Breaking News

FURUCI 61-62

 🗡 *FURUCI*🗡

         💔💔

       

*(Murd'add'iyar Soyayya)* 💓❣💘


Story and written 

            By 

NPEEDY A AJI 🌸mamyn Zarah🌸


               🅿️61 to 62




                   Dedicated 

                          To

                    My lovely  

                     *Ummi*

                         and  

                       Lovely          

                     Daughter 

                     *ZARAH*


           My Novels

*NAYI RAYUWA DAKE* 

*SANADIN ACCIDENT*

*SAKAYAR CUTA* 

*RUFAFFIYAR ZUCIYA*

*HAYATUL MAHAYAT*

*MUGUN SARTSE*

         Loading....🖊

🗡💔FURUCI!!!!💔🗡


 *_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*





 🅿 61 to 62


Abu kamar wasa d'aga waya Kabir yayi yakira ma'ay kata cikin hadda wani doctor dan tabbatar da gubar da babyn taci cikin tsananin  'bacin rai Akeey Zaffar yace " Wai kai Kabir kananufin dagaske kakeyi ne wajan tuhumar Momyn yarinyar nan ? kabarni naji da d'aya mana ganin gawar baby a kwance kad'ai ya'isheni tashin hankali wallahi nayi imanin Bahijjat bazatakashe min baby tun bayan wasu shekaru take riqe da ita dazata kashe ta datuni takasheta " dafashi Kabir yayi yace " ka kwantar da hankalin ka Zaffar nimafa banace Wai tabbas itace takashe baby ba a a zargine Kuma nasan zakaso sanin wanda yayi maka wannan d'anyen aykin dubada irin tsananin son dakakeyima baby Wanda babu alamar zakasamu wata Koda kasamu dole bazaka manta da baby ba kodan Mahaifiyar ta kasanfa ni hukuma ne Mai hakqin kwatar makowane d'an Adam haqqin shi idan bincike yanuna matarka batada lefi to babu abinda zamuyi mata amma yanzu dolene mutuhumaita gunda ayanzu bamuda wani abin zargi se ita kayi haquri zamutafi da gawar baby danyin wasu gwaje gwaje dukda kasancewar ka doctor bakaine yakamata kayi wannan binkiken ba sabida ba lalle ne kasanar damu gaskiya dubada yadda kake qoqarin hanamu aykin mu bazamu tafi da matarka ayanzuba amma idan akwai yiyiwar hakan tofa zamudawo sekaji daga gareni " 


Sawa Kabir yayi aka d'auki gawar baby kafin yafita Akeey Zaffar yadakatar dashi sannan yace " inaso kasani tabbas Bahijjat bazata iya kashe kowaba balle baby sannan dakake maganar babu tabbas d'in samun wata babyn to kasani ayanzu Bahijjat tana d'auke da cikin 2 months kuma wallahi idan kukayi sanad'in wannan cikin yasamu matsala asanadin wannan mugun zargin naku to wallahi senayi shari'a dakai sannan nikoma waye yakashe Baby nabarshi da Allah tunda nayi imanin ba Bahijjat bace dan haka kubani gawar 'yata ayimata sutura Allah yawadaran aboki irinka   " 


Sosai Kabir yadubaishi yace " haba Zaffar wallahi da alkairi nake tare dakai wannan abin dakaga nayi yazama dolene ni hukumane kasan wannan yazama dole nakama duk wani mai lefi koda kuwa shid'in ubanane to wallahi senakamashi sabida nayi rantsuwa akan haka sannan bama matar kaba Koda kaine zargi yagifta takanka tofa wallahi sena bincike ka dukda kuwa kaine kahaifi baby sannan idan Kai kayafe tofa ita government bata yafeba dole tabinciko mai lefi aduk inda yake kuma tahukuntashi har gobai Kai abokina ne Bahijjat inatayaki murnar samun qanwar baby " 


Daga haka suka fita shida sauran jami'an da gawar babyn dasauran abincin dabata qarasa cinyewaba se alokacin Aunty Bahijjat tasaki wani irirn kuka had'ida fad'in Innanillahi wa'inna ilehirraju'uuuunn Allahumma ajirni fimusibati wakalumfi kayrun minha waqifli kairun minha " bata tayi zata fad'i Akeey Zaffar yayi saurin riqota shiko yamakasayin kukan sede wani irin zafi da zuciyar shi keyi yamarasa Yaya zaiyi 


Cikin tashin hankali yad'aga waya yakira Mahaifiyar shi yasanar da ita kafin yaji yanayin tashin hankalin dazata shiga yayi saurin kashe wayar cikin raunin murya yace " my dear banaso kitashi hankalin ki kinsan de halin dakike ciki kuma nayi imanin bazaki iya  kashe Baby ba kisaka hakan cikin ranki nasan su momy sunanan tafe ni zan bi su Kabir " daga haka yami'ke cikin sanyin jiki Yana kaiwa bakin qofa yajuyo yasake duban Aunty Bahijjat yace " dan Allah kibar wannan kukan har abada kece Momyn baby tatafi da tsananin sonki cikin zuciyar ta tabbas wannan abun alfahari ne agareki  ada Baby babu Wanda takeso sama dani amma ayanzu tafi sonki fiye dani gashi kin rasata alokacin datake cikin tsananin gata agun Momyn ta Allah sarki baby ashe bazataga qanin nataba narasa Mahaifiyar ta yauma gashi narasata my dear Koda kece Kika kashe min baby bazan hukuntakiba sabida kinyi Mata dukkan alkairi amma ina da tabbaci cikin zuciyata cewa bake bace  naroqeki karkisa nasake rasa little baby dan Allah my dear dan Allah 😭😭😭 👏🏻👏🏻👏🏻 " 


Daga haka yafita cikin sauri yanazubba zafafan hawaye tsayin lokaci yana tsaye a parlour yakasa fita wani irin kuka yakeyi marar sauti amma dukda haka Aunty Bahijjat tanajiyo sautin shasshekar kukan nashi wani irin juwa Aunty Bahijjat taji had'ida wani irin mugun ciwon kai wayar shi tad'auka wadda yabari anan kiran wayar Ammin tayi bugu 2 tad'aga kasanin magana Aunty Bahijjat tayi sabida kuka sautin kukanta kawai Ammin keji cikin tashin hankali Ammin ke tambayarta amma takasayin magana sosai hankalin Ammin yatashi da qyar Aunty Bahijjat tace 


" Nashiga 3 Ammin wallahi mutuwa zanyi kizo tun kafin kirasani " daga haka tasaki wayar tafad'i jin haka yasa Ammin miqewa cikin tashin hankali tafita zuwa part d'in Sarki Zaid  tsayin lokaci Akeey yana parlour Yana kuka kamar ranshi zaifita sannan yamiqe yafita cikin sanyin jiki Kiran driver yayi yace yatada mota bayan driver yatada mota Akeey Zaffar yashiga yazauna amma yakasayin magana dubanshi driver yayi cikin tausayawa yace " se ha'kuri Yalla'bai Allah yajiqan baby ina zamu ?  " police Station " kawai Akeey Zaffar yace cikin dashasshiyar murya " 


Babu jimawa dafitar  Akeey Zaffar su Momy suka shigo cikin tashin hankali suna shiga Suma su Ammin da Umma suka shigo hadda shi kanshi maimartaba kafin wani lokaci duk sunji abinda yakefaruwa sosai hankalin kowa yayi matuqar tashi sannan kowa yayima Aunty Bahijjat kyakkyawan zato amma abin mamaki banda Momy wato Mahaifiyar Akeey Zaffar cikin tashin hankali tadubi Aunty Bahijjat tace 


" Damani zuciya ta takasa yarda da irin kulawar dakike bama baby shidama mugu bashida Kama wato kinyi hakanne tsawon shekaru sabida wannan mugun nufin naki sabida idan kika aykata kowa yace bazaki iyaba sabida anga kinabata kulawa matuqar to Allah yafiki wato kinga tunda kikazo ke babu alamar haihuwar sede kici kiyi kashi to in Sha Allah se  Allah yatoni asirin ki azzaluma Kuma kisan" dakatar da ita maimartaba yayi dafad'in " haba Hajiya wa'innan kalaman basudace dakeba dukda bakashedan d'an yau to amma akwai d'aure kai da tantama cikin wannan lamarin sannan kisani har yanzu zargine ba tabbaciba sabida haka mubari hukuma suyi aykinsu idan akagane cewa Bahijjat itace ta aykata wannan ayka ayka to tabbas ni Sarki Zaid Ina bayan gaskiya Kuma zanyi jagora wajan yanke mata hukunci idan Kuma yazama batada hannu acikin lamarin tofa bazan iya maida mata kimarkiba cikin idanunta " daga haka yadubi Ammin da Umma yace " zanje police station d'in naji Yaya ake ciki " kafin maimartaba yafita Momy tasake cewa " ay wannan lamarin yafi qarfin police Kotu kawai zamu ananne za'ayi cikakken bincike idana qwararan lawyer Wanda zai tabbatar dacewa Bahijjat itace takashe baby Wai ga abu afili akeyin wata kwana  "  


Cikin 'bacin rai Ammin zatayi magana maimartaba yadakatar da ita yace " Kar kice komi kude kukula dahalin da Bahijjat take ciki nakuma san 'yata akwai imani dakuma yarda da qaddara kowace irice yau ga ranar karatun Saraki tazo ashe gara danabar shi yakaranci abinda yakeso kisanar dashi komi yanzu Kuma cike komi yakeyi yabaro yataho agobe shida iyalin shi dama nagaji dazaman shi a USA " 

Daga haka maimartaba yafita jikin sanyin jiki 


Comments please

No comments