Breaking News

A GIDA DAYA 15-16

 


🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾

      🌹A GIDA D'AYA🌹

            🏘️🏘️


🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾


    Story & written by mmn fareesa



🅿️15&16


.....Anty na kitchen tana k'ok'arin had'a breakfast"taji muryan hjy hakimah nacewa"kina Ina ?"ki fito ayita yau ta k'are!saikun fitomun da duk wani abu dakukasan mahmod yamallaka wa wannan y'ar Taki agola.innalillahi wa inna ilaihir raju'un!anty ta fad'a azuciyar"Tada abinda take gudu kenan yafaru..da sauri ta fito dg cikin kitchen d'in"adedenan kuma hjy hakimah ta jingina da bangon parlourn ta rik'e k'ugu.fuskarta bbu annuri ko kad'an" tana jifan anty da wani irin kallo.

       Yyinda Khadija ke tsaye itama fuska jage jage da hawaye"

     Anty ta dubeta tace".lfy meke faruwane??"kafin Khadija tayi mgn.hjy ta karb'e zancen da cewa"K ! karki maidani bansan menakeyi ba"akan kissar dakika koyawa wannan munafukar y'ar Taki"takeyiwa mahmod d'ana nake mgn.sannan dolenku ku fit....ban haifi munafukaba wlh!Kuma insha Allah bazan haifetaba.anty ta fad'a cikin fusata sbd hjy takaita bango.tacigqba da cewa" ya Isa cin fusakar da wulak'ancin dakike Mana agidan nan"K kike rik'e damu ko d'aukar nauyin mune??ban saniba!Dole kikama burgar nad'e tabarmar kunya da hauka."to Bari kiji ke baki Isa intsaya Ina musayar yawu dake ba"sai dai....kinji kunya hakimah wlh"Kuma kinbani mamaki dakika zama sakarai har jummai tazo tamiki iza Mai kantu ruwa.bacin jumman ba k'aunarki takeyiba".cewar inno Kaka (da ummi taje da gudu part nata tasanar mata"kasancewar duk sunji abinda mama jummai ta fad'awa hjy.shine ummi ta je tasanar mata dataga hjy zata nufi sashen anty)


    Shiru kawai hjy tayi "sbd bataso inno tasameta anan ba."


Inno tace".gaba d'ayan ku ,kusameni   a babban parlourn gidan nan"zanyi mgn da mazajenku .sbd su na Isa dasu inban Isa daku ba.zanje dakaina nakira ita d'ayar makirar data had'a husuma ta gudu.(mama jummai)


Gaba d'aya hjy hakimah hankalinta yatashi sbd ganin Abba zaiji kenan"tasan muddin yalura da ran mahaifiyar'sa yab'aci zqta sani.inno tace".aisaiki fito ko anan zaki tsaya nabarki kicigaba da sa'insa da y'ar cikinki?"shiru kawai hjy tayi ta rab'a tafice cike da fargaba.yyinda Khadija hankalinta yasake tashi"sbd ganin itace sanadin komai aganinta.anty ta dubeta tace".kidena kuka ,maza kije kitchen kifito da kayan break fast kiyi.nibaraje naji abinda yafaru"aidama Raina yabani jummai ce ta had'a abun nan.narasa menatsarewa matar nan arayuwa.na yadda da akecewa kishin sauri tafi kishiya"to gashi akaina yafaru.tafad'a tana k'ok'arin shiga bed room d'in ta sbd ta d'akko hijab nata..


Gaba d'aya suke zaune kan carpet"yyinda inno ke zaune kan kujera"cikin b'acin rai tace". da farko dai bello(daddy)dakai zanfara"Allah yabaka shaid'aniyar mace .Bata tsoron Allah ko kad'an "duniyace agabanta itada y'arta zainqb.duk abinda ke faruwa Ina sane dakomai"bana mgn ne sbd naga iya gudun ruwan mutum"inaso hakima kisanar Dani da mutanan dake zaune me jummai tazo tasanar Miki ayanzun bbu jumawa?"

      gaba d'aya hankalin mama jummai yatashi"cikin tsoro da fargaba tace".nifa ba wani abu...inkika sake mgn bakin aurenki"kin Isa mahaifiyata na mgn kinayine.cewar daddy cikin b'acin rai.abba yadubi hjy hakimah yace kiyi mgn ke Kuma kina wasu mazurai...bbu wani b'oye b'oye hjy hakima tasanar da yadda mama jummai tasanar mata da komai.salati daddy yyi" yana kallon mama jummai da kanta ke aduk'e.


wani murmushi inno tayi"kafin tace".ayanzun nasan mikuka fahimta gameda jummai ko?"

To bari kuji"Khadija k'anwar mahmod ce itama.kuma jikatace itama tamkar su maryam na d'auketa.hassada kedamun jummai sbd ganin nata yaran bejawosu jikiba.kinsan inada labarin kindaki hafsat hartayi zazzab'i sbd kawai tana kula yusuf...zaro ido mama jummai tayi"aranta tace"nashiga ukku meke Shirin faruwa dani?"

    Hjy hakimah kuwa Tasha mamakin jin wannan mgn na mama jummai ta daki hafsat akan Yusuf"dama ta lura kafin yatafi akwai shak'uwa Mai k'arfi atsakanin su.wato ita jumman bataso kenan?"dg yau karnakoma ganin k'afafunki kinshigo anan sashen "tunda makirci ke kawoki kidena zuwa..cewar Abba cikin b'acin rai"kafin yakalli hjy yace kekuma babbar banza kinji kunya wlh"ace anzo ankaiki anbaro"dg yanzun kika koma zuwa sashen asma'u da sunan fitna  ranki zai b'aci...hukunci na karshe amatsayina na mahaifin mahmod nazab'a mishi Khadija amatsayin Mata"umarnine ba shawara"karki manta hakimah! muddin kikayi yunk'urin saka mahmod yabijirema umarnina" nikuma zanyi amfani da damata namahaifinsa"  nahanashi auren *khairat*


Atare k'irjin anty,hjy da mama jummai yabuga.anty dai batace komai ba"Amma aranta batason wannan had'in ,insunkoma ciki zata ankarar da Abba yadda zai gane....Masha Allah adamu! Allah yyimaka albarka.wannan had'i yamun dad'i sosai sai y'an bak'in ciki su mutu.koshi mahmod d'in bai Isa yace ah ah ba wlh.sai yarinyar da kika tursasashi  ya aura tazo ata 2.cewar inno tana kallon hjy hakimah..


Daddy yace$. hakane inno"insha Allah zamuje Gurin iyayen Khadija nemawa mahmod aurenta.


Inno tace"hakan nada kyau"sai Abu nagaba kaima yazama Dole ka k'ara aure..

Aure fa kikace inno?"cewar mama jummai cikin subutar baki.tayi sharkaf da gumi"inno na murmushin takaici tace" eh shifa.

Kutashi nasallami kowa.muddin wata fitinar takoma faruwa duk zanbawa kowa mamaki wlh.tana fad'in hakan ta tashi tsaye ta fita.


    Mama jummai har bibbiyu take gani sbd tsabar tashin hankali"aranta tace".tabbas maganar matsiyacin malamin nan yafaru.ita kuwa datasan haka zqi faru dabazo tasanarwa hjy hakimah wani abu ba.bata ankaraba taga bbu kowa aparlourn duk anwatse anbarta.cike da tashin hankali da farga ta tashi dafe da kanta ta nufi part d'insu...


Anty kuwa , aranta ta sha alwashin bazata sanarwa da khadijaba."sai sunyi mgn da abbah.sbd bata fatan had'a zuri'arta data hjy hakimah" zata Kuma dage da addua ,tasaka Yaya Abbas yamata istahara akan lamarin.(yayanta uwa d'aya uba d'aya)

    Tana shiga taji motsin khadija a kitchen"hakan yasa ta wuce bed room d'in ta ,ta d'auki wayarta takira Yaya Abbas"bayanin komai ta mishi.yace"ki kwantar da hankalinki ,adaren yau zanyi istahara insha Allah.abinda ke nan Zan sanarmiki"amma karkiyiwa alh adamu maganar Baki yardaba"bazaiji dad'i ba gsky.da to anty ta amsa sukayi sallama.


****************

Zaune mama jummai take a parlourn ta"gaba d'aya duniyar ta Mata k'unci.abu 2 ke tayar Mata da hankali"na farko k'ara auren da inno tace daddy yyi.na biyu yadda duka iyayen gidan kowa yasan halin ta"ga mutuncinta yazube,zasu cigaba da Mata kallon munafuka kenan" Koda tadena makircinta...


    Mama wai lfy ?"naga tun d'azun kinyi zurfi atunani"cewar zee tana zama kusada mama jummai.hawaye suka zubo mata a kumtunta.cikin tashin hankali zee tace". subahanallahi!dan Allah kisanarmun meke faruwane?"

    Mama jummai na kuka tasanarwa zee komai"innalillahi wa inna ilaihir raju'un!zee ta fad'a arikice"kafin tace".ikon Allah!ita yanzun inno Ina ruwanta dazata ce daddy yak'ara aure?"shiru kawai zee tayi sbd ganin hafsat ta shigo parlourn.hafsat kuwa sarai taji duk abinda mama jummai kesanarwa zee.takumaji dad'in khadija zata auri Yaya mahmod"abu d'aya ne bemata dad'i ba"turke mama jummai da akayi"Amma ita kanta tanaso daddyn yak'ara aure kodan sbd mama jummai tagyara wasu abubuwan da takeyi narashin daidai..


Da dare misalin karfe 8:30 pm"Khadija na zaune gefen katifarta"Kiran Yaya mahmod yashigo wayarta.kasancewar yau sim card d'in yafara aiki."tana duba wayar komai daya faru agidan d'azun yadawo Mata"harga Allah tayi alk'awarin fita harkan Yaya mahmod .sbd mahaifiyar'sa tadena Mata gori"dg wayar har kayan daya siya Mata duk inyadawo zata mayar masa.amma saita shawarci mama"sake Kira yyi akaro na2.....harta tsinke bata d'agaba".

       "Kusan 12 minit ago"saitaji k'arar shigowar text message.tana dubawa taga shine"budewa tayi kamar haka.

*Khadija nizan kiraki   kik'i picking?me hakan ke nufi?raini ne kenan*....

Yah Salam!Khadija ta furta"tana k'ok'arin bin Kiran"saida ta kusa tsinkewa tukum yad'aga beyi mgn ba "sbd tabashi haushi sosai.

    "Ahankali tace".kayi hakuri Yaya dan Allah"bada gangan nak'i picking ba" inada dalil....saikuma tafashe da kuka" harda shashsheka tana kashe wayar.


Yaya mahmod ya rintse ido"yanajin zafin kukanta aransa.afili yace waye yasaminke kuka my khadi?gabansa yafad'i sbd tuna hjy bason Khadija takeyiba...sake Kiran Khadija yyi"amma wayar akashe"hakan yatabbatar mishi da cewa akwai abinda yafaru agidan nasu.tunani yakeyi koya Kira wani yaji meyafaru ko kuwa?"gaba d'aya kansa yak'ulle.


    Hjy hakimah ce kwance a bed room d'in ta.talula duniyar tunani"jitakeyi aranta bazai yuyuba mahmod ya auri Khadija!duk Kuma inta tuna furucin Abba nahana mahmod auren khairat"saitaji gabanta yafad'i.saidai Tasha alwashin Allah yakaimu jibin taji ta bakin mahmod d'in.amma Bata zaton zata iya bari" d'anta dafiso aduniya ya auri y'ar kishiyarta data mallake Mata miji.sannan wani gefen zuciyarta tana mamakin mama jummai akan batason hafsat na kyla yusuf.ummi da Maryam bbu irin tambayar dabasuyi mataba"akan meke damunta amma saitace babu komai..


*Washe gari*


da safe anty da Khadija suna kitchen sbd had'a kayan break fast".Khadija tace".anty inyaya yadawo zanmayar mishi da kayansa da wayarsa...kirki sake ki soma" kinji abinda nagaya maki?"kan Khadija ak'asa tace".naji"anty tace".ko yazo bance kije sashen shiba.inyamiki mgn" kice nina hanaki.kaf gidan nan inaso kiyi nesa da kowa tunda abun yazama haka... ringing d'in wayar anty yasakata yin shiru" tana k'ok'arin d'aga Kiran Yaya Abbas"bayan sun gama gaisawa yace".abinda nakeso dake!kicigaba da yiwa Khadija addua"amma gsky wannan aure bbu fashi"Kuma akwai alkhairi aciki insha Allah.bance kiyiwa alh maganar ba"inabashi yyimiki ba.jikin anty asanyaye ta amsa da to ,tana kashe wayar...


*Bayan kwana2*


Gaba d'aya Yaya Yusuf yashiga damuwa"na rashin maganar dabasuyi da hafsat a waya.duk sadda zai Kira akashe take"gashi yanajin nauyin Kiran hjy yace ahad'asu da hafsat...wata dubara ta fad'o mishi arai"hakan yasa yyi calling d'in hjy.bayan sun Gama gaisawa yace".hjy kina a babban parlour ne?"

    Hjy tace"eh Ina anan "yace"Dan Allah inaso kihad'ani da hafsat "zansakata ta d'akko sak'o d'akina .abokina zaizo ya karb'a"murmushi sosai hjy hakima tasaki nasu na manya.cike da tausayin yaron nata tace" to shikenan bara nasa akirata.cikin farin ciki yace"to"


Hjy kuwa jitakeyi inda zee ce"koda wasa  bazata yarda d'an cikinta ya auretaba.amma hafsat nada halaye masu kyau"tamkar bama jummai bace mahaifiyarta.wani tausayin hafsat taji aranta data tuna ance mama jummai ta daketa akan Yusuf "harda zazzab'i tayi..acikin sa'a kuma hjy taji muryan hafsat nagaida ita"da yuni foam na skul ajikinta."fuska asake hjy ta amsa,tana cewa yauwa hafsat zonan" kikiramun yayanku Yusuf"bangane number saba.da to hafsat ta amsa tana karb'an wayar tashiga contact ta fito da numbesa.kallon hjy tayi tace".akira shi?"eh kirashi manah"bugu 2 yad'auka Yana cewa hjy!hafsat tace hjy yad'aga ai"hjy ta tashi tsaye tace kugaisa Mana bara nazo"batajira cewar hafsat ba,ta wuce part nata.yyinda su ummi da maryam suka k'unshe dariyarsu.kasancewar suna zaune a parlour...


cikin turo baki tace".Yaya Ina kwana?"Yana murmushi yace".bazan amsaba hafsat!sbd kin rainani shine kika kashemun waya ko?tashi tsaye hafsat tayi tana k'ok'arin fita tace".bafa haka bane Yaya"to menene gayamun"cike da shagwaba tace".bakaine kaketa zancen wannan taslim d'in ba.hmmm !nadena zancenta "tunda bakyaso.amma Yaya anan Kano take?"

    Yace"eh"a anguwarmu ma!kokinaso kisanta ne?"da sauri tace".eh Mana"

Hmmmm!kibari ranar Dana dawo zannuna Miki pic nata karki damu.jikin hafsat asanyaye sukayi sallama.shikuwa yanata dariya abinsa.sbd yamata wayo"


Komawa tayi parlourn"tasami su ummi da hjy"ta dubi hjy tace".gashi hjy ,yayan yace"zaikiraki yanzun.hjy tace ".to tana karb'an wayar.nikuwa nace lallai hjy kinso kanki da yawa"meyasa ita Khadija bakya sonta.☹️


Gaba d'aya Yaya Mahmoud Yana cikin damuwa"tun Daren dasukayi waya da Khadija.ak'agare yake yazo gida.hakan yasa yabarwa nura motar yataho da ita"shikuma yabiyo ta jirgi.gurin karfe 12:35 pm ya iso gida.kai tsaye part d'in su hjy ya wuce"bayan yasaka isah driver yakaimishi kayansa abakin k'ofar d'akin sa..

Cikin kamilalliyar muryansa yyi sallama"Yana shiga acikin parlourn"su ummi d Maryam dake zaune suka amsa.suna mishi sannu da zuwa.kallon ummi yayi yace".hjy fa?"

    Ummi tace" tana ciki.part d'in hjy ya wuce"tana kwance kan bed d'in ta"tayi zurfi atunani taji muryansa yana sallama.tashi zaune tayi fuskarta bbu walwala ta amsa sallamar.gabansa yaji yafad'i dayaga fuskarta"hjy sannu da hutawa"yafad'a Yana k'ok'arin Zama kan kujerar dake gaban gadon.


Hjy tace".yauwa" shigo war wuri kayine?"yace eh"

     Tace".dama kuwa inason nafara ganinka ,kafin alh yaganka"dakewa yyi yace lfy dai ko hjy?"tab'e baki tayi had'e da cewa dadai sauk'i"tashiga kora mishi bayani akan komai.tsabar farin ciki. jiyake tamkar yataka rawa".saidai Koda wasa be nuna hakanba"wani k'in mama jummai yak'ara d'arsuwa aransa"inbacin darajarsu Kamal ,wlh shima da kanshi sai yyi maganinta...meye mafita yanzun?"muryan hjy takatse mishi tunani"kallon ta yyi cikin taushin Murya yace".hjy kiyi hakuri kibar Abba yyi komai game dani"nibanason yarinyar nan"kinsan halina banason raini.inma ya auramun ita dg baya nasan yadda nayi narabu da ita.amma yanzun inna bujure bazai ji dad'iba"zaiyi zaton dasaka hannunki.sannan hjy dan Allah kidena d'aukar jita jita"sbd gudun irin wannan matsalar.gashi inno tazo taga laifinki,hakan yyi sanadin daza'a auramun wannan yarinyar ko? tab'e baki hjy tayi tace".waye yajawo ?inba kaiba!na hanaka sakata aiki kak'i ji"aigashi ammanna maka agola ko?"kiyi hakuri hjy dan Allah zanyi .aganinta"hjy tace"ni yanzun bansan Yaya halima zata d'auki wannan maganarba gsky.(mmn khairat)

   Tab'e baki yyi yace"yoyafa hjy?tsoronta kikeyine ?"iyaka kisanar Mata komai ko?hmmmm! mahmod kenan"Allah ya kyau ta.amma Ina sanar dakai karka sake kasakarwa yarinyar nan Khadija fuska.dato ya amsa" Yana cewa"bara naje hjy na watsa ruwa!da haka ya wuce zuwa part d'in su na mazan gidan.yyinda ransa fal farin ciki"Yana yiwa Allah godiya"hade da addu'a, Allah ya Ida nufi khady tazama mallakinsa.


Ruwa ya watsa ,ya kwanta yanata tunanin zuci"kiranta yasake gwadawa yaji wayar akashe.


Afili yace toko tasan da zancen aurenmu ne?"wata zuciyar tace ah ah gsky"kaima inbacin hjy ai bazaka saniba...wayarsa tayi ringing"Yana dubawa yaga Abba ne.cike da girmamawa yyi sallama"abba yace" kana hanya koka iso gida?Yaya mahmod yace".nadawo Abba kusan awa guda kenan.abba yace ok kasameni a parlour na.


Abba na zaune kan kujera"Yaya mahmod yashigo da sallama"yanemi guri akan carpet yazauna.

      Bayan yagama gaida Abba"Abba yakora mishi bayanin komai da komai"Yaya mahmod na murmushi yace"nagode k'warai Abba"Allah yabani ikon rik'eta Amana"Abba na murmushi yace"ameen...dama Abba tuni ya fahimci Yaya mahmod nason Khadija" yak'i nunawane sbd hjy...Abba yace munyi mgn da daddynku sati na sama zamuje nema maka aurenta.ai gara kafara auren ,kafin nan da shekara gudan yyi"kayita zama bbu iyali"iyali su suke k'ara ma mutum mutunci da kima.kuma insha Allah zakayi alfahari da auren nan.yaya mahmod kansa ak'asa bece komaiba.abba yaci gaba da cewa kaga ba'a kaiga sanarma Khadija ba"nabari sai iyayenta sun baka ita.sannan inaso kayi d'an baya da ita"ko aikin dakake sakata kadena.kafahimceni?"Yaya mahmod yace ".eh Abba na fahimta.

      Abba yace". Allah yyimiki albarka"Yana amsawa yatashi ya fita.sbd anfara kiran sallar azahar.


Yaya mahmod nak'ok'arin shiga cikin gidan"su Khadija na k'ok'arin shiga mota"driver yakaisu  skul"da ita yahad'a ido"tamke fuskarsa yyi , had'e da d'auke kanshi yawuce.khadija kuwa batayi mamaki ba"sbd tasan ta mishi laifin kashe mishi waya..


Koda suka dawo dg skul"boye kanta Khadija tayi .sbd batason su had'u balle yasakata aiki"sannan gefe guda ko waiting parlour tadena zama.inta gaisheda hjy bata amsawa "saima tayita zaginta da aibatata.hakan yasa dg khadijar har anty suna cikin damuwa"


*************


Zaune mama jummai take"abin duniya yataru yamata yawa.gaba d'aya daddy yafita harkanta"fushi sosai yakeyi da ita,ko girkinta baya ci"kwana 3 kenan"sannan yasaka Yaya Kamal yyiwa zee mugun duka"akan tanutsu .bayan yace karta sake zuwa o ko Ina sai skul kawai..

Tashi tsaye tayi "ta nufi d'akin daddy.kokarin fitama yakeyi ta shigo" had'e Rai yyi had'e da cewa meyakawoki d'akina?haba alh !wlh bakamun adalci"shin waye kebe kuskure arayuwa ne wai?Dan Allah kayi hakuri koami ya wuce dan allah.murmushi daddy yyi,yace "nahakura ai tuni"tunda mun daidaita da tsohuwar baza warata....tuni mama jummai ta gimtse fuska"cikin b'acin rai tace".banganeba?cikin ko inkula yace abinda kikaji.

No comments