WASU MATAN 7-8
*page* 7~~8
Duke take a bakin murhuu tana fitar wutar itacen duk hayak'i ya cika gidan sakamakon itacen da take amfanii dasuu dan yu ne, duk idanunta sun cika da kwalla, fita kawai take amma wutar taki kamawa sai dan banzan hayakin da takeyiii "sallamar k'anwar ta Salamatuu Tajii tana k'walawa inna Saude Kira, inna inna ga kukar na k'arbo miki, kuma tace nace tana gaishekiii"
Inna Saude Ce dake fitowa daga ciki dakin ta, "tace yanxuu Salamatu Dan kin rainani shine baza ki shiga ciki ki mik'amin shine kike ta k'wallamin kira haka", maganar tace ta katse a lok'acin da hayak'ii ya mata maraba.
"Innalilla'hi wa inna ilaihi raji'oon tafada tare da rafka salati",wanda yasa sai da Aleeya Ta mike tsaye da sauri, "yayin da inna Saude Tace, yanxu Aleeya kina zaune gidannan ya cika da hayak'ii amma ko ki heta wutar nan".
"Wlh inna ita ce nake hetawa tun dazuu cewar Aleeya amma taki kamawa", "ok to bara nazo na heta miki k'ar ki ci gaba da hetawar"cewar inna Saude Tana kok'arin komawa cikin d'akin.
Maganar Salamatuu Ce ta katse mata hanzari yayin da take cewa "ni gaskiya inna nace miki kidaina cemin Salamatuu".
"Salmaat ne suna na fah, amma k'in ki barin kirana hakan, kin maida min suna sai kace na tsoffi tafada cikin shagwabaa".
" Yi hakurii auta bazan k'ara ba kinji", "murmushi salamatuu tayi", "inna Saude Tace ko kefa autaa, tare da shiga cikin dakin ta da ko arxikin ledar kasa bai samu ba balle ai maganar kujeruu....
Salamatuu Ko nace Salmaat Ce ta nufi wurin Aleeya Tana cewa "Addana sannu da aikii",
" yawwa k'anwata harkin dawo daga aiken inna ne"?
"Eh tace tare da cewa Addana wannan wutar ba kamawa zatayi ba,naga da alama itacen nan danyu ne, bara na k'arbo kudii wurin inna na sayo miki yanga", (tafada cike da tausayin y'ar uwarta kan hayakin da take sha).
"A'a barshii kawai kinji!
yanxu wutar zata kama",
"Aa Adda bara na k'arbo dai tafad'a tare da nufar dakin inna Saude, ko sauraren Aleeya Bata tsaya yi ba tashiga dakin tana cewa inna bani kudii na k'arbowa Adda yanga, itacen chan basa ci suna bata wahala sosai".
"Wai auta yaushe zakiyi hankali ne?
"Ko sallama babu xaki fadowa mutane cikin dakii kamar karamar yarinya, baki ga yadda yayarki take yi baaa hala?
"Msstwwwssss" "bana san shirme wlh ta fada tana jan tsakii".
"To ni dai kiyi hakuri dan Allah" kan wannan dalilin tasan halin innar ta ta cewa zatayi batada su, dan shegen son kudin tsiya gareta,shiyasa ma bata biyema fad'an da take mata ba ta bata hakuri, tare da cewa" ni dai dan Allah inna ki bani na sayo mata mana, kinga lokacii na tapiya hudu ta kusa gashiii kuma 5:30 zamu tafii makarantar dare".
"Ah lallaima yanxu hutar ce baza ta kama ba sai an sayo yanga"?
"To kada Allah yasa takama indai sai na bada kudi, ai ubanku ba kawowa ya yi ya jibgemin ba" ta fad'a tana hucii.
Bata rai salmaat tayi dan Allah ya sani tatsane wannan abun da innar ta kema bappan su sai dai ba yadda ta i'ya ne,mai hali baya fasa halinsa in da sabo yaci ace ta sabaa.
"Naji nidai in kina bani ki bani kawai basai kinsaya kina zagar min uba ba cewar salamat cikin baata rai wlh auta kin cika rigima da yawa, girma kike bakya hankali kin mai dani sa'ar ki, ko nace kakar ki, ungo nan dan ALLAH ki fice ki bani gurii" ta fada tare da mika mata naira hamsin.
k'arban kudin tayi tareda fita a dakin tana cewa mungode innataaa.
Nufar wurin murhun tayii da yake cikin fillin gidan domin taa nunawa Aleeya kudinn.
"Addana kinga inna ta bada hamsin a sayo yanga"!
" iyee cewar Aleeya cikin sassanyiyar muryar ta, tana cewa munko gode ALLAH ya kara arzikii, yayin da salmaat ta fita domin sawo yangar wurin idii mai kayan miyaaa.
Aleeya kuwa cikin ranta Alhmdllh take cewa dan bata sa sanmanin inna Saude ta bada kudin yangar ba, domin kowa yasan halin inna saude da mugun son kudin tsiya.In tana tanadin naira hamsin sai kin dauka nera dubuu ce.
Allah ne ya dubeta da idon rahama ya rage mata wannan wahar hashin wutar, ya yin da take saka itace a dayan murhu domin ta d'aura sanwar miya take wannan zancen a zuciyar ta.
Ta amsa sallamar ranta a bace, tana cewa.... "haba haba yaya kabeer a gaskiya ni ba ka kyautamin wlh kayi sallama kaji ban amsa ba ai sai kamin uxurii ko? amma sai kayi ta rangada sallama sai kace mai shela a garii, haba dan Allah taja wani wawan tsakiii.
Duk fadan da yayi niyar yi mata suna hada ido sai ya kasa cewa komi, domin in yana tare da maryam mance komii yake, baya iya tabuk'a komiii sai abunda ta sashii.
"Cikin kwantar da murya yace mata kiyi hakuri" dauke kai kawai tayi ta ci gaba da karatun novel dinta.
kusa da ita yaje ya zauna yana cewa "haba maryama gimbiyar mata ki hakura mana! na bakii hakuri kinkyaleni."
"Inshallah bazan koma ba" (ya fada cikin lalama) "daya fi ma dai" cewar maryam.
Shiru ya yi na d'an wani lokaci....
sannan cikin dakiya yace "Gimbiya gidannan kamar bai ga tsintsiya ba ga kuma kayan wankii chann dana wanke-wanke duk zube?"
"Hakane banga damar yi ba shiyasa" shiru ya yi da bakinsa bai sake cewa komii ba amma cikin zuciyarsa tsuya take yarasa yar da zaiyi da maryam ta zamar masa jidalii a rayuwa, baisan miyasa yanzu ko kadan baya iya ja inja da itaba kamar bashi ba haka yake jin kaine, da yasan yadda zaiyi da ya yi tun tuni, amma ina, ya rasa mafita.
Da yana i'yawa sakin ta zai yi ko ya kara aure dan gsky yagaji da halinta na kazamta.
Gidanta kazam kazam jikinta ma haka ko da yaushe batada aikin da ya wuce karatun littafi ko charting cikin group dinsu da ake tattaunawa kan novels.
"Gwauran numfashi ya sauke tare da mikewa tsaye ya nufi dakinsa.
Kamar yadda ya fita ya barsa haka yake cire tupapinsa yayi tareda shiga bathroom ya watsa ruwa bayan yafito ne ya shafa lotions din sa tare da sa tupapinsa yafara gyara dakin.
Tsaff ya gyara komii ya sharee,yafito palo ma haka ya gyara.Bayan ya kammala gyaran palon ne ya zauna ya dan huta, kafin ya tashi ya fita waje ya samo Almajiri yace masa "ya share masa gidan sannan yayi wanke wanke",ya biyasa kudinsa bayan ya nuna ma sa aikin da zaiyi.
Gidan su ya nufa dake cikin unguwar Runjin samboo domin ya gaida iyayensaaa.
Abangaren A.M.A(haidar) kuwa,bayan ya tashi daga aiki a company,tafe yake cikin motar sa kirar Benz yana waya cikin zazzakar muryarsa, Ahankalii yake driving kamar wanda baya son yin tukiinn.
Waya yake ki da'alama da mahaifiyarsa ce, domin sai narke mata yakeyi kamar mai waya da budurwarsa; chan najii yana cewa "ok momy zan shigoo Abuja inshaallah before next week"shiru yayi a dayan bangaren tayi magana, sai cewa yayi "dear yanxu ina kan hanya ne" banjii mi tace masa ba "najii yace ok bye luv u much my dear" tare aje wayar.
Area dinsu ya nufa dake cikin sama road,wasu jerin gidaje na gani masu mugun kyau, wurin makeken gidan nan na d'azu naga ya nufa tare da danna order, da hazarii mai gadii ya wangale katon gate din gidan ya cilla kan motarsa ciki.
Bayan mai gadi ya kulle gate din da guduu yazo gurin motar haidar dake kokarin fitowa ya durkusa yana mika gaisuwa, amsa masa yayi tare da wucewa cikin gidan,shiko mai gadi ya wuce zuwa aikinsa.
Cikin makeken palon ya nufa tare da sallama kan lips disa, duk da yasan da wuya ta kasance cikin palon koda ma tana nan baza ma taji mi yace ba,hasashen sa ne yazama gaskiya A lokacin da ya isa tsakiyar palon, bai saya bi takanta ba dan duk a tunaninsa tana room dinta.
Uptchairs ya haye tare da nufar room d'insa, yana shiga cikin palon da yafi na d'azu tsaruwa da haduwa nace wow mashaallah... ina mai bin katoton palon da kallo tsaya misilta muku yadda palon haidar yake bata lokacine,bangama karewa dakin kallo ba dga ya nufi wani room na daban a cikin palon, da hanzari na bi bayansa.
Hmmm da ace kudii na magana a duniya da sai sun maganta a wannan dakin, bawai dakin ma kad'ai ba, gidan ma baki daya zai maganta.
Zaunawa ya yi a bakin lallausan bed dinsa yafara cire takalminsa, tare da zare zara zaran yan yantsun kafarsa dake cikin safa ya cire suit dinsa ya daura towel.
Bathroom room ya nufa..... hmmm komi na haidar daban yake, duk da da bathroom din tamkar ka shiga wani palon ne na daban,fita nayi nabashi gurii.
Ina cikin room din ina kalle kalle naji alamun ya fito direct gurin miro yanufa ya zauna bisa kujera yana shafa lotions, shafa wancan..fesa wanchan,sai da ya kwashe 30mint kafin ya nufi wani gurin da duk glass ne baza ka d'auka akwai wani abu a wurin ba.
Hannu naga yasa ya danna wani abu red a gurin, take wannan wurin ya bude, (hmmmmm in ana salla ba'a magana) kunsan mina gani kuwa? wani karamin .........................................✍️✍️✍️
*Zeesardaunerh ce*
( ~y'ar karamar su babbar~ ~su~ 👧🥰🤩)
# _comment_
# _like_
# _share_
No comments