takasa natsuwa inajin kamar awai matsala  "


Cikin sauri momy tace 


" a'a muzaffar kabari zuwa anjima sabida yanzu yana ganawa dawasu 'bakine "


Badan ranshi yasoba yakoma yazauna itako momy tayi hakanne dan yaci abinci cikin natsuwa kuma su kawu Yusuf sunce kar abari kowa yashiga inda yake se malam yazo wato boka malamin 'karya cikin yatsina Aunty Sumayya tace 


" kai muzaffar wannan yarinyarfa daga ina gashi hadda yara ? "


Banza muzaffar yayi mata sema ciro wayar shi dayayi yana latsawa mu'azzam ne yabata amsada 


" matarshi ce da yaranshi "

Azabure Aunty Sumayya tami'ke tana 'karema Rayhana kallo tafi tayi had'ida shewa tace 


" tabd'ijan badai a cikin gidannan ba wannan kalar rainin hankalin  yaushe harya aureta hadda wa'innan yaran  lalle muzaffar kanayin abinda kaga dama cikin gidannan "


Rai'bace muzaffar yace 

" ya'isa haka Aunty Sumayya Rayhana matatace kamar yadda kikaji mu'azzam yafad'a kuma wa'innan yaranane Sudees da Shureem wallahi idan wani abu yasamu Rayhana da yarana cikin masarautar nan narantse da Allah sena bankama kowane part dake cikin masarautar nan wuta illa na mahaifina da mahaifiya ta akwai idan kuna ganin narikice akan son Nabila da Twins d'in ta to akan Rayhana da Twins d'innan hauka nikeyi dan haka duk wanda  zaiyi wani munafurci ina sauraran shi dan Allah karyafasa kuma nasha alwashin duk ranar dana gane makashin Nabila da sace yaranta sena kaishi kiyama "


Cikin d'aga murya momy tace " ya'isa haka muzaffar Sumayya karnasakejin wannan maganar kowa 'yan'uwanki suka kawo yakamata kiga kimarshi sabida ba 'kiyayyace tahad'asuba nagaya miki kibi hakankali karkijama kanki raini agun 'kaninki da matar shi "


Cikin fushi Aunty Sumayya tafita tana fad'in bari nasanarma kaka nasan batasan abinda yakefaruba  idan ita tayi magana ay dole muji yadda akayi hakatafaru batatedasanin kowaba tunda kai karenamana arziki "


Fita tayi afusace bayan fitar Aunty Sumayya momy tace 


" muzaffar wannan lamarin akwai d'aure kai yimin bayanin yadda har kayi wannan auran batare dasanin kowaba kuma hadda yara masu kusan shekara dama babu yara senace bayan tafiyarka kayishi sanar dani muzaffar ni mahaifiyar kace kuma ina matu'kar son abinda kake so "


Kallon muzalbil yayi bama momy bayani muzalbil yayi kamar yadda yabasu jinjina kai Momy tayi cikin gamsuwa murmushi tayi cikin farin ciki tace 


" matsonan 'yata Raihan ko dagajin sunanki akwai al'kairi atare dake kisaki jikinki kamkar kina gaban mahaifiyar ki kinji "


Sanyi Rayhana taji cikin ranta se yanzu taji sassaucin bugunda zuciyar ta keyi ko babu komi tasamu kakkyawar kalma daga gareta 


Shikin sababi Kaka tashigo cikin parlour Momy tsayawa tayi tana 'karema Rayhana kallo da muzaffar ta'be baki tayi tace 


" sannu ishesshe wato dama mata 2 gareka kaboye d'aya ko ? to bari kaji idan nabarka akan wancan kuskuran dakayi  na auran Nabila to akan wannan baka isaba dan haka kayi gaggawar mayarda wannan yarinyar tunkafin dare yayi dan bazata zauna cikin masarautar nan ba yara kuma ta'ajemin su dan ina matu'karson jika musamman  Twins


Cikin tashin hankali  Arfat  tami'ke sabida razana dajin labarin dawowar muzaffar amma da mata harmada yara  cikin wata irin murya tace 


" ina bazai yiwu muzaffar d'ina dawata mace ina bazan iya jurar hakanba wallahi dole tabar cikin masarautar nan "


Misalin 08:06 

Boka yashigo cikin masarautar HAYAT har wannan lokacin Muzaffar baisan maimartaba bashida lafiya ba suma su kawu Yusuf basusan muzaffar yadawoba 


Dede lokacin Muzaffar yami'ke yace gaskiya koma wa'inne irin ba'kine senaje gurin mahaifina naganshi dan Zuciya ta takasa natsuwa Rayhana zomuje in gabatar dake gurin mahaifina d'aukar yaro d'aya yayi itama tad'auki d'aya suka fita sauranma bin bayan su sukayi itakam momy dama tana can da Ummi suna jiran shigowar Malam



Daga  Al'kalamin.....🖊

No comments