Breaking News

WANDA BAIJI BARI BA BOOK 2 PAGE 1

BOOK 2

           PAID BOOK


_WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE DA NAIRA 100 KACAL ZAKI KARANTA CIKIN KWANCIYAR HANKALI KI BIYA KI KARANTA ABINKI IDAN KINA BUƘATAR VIP WATO POSTING SAU BIYU A RANA ZAKI TURO KATIN 200, *DAN GIRMAN ALLAH ƳAR UWA IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI KARKI SIYA NA YAFE CINIKINKI* ZAKI TURO DA KATIN MTN NA 100 KO VIP 200 TA WANNAN LAMBAR 0706 206 2624 TARE DA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DA KIKA TURO._



Free page     1&2


      Marwan na shiga cikin bishiyar kai tsaye bai tsaya ko'ina ba sai cen tsakiyar da'irar fadarsa, cen maɓoyar sirrinsa ke cikin wani kogon dutsensa, suna shiga ciki ya watsa su da ƙarfin gaske sannan watsa su cikin wani ƙaramin ɗaki, acen kusurwar ɗakin suka hango wata matashiyar budurwa takure a gefe ta kifa kanta cikin ƙafafuwanta tana rusar kuka.


     A zabure kowannensu ya miƙe domin ganin duniyar da suke ciki, Mai Unguwa faɗuwarsa biyu saboda yanda Abayar jikinsa take taɗe yana tashin tana fyaɗoshi ƙasa, Alhaji Babba ne a kusa da shi ganin haka yasa Mai Unguwa miƙa hannunsa domin ya dafa shi, da sauri Alhaji Babba ya fisge jikinsa yana cewa, " Mugu ɗan masara son kake ka taɓani nima Abayar ta shiga jikina ta Allah ba taka ba " 


      Mai Unguwa da har lokacin zuciyarsa a karye take ya ce, " Yanzu haka zamuyi da kai Alhaji Babba? karka manta tun muna yara tare muka taso "

      Alhaji Babba matsawa yayi gefe ya watsawa Mai Unguwa kallon ka rainawa kanka hankali ya ce, " Ka ga wannan? " ya faɗa yana nuna Abba sannan ya cigaba da cewa, " Ciki ɗaya muke dashi uwar mu ɗaya ubanmu ɗaya shima lokacin da yake sanye da wannan Abayar raba hanya mukayi da shi " Marwan da ke gefe a tsaye ne ya buga musu uwar tsawa har sai da kogin dutsen ya girgiza.


      Cen gefe na hango su takure sun rungume juna banda karkarwa babu abinda jikinsu yake yi, cikin wata irin kausashshiyar Murya ya fara magana, " Bana buƙatar surutan banza da wofi duk wanda ya kuma damuna  magana zan ɗauki babban hukunci akansa " 


    Abba ne ya share hawayensa cikin nadama da dana sani ya kalli Marwan ya ce, " Yusra nine Abbanki fa, Yanzu duk ƙaunar da na nuna miki sakayyar da zaki mun kenan karki manta ina iya ɓatawa da kowa akan samun farin cikina "


        Marwan wata irin girgiza yayi take yanayin hallitarsa ta canja zuwa wata mummunar hallita, siffarsa ta koma fasalin ta kare sai dai ƙafafunsa guda takwas ne a madadin huɗu, girgiza ya ƙarayi sai gashi ya dare gida biyu ta tsakiya, harshensa ya zazzago har yana jan ƙasa, baƙi ne wuluk mai ɗauke da jajayen idanu da jan baki daga wajen saman wuyansa wani irin tafkeken ƙaho ne maƙale guda biyu.


    Cikin wata murya mai amo ya ce, " Ni ba ƴarka Yusra ba ce karka ƙara dangantani da jinsin Bil-adam inba haka ba zaka gane kurenka " gaba ɗaya tsumu sukayi aka rasa mai bakin magana, kallan gurin da Matashiyar budurwar nan take yayi ya ce, " Ka ganta cen waccen itace ƴarka kuma duk abinda zaka ce mata bazata kulaka ba har sai na bata umarni, laifinka har yafi na Yusra a gurina domin na tura Babban ɗana yana mun gadinta ta cikin siffar magenku ka nemi ja hallakamun shi, yanzu haka yana cen jinya yake yana jin jiki, kana tunanin zan ƙyaleka a banza ne? " 


      Kallon gurin da Yusra take sukayi gababɗaya suna ƙare mata kallo, Abba sai a lokacin ya ƙare mata kallo har ya fahimci ita ce agurin, wani irin tausayinsa da na ƴarsa ne ya ɗarsu cikin zuciyarsa a take ya fashe da kuka mai cin rai.


       Marwan bushewa yayi da dariyar ƙeta sannan yayi girgiza take ya bi ta jikin bangon Kogon dutsen ya ɓace gaba ɗaya, sai da suka ga ɓacewarsa sannan kowannensu ya fara dawowa cikin nutsuwarsa, Alhaji Babba dake rungume da Mai Unguwa sai a lokacin ya lura, zabura yayi ya fisge jikinsa ya na watsawa Mai Unguwa mugun Kallo.


       A ƙufule Mai Unguwa ya kalli Alhaji Babba ya ce, " Ƙaryar banza ƙaryar hofi tsoronka na ƙarya ne tunda har kake cikin kogon dutsen nan ai maganar tsoron Abaya ta ƙare da ni da ku dik tamu ta ƙare " Alhaji Babba kallon gefe da gefe yayi cikin muryar raɗa ya fara masifa, " Kai ne ta ka ta ƙare amma ba ni ba, mugu mai baƙin baki lokaci kawai nake bawa shakiyin Aljanin nan amma ka jira ka gani. "


     Abba da abin duniya ya isheshi ko tanka musu baiyi ba hakan ba ƙaramin haushi ya bawa Alhaji Babba ba, kallan Abba yayi cikin masifa ya ce, " Auwalu wai kai kaɗai kafi kowa san ransa ne? Ko ka manta kai jikan waye ka manta waye kakanka?  Kai da Aljanu sukewa Kakanka kuka yau kai kakeyiwa Aljani kuka amma tir da halinka ka bani kunya Allah wadaran naka ya lalace..." 


    Alhaji Babba na cikin magana yana marigayin kakansu ya ɓullo ta jikin bango jikinsa sanye da wani farin likkafani.


MASU TAMBAYATA LITTAFIN MARWAN KU TUNTUƁENI TA WACCEN LAMBAR👆🏼




_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉

No comments