Breaking News

DUK NISAN JIFA 44

 


🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

          *DUK NISAN JIFA*

           _(K'asa zai dawo)_

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾


            _RUBUTAWA_


               *SAJIDA*


        *SADAUKARWA*


                   *GA*


           *MASOYA NA*



💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_

 




                                44




A hankali muryarta na rawa ta ce" Aba, ni sam ban taba sonsa ba, banma san meye hakan zai bada wata ma'ana ba, ni yayana ne, baban yayana ne, wanda ya rike ni tamjar yarsa, Aba kar ku min irin auren nan a karro na biyu, kar ku mika ni a sake ni ba tare da wata kwakwarar huja ba Abana"



Mahaifinta dake kallonta shima jiki a mace ya ce" Bilkisu am, to menene na zubar da hawayen? Yanzun hamanki ne bakya so? "


Bilkisu ta kara sada kanta tana tare kanta wa fashewa da kuka ta gyada kan nata ta ce" Bana so Abana, bana so kar a min, ya je ya karata da matarsa ba wani abinda zan iya so kuma a tare da shi"


Abanta ya kuma tsatsareta da ido ya ce" Kamar me fa? "


Dubansa ta yi ta ga irin yadda ya bada hankalinsa a kanta gaba daya, sai kuma ta sada kanta da sauri ta kasa cewa komai


Aba ya sauke ajiyar zuciya a sanyaye ya ce" Da farko kalaman bakina na bada ban rigaya na gabatar da istihara a kan maganarku ba, ki yi hakuro autana ko wancen na maki aurwn gagawa ne cike da tsoro da firgicin rasa yar uwarki ke kina kuka shi mijin da za'a aura mata yana yi, shine na aura da ku dan kowane ya rarashi dan uwansa, ashe ke ke yin kukan rasa yar uwarki shi kukansa ya fi karkata kan tsoron Allah da tunanin me zai cewa unangijinsa a kan abinda ya so boyewa a hadu da shi a cuci baiwar Allah, ba zan ce maki komai ba a kan auren nan, idan ya zama alkhairi za'a daura shi, idan ba alkhairi bane na tabata Allah ba zai bamu ikon kuma daura maki shi ba sai dai idan zanen kadararki ce a haka, raba aurenki na farko luwa shine huja, ba auren nan!"


Bilkisu kanta a kasa yake har yanzu, mahaifinta ya dauki shiru na dan lokaci kafin ya ce" Ki je gida ki huta, banda koke koke da tunani kin ji? Idan kuwa a nan zaki yi zamanki na bude maki gidan ki shigo kin ji autana? "


Bilkisu ta dan girgiza kanta tana jan hancinta har Aba ya gama mata adu'a ya juya ya fita a mktar sannan ta tayar da motar ta juya ta yi gama


Haka kawai daga kasan zuciyarta take jin tana hasala da lamarin nan, sosai take jin haushin abin harma take jin bata so har kasan ranta, du ta watsar da komai ta ture komai a me zata je? Ta biyu kuma ba shi ya nema ba! Shin yaya suke so su yi zaman fahimta bayan yana mata kallon yar jaririyar da bata kai wajen da namiji zai iya yi mata kalmar so ba? Sarai ta san dalilinsa na tatarewa da kasa fada, kai ita batama yarda ba domin sarai mama ta saka mata kokonta a zuciyarta


Maimakun ta je gida sai ta samu waje ta raba motarta tana ji ana kiraye kirayen sallar magariba

Gannin ita ba abin sallah ne da ita a motar ba sai kawai ta karkata ta nufi gidan su laila


A cen ta yi sallar magaribar, har isha'i ta shigo suka yi kafin ta kwonta lamo saman doguwar kujerar falonsu ta afka tunani


Mahaifiyar Laila ce ke magana ta hanyar fadin" Bilkisu Bilkisu? "


A zabure ta dago domin ta afka tunani ne

Maman Laila ta ce" Lafiarki kuwa?"


Bilkisu ta sauke ajiyar zuciya tana kallonta ta mike zaune 

Mamanta ta ce" Waya ke kuka tun dazu shin lafia kuwa? "


Dan Murmushi ta saki a hankali ta mike wajen da ta jona wayarta a caji ta je ta dauka tana dan jan karamin tsakin iya shegen Laila wai wani ta yi bako saurayinta ne da abokinsa sunna cem sunna zance


Wayar ta duba , mama ce, sai kuma Yayanta

Tana shirin maida kiran a number mama wani kiran ya shigo a number yayanta 

Tana dagawa ta yi shiru bata yi magana ba, shi kuwa muryarsa a sanyaye ya ce" Kina ina ne? "


Bilkisu ta lumshe idannuwanta ta dane bacin ranta  sannan ta bude ta bi fallon su Laila da kallo tamkar wace ke son gane a inda take kafin ta ce" Ina gidan su Farida " sannin da ta yi cewar gidan su Farida na yanzu bako ne a wajensa domin bai san inda suka koma ba sai ta yi wannan karyar dan idan ta ce da shi gidan su Laila ta tabata yana iya zuwa inda take ya umarceta ta koma gida kamar yadda ya saba


Tana jin yadda yake dan sauke numfashinsa ya kasa magana sai kuma ta ji muryar mama tana fadin sannu da yannayi na kamar a mota suke


Cen dai ta gama gajiya da sauraron numfashinsa ta nemi kashe wayar tana ji ana bude motar mai yiwuwa fita ne suke a cikin motar su kuwa sun dawo daga asibiti da Tati ne wace ta tsurawa waje daya ido ta kasa magana sai kallo


Yannaciki lon yadda mama ke rungumota a jikinta har suka shige kafin ya sauke ajiyar zuciya yana kallon wayar da ta kashe masa

A hankali ya danna dan maida kiran aman sai ya sameta online

Gurum ya yi da wayar a hannunsa yana ta tunani, gidan su Fareeda da wannan daren bayan ya fada ta dawo gida? Kuma ta katse masa kira yanzun take online da wa? 


Kader ya gyara zamansa ya ce" To fita mana "


HISHAM ya juyo yana kallonsa yadda yake jira ya fita a motar shi kuwa ya gyara mata tsayuwa ya ce" ka san gidan su Fareeda kawar Billy ne? "


Kader ya girgiza kansa da sauri ya ce" ni ai mun jima da batawa da ita, sam na kula ba kaunata take ba tunda har ta ce sai ta yi exam zata aureni!"


Hisham ya tabe baki, domin haka suke bini bini zai kwashi fada shi sun rabu da farreda ba zai kuma kulata ba, kuma ana dan jimawa sai ya maido zancenta ka ga yana koda soyayarsu da abubuwa daban daban, ko yanzun ya tabata karya yake masa aman sai ya share yana kallon wajen redion motar Kader ya ce" Yauwa, ina fatan ka yi tunanin ta yadda zaka sanar da uwar gida zaka yi mata amarya ko? "


HISHAM ya zuba masa ido, ta yadda zai sanar mata? Har ta wani yannayi zai sanar mata da abinda ta rigaya ta sani kamar wani mawaki zai kama maimaita abubuwa? Ai ta sani, itama ta fada cewar bata kishi da Billynsa, dan haka baya gannin dalilin da zai saka shi zama da ita ya wani maimaita zancen


Irin yadda ya tabe baki ya cire kansa a maganar ya saka Kader gane ba wannan ne a gabansa ba, dan haka sai ya gyara zamansa yana kallonsa ya ce" Ka ga, kar ka zamo cikin mazan da so zai saka su shiga wuta, Hisham kai dai ba jahili bane a mayar da maganar auren hadi tsakaninka da Aisha tunda har ka iya amsar bakuntarta ka mayar da ita sirrinka ina gannin idan abu na cutarwa ya shiga ba dadi, me zai hanna ka kwatanta adalci? Ka yi kokari ka bata nata matsayi na matarka, to ka ga fa ko wata bata cire ba za'a yi mata kishiya, na tabata koda bata darza maka rashin mutunci irin nasu na mata ba sai ta sha kuka ko ta ce a saketa bayan ba wanda ya isa ya sa a saketa ko idasa more sadakinmu bamu yi ba! Ah tam million biyu? Idan ka saketa ni ko a hanya na ganka ba zan kuma kulaka ba!"


Hisham a dake yana jin gaba daya hayaniyar da tsarabe tsaraben matsalolin yau da kulun sun fara saka shi juwa  ya ce" Ka rage murya mana kana min ihu a ka!"


Kader maimakun ya rage muryar sai ya yi gum da bakinsa yana kallonsa


HISHAM ya ajiye wayarsa nan ya kwonce belt din jikinsa ya fita ba tare da ya kuma ce masa komai ba


Kader ya gyara zamansa yana dan turo baki domin ya tabata fita zasu yi, shi kuwa a yau ba zai kaishi gidan su Fareeda ba dan ya san yana zuwa zasu shirya bayan ya kamata da wani saurayin daban sun yi fada basa magana salon gobe ta ce ai shi ya dawo ko? 


Yana shiga fallon ya tarda tarron yadda ya saba, kowa na nan banda Billy


Mama dake waya ya kalla bayan ya amsar gaisuwar su Aisha yana sauraron abinda take fada

Mama ta ce" Bilkisu gani na yo ba sallah ba, ba wani biki ake ba, idan ba wadinnan ba ai bakya zuwa ki kwana gidansu, itama idan ana wani sabga take kwana a nan shikenan kamar tautau sai ki kama yawo harda su son kwana" 


Hannunsa ya dora gaban goshinsa yanna kallon yadda fuskar mama ke nuna alamun amincewarta da maganar har sai da ta furta" To ki tabatar kin kula, ki kama mutuncin kanki safia na yi kuma ki dawo min gida kin ji ko? Bani maman tasu mu gaisa na fada mata safia na yi ki dawo kin ga bana son rigima ni!"


"AN gama", ya fada a kasan zuciyarsa kafin ya karasa ya nemi waje ya zauna yana fuskantar Tati dake zaune da mahaifiyar Aisha a kusa da ita tana wani yi mata magana kasa kasa, ga Aishar gefe tana zaune cikin shiga ta lesh tana danna wayarta domin au kansu basu jima da dawowa daga asibiti ba, yau kakanta har murmushi ya mata shi yasa gaba daya take cikin farin ciki.


Jiki a sab'ule ya mik'e ya bar falon ba tare daya tanka kowa ba sabida alhinin kwanciyar Billy a wani gidan da ba na su ba kuma bana Abba ba, gidan kawarta!




Da sassafe Abba ya doko musu sammako yazo, Tati da maman Aisha na gefe zaune tana ta tausarta da kalamai, sai Aisho da shigowar kenan falon tana mik'awa Tati tea mai zafi da Mama ta bado daga kicin, sallamarshi ce tasa Mama fitowa tana gyara zaman hijab d'inta tana kallonshi da mamaki, gaisawa sukayi sosai har yana tambayar jikin Tati, cikin son sanin abinda ya kawoshi Mama ta nuna mishi wuri tace "Bismillah ka zauna." 


Da fara'a ya zauna yana d'an waigawa dan son ganin Bilkissu, kallon Mama yayi zaiyi magana sai kuma Hisham ya shogo da siriryar sallama a bakinshi cikin shirin fita, kamar kullum dai k'ananan kaya ne da suka dace da likitoci, da girmamawa ya isa kusa da Abba suka gaisa. Dan satar kallon Tati yayi data zuba mishi ido take ganinshi kamar ubanshi yace "Ya jikin?"


Mamar Aisha ce tace "Da sauk'i, saidai bata ma kowa magana har yanzu, ina tsoron damuwa ta mata yawa."


D'auke idonshi yayi kamar abun bai dameshi ba, saidai ciwon daga zuciya yake, haihuwa tafi k'arfin wasa kam, Aisha dake tsaye har yanzu ta kalleshi ita ma tace "Ina kwana."


Kallonta yayi fuskarshi bâ yabo ba fallasa yace "Lafiya lau."


Ganin kamar suna gaishe gaishensu yasa Abba kallon Mama yace "Ina Bilkissu ne?"


D'an sosai goshinta tayi tace "Tana gidan k'awarta, amma yanzu zata dawo."


Da mamaki yace "K'awarta kuma? Me ta tafi yi da sassafe haka?"


Galala mama ta kalleshi tace "Ai a can ma ta kwana."


Zarro ido yayi yace "A can ta kwana? Akan me? Dare tayi ne jiya?"


Shiru maama tayi kanta k'asa saboda yanda ya tsareta da ido yana tambayar kamar zai daketa, jinjina kai yayi ya muskuta ya gyara zamanshi yace "Yayi kyau, dama ba wani abu bane ya kawoni maganar aurensu ne."


K'uri duk mutanen d'akin suka mishi da ido suna kallo harda Tati, ba tare daya kula da yanayin kowa ba yace "Bayan mun tattauna da Bilkissu jiya nayi istihara a game da lamarin nan, ba abinda na gani sai alkairi, dan haka ku shirya *ranar juma'a* za'a d'aura musu aure."


Mik'ewa yayi alamar tafiya zaiyi, ga dukkan alama ya fahimci akwai Wanda zasu kawo masa wargi shiyasa, da sauri Mama data bishi da kallo tace "Abban Bilkissu."


Juyowa yayi yana kallonta sai kuma ta kasa magana, cikin taushin murya yace "Kina da magana ne?"


Rufe bakinta tayi sosai tana dan had'a yawu, murmushi ya sakar mata yace "Da namu auren za'a d'aura ai."


Sake wangale baki tayi kunya kawai ta ryfeta, tana kallo ya fice a gidan ya barta da kunya da al'ajab, yanda ta kasa motsawa haka Hisham ya daskare a wuri d'aya, juma'a kawai yake maimaitawa a ranshi, abu d'aya kawai ya sani indai juma'a za'a d'aura aurenshi da Billy to tabbas wannan juma'ar ta misamman ce a ganiyar na musamman d'in, yana tsaka da tunane tunane yaji muryar Maman Aisha tace "Tabb'! Lallai ma."


Kallonta duk sukayi ita kyma ta mik'e tsaye tana kallon Hisham kamar yanda yake kallonta tace " Maganar aurenka ake bayan aurenka na fari yarinyata ko tarewa batayi ba a gidanta? Wannan wace irin rayuwa haka? Ko gusar da ita bamuyi ba daga gabanmu za'a mata wata kishiya, to gaskiya da sake, wannan ba ma abu bane da zai yiwu ehe!"


Saida ta dasa aya Hisham ya saki wani lallausan murmushi ya mik'e daga rank'wafawar da yayi juya ya kalli Mama, takawa yayi har saida ya tsaya gabaanta ya rik'o hannayenta yana mata murmushi yace "Mama na, karki damu kanki dan Allah, karki bari damuwa ko tunanin wani zai d'aga miki hankali yayi tasiri a walwalarki, kinsan dai farin cikinki shi ne nawa ko?"


Yanda yake magana kawai yasa ta d'aga mishi kai alamun eh, jinjina kai yayi tare da sakin hannayenta ya juya zai fita, takon sassarfar Aisha yasa shi tsayawa ya juya ta b'angaren da take, ita ce ta bar wurin da sauri da alama kuma kuka ne take son b'oyewa.


Tab'e baki yayi ya juya zai tafi, cak kuma ya k'ara tsayawa saboda tuna maganganun Kader na daren jiya, a hankali a sanyaye yaji tausayin yarinyar na samun mafaka a zuciyarshi yana zama, d'an k'aramin tsaki yayi na rashin jin dad'i tare da juyawa da sauri ya nufi inda Aisha ta shiga...... mahaifiyarta kuwa buuuu ta mike ta yi ciki da waya a hannunta tana lalubar number mijinta, tati kam kanta na kallon kasa gaba daya ji take idan ta budi baki wani irin kuka ne zata yi wanda zai saka ta kuma wata sumar har jinnin nata ya kara hawa sosai


Yana shiga ya ja ya tsaya jikin garun yana kallonta

Kwonce ta yi tana rusa kuka duda irin yadda take kokarin hanna kanta yin mai karfin nan


Tausayinta sosai ya kara ji a kasan zuciyarsa hakan ya saka shi a hankali ya karasa bakin gadon ya dan zauna kafin ya dan yi guaran murya


Kittt ta yi da kukan sannan ta dago da sauri tana kallonsa


Ido ya tsura mata, Aisha bata da muni ko kadan sai dai da ake cewa shan koko bukatar rai kuma sam baya jinta yadda yake jin soyayar wace ya raina shekara da shekaru, aman kuma zai yi iya yinsa dan kamanta adalci a tsakaninsu, sam ba zai bari ta kara gaskata cewar dan ba itace zabinsa ba kuma ba zata ji dadin zama da shi ba


A sanyaye ya ce" Kuka kuma Aisha? "


Aisha ta zauna sosai tana dan girgiza kanta tana share hawayenta


A hankali ya kamo tafin hannunta yana kallonta ya ce" Da kika ce min zaki fi kowa taya ni son abinda nake so, ba zaki yi kishi da ita ba domin kanwarki ce shin kin fada ne dan kin ji a lokacin ta min nisa ko har cikin ranki da gaske kike? "


Aisha ta sada kanta tana sauke ajigar zuciya ta rasa me zata ce masa


A hankali ya ce" Ko dai dan bamu jima da auren bane kema yake maki ciwo? "


Aisha ta dago tana kallonsa ta ce" Tun kafin a sako maganana na san da so a zukatanku na junnanku har na so na takafa ku furtawa junna, na san cewa koda ta auri wani da kyar na iya samun kasonta, aman zuciya bata da kashi docter, na kasa hakuri har na kama kuka bayan ba rashin adalci akai min ba hasalima halaci akai min tunda ni din kutse ne na yi"


Hisham ya sakar mata dan murmushi yana kallonta ya ce" Ba'ai maki adalci ba, ki yi hakuri Aisha, domin ya dace na kilace ki na sanar da ke, haka na tsara to Aba bai san  baki san da zancen ba, baki yi kutse ba dan kuwa kina da kima da daraja a idannuwana, Aisha kin zama sirrina ki kasance bargona ke din suturata ce, ba maganar kutse a matar aurena koda ban je shinfidarta ba bale jar hakan ya faru, Aisha i'm so sorry da irin abubuwan dake faruwa domin kin fi karfin haka, ki taso mu tafi gidanmu, ki saka a ranki Billyna kanwa ce zata zo ku zauna ku hade kawunnanku ba abokiyar gaba ba, ina rokarki da ki kwontar min da hankali domin da gaske *Damuwarki* na iya damuna"


Kalamai ne da basu taka kara sun karya ba, kalaman da bai dauki lokaci mai tsayi yana furta su ba, haka kuma bai tsara karya dan ya faranta mata ba sai tsantsar gaskiya da kula da dan lokacin da ya bata dan ya nuna mata cewa itama mutun ce kuma dan an masu auren hadi ba yana nufin ita din makiyiyarsa bane, haka kuma auren da zai kara ba dan ya tsaneta bane sannan zai kwatanta adalci a tsakaninsu sai ta ji wani sanyi ya ziyarci zuciyarta, a hankali ta dora kanta a tafin hannunsa muryarta a sanyaye ta ce" ni dai fatana kar ka guje ni, kar ka tsane ni, kar ka wulakanta ni"


Murmushi ya yi yana dan murza damtsen hannunta ta kuma dan yin murmushi ta ce" Saura kwana uku, kwana uku kawai ya rage , ina tsoron rigimarta "


Idannuwansa ya lumshe a kasan zuciyarsa yake ayana' Nima ina jin shayin sabuwar Billyna, shin yaya zamu fuskanci junna? Ya Allah ka san ta amsa ba sai na maganta ba, ta sada kai ba sai mun yi gumurzu ba, ta dube ni ba tare da ta kireni abanta ba' 😫



😁😁😁

No comments