WANDA BAIJI BARI BA 25-26
25&26
_Amma sai inshafawa idona toka na gaya mata baƙaƙen maganganu a gabanta, haka nake gudanar da rayuwa har Allah ya raya mana ita ta zama budurwa, ko da ta zama budurwa Yusra na da farin jinin samari amma duk daɗewarta da sauri abu ƙalilan na haɗasu zata yi masa korar kare ta sallame shi, idan ban manta ba akwai samari biyu da har kuɗin gaisuwarsu na karɓa, amma daga baya Yusra ta ce sam bata yarda ba nima kuma babu kunya nace bazanwa ƴata auren dole ba, a lokacin ɗan Uwana Alhaji Babba ba ƙaramin faɗ mukayi da shi ba, saboda cewa yayi bazan maida su ƙananan mutane ba_"
Alhaji Babba na gama jin ta bakin Abba ya ja guntun tsaki a fili yace, " Ay Auwalu ka gama karkaɗarmun da ragowar mutumci na gaban iyaye Saurayin yarinyar, amma ai tayi kai yanzu ko kare take soyayya dashi ya turo iyayensa to shi zata aura " A zabure Umma ta ce, " Kare fa Yaya Babba? "
Alhaji Babba tsuke fuska yayi yace, " Eh Kare, ko ban isa ba? "
Yusra da ke gefe lokaci guda idanunta suka juye zuwa jawur baku ko ɗigon fari, cikin wata irin gwamamniyar murya ta kalleshi ta ce, " Ashe kuwa zaka mutu domin duk duniya bayan ni babu wanda zai auri Yusra, dan haka gaba ɗaya ku iya bakinku akanta "
Tsit kake ji ko motsi babu wanda ya ƙara yi, Alhaji Babba wani irin gumi ne ya ke ta keto masa ta ko'ina, Abba sunkuyar da kai ƙasa yayi cikin damuwa yana tausayin halin da ƴarsa take ciki.
Umma dake kusa da Yusra banda goge hawaye babu abinda take yi, Malam Liman jiki a sanyaye ya cewa Abba, " Malam Auwalh muna jinka "
Abba ya cigaba da cewa, " _Sai da muka shafe wani lokaci sannan muka daidaita da ƴan uwana haka ma maiɗakina alokacin ba ƙaramin fushi tayi domin kullin maganarta ɗaya, wannan soyayyar da nake mata akwai lokacin da zanyi nadama, Na ɗora Yusra akan wata banzar ɗabi'a duk abinda ta gani tana so indai tace na saya mata to ko bani da kuɗi zanci bashi nayi mata domin na faranta mata, daga baya idan ta ce nayi mata abu nace bani da kuɗi tofa daga ni har mahaifiyarta babu mai kwanciyar hankali._"
" _Kwatsam ana cikin wannan yanayin sai ga wannan yayi na ABAYA ya shigo..._"
Mai Unguwa ne ya katse Abba, " Ai kaima gashinan kabi sahu na masu yayin Abayar " Ya ƙarasa faɗa yana tuntsirewa da dariya.
Yusra na gefe kallan tsaf ta gama yiwa Mai Unguwa, ƙasa-ƙasa take faɗan wasu kalmomi idanuta ta maida kan Abba da yake kallan jikinsa, dan shi tunda ake zancen yasa Abaya bai taɓa ganinta ba sai yanxu, yana tsaka da duba jikinsa sai ji yayi Abayar ta zame ta tashi ta sama, duba kayansa yakeyi sa a wannan lokacin mutane suka ganshi cikin shigarsa ta magidanci.
Kallo ne ya koma kan Abayar take kowa ya fara tunanin inda Abayar zata nufa, kai tsaye ɓangaren su Malam Liman nufa, bata bi ta gurinsa ba ta zagaya ta baya zatayi kan Mai Unguwa.
Gabanɗaya sunan ganin haka kowa ya cakumo babbar rigar Malam Liman, gida biyu suka kasu da ƴan ɓangaren Alhaji Babba da ƴan ɓangaren Mai Unguwa, idan suka fusgo Malam Liman ta nan sai waɗancen ma su fisgeshi ta cen kowa ƙoƙarinsa na ganin ya shige cikin Babbar rigar Malam Liman.
_🤣🤣🤣🤣MALAM LIMAN KAGA TA KANKA_🤣
_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
ƊANƊANO DAGA SABON LITTAFI NA
PAID BOOK
Littafin nan na kuɗi ne da naira 200 ki zaki karanta shi cikin nutsuwa, game buƙatar ƙarin bayani zai iya mun magana ta wannan number 0706 206 2624
ANYA BAIWA CE?
NA
AMEERA ADAM
Free Page 2
Wani mudubin tsafinsa ya ɗauko yasa wata jelar ɓauna dake hannun sa na hagu cikin ƙwaryar ya yarfawa mudubin, inuwar wani ɗan ƙanƙanin Yaro ce ta bayyana na ɗan wani lokaci sannan ta ɓace, maida mudubin yayi gefe sannan ya maida kallonsa ga Fulani Maryama ya ce, " Alƙalami ya riga da ya bushe, duk duniya babu wani ko wata da zai iya dakatar da cikin jikinta har sai ta haifeshi, Zata haifo Ɗa namiji Mai kama sak da Mahaifinsa kuma koda baki ci wannan Alwashi ba haihuwa ta dakatawa Sarki Aminullah, duk wacce kika ga ta kuma haihuwa sai dai idan wani ne mahaifinsa ba Aminullah ba "
Cikin damuwa Fulani Maryama ta ce, " Yanxu babu wata mafita da zaka bani ya Shugaba na?? "
Wani Allon jar ƙasa ya ɗauko ya jingine ya na faɗan waɗansu irin kalmomi, yana watsa wani tafasashen jini dake cikin wata ƙoƙon kan Ƙwarangwal, yana cikin haka baiyi aune ba sai gani sukayi Allon jar ƙasa ya ruguje wani irin hayaƙi mai wari na fita daga jikinsa.
A tsorace gaba ɗaya suka ja baya Marduska ba ƙaramin tsorata yayi da ganin faruwar haka, cikin yanayin firgici ya fara magana, " Tabbas Ruhin wasu ababen hallita na katange da shi, idan na matsanta halaka shi ba mu ba hatta Aljanun da suke taya ni aiki sai sun halaka, maganin kar ayi kar afara inba haka ba wanda baiji bari ba yaji woho "
Fulani Maryama jikinta ne ya gama sanyi amma duk da haka zuciyarta bata karaya ba ta ce, " Marduska abar batun Halaka shi tunda ni kaina ganau ce ba jiyau ba, amma bayan haihuwar sa ba damar a sace shi daga cikin masarautar ko kuma a nakasa shi? Ina nufin a ɓatar dashi daga nahiyarmu gaba ɗaya "
Matsawa yayi bakin wutar dake ci ya ɗebo wani garin magani mai haɗe da garin naman mage da haƙoran jemage ya zuba aciki, take wutar ta kuma tashi sama sannan wata ƴar ƙaramar ƙorama ta bayyana aciki, daga cikin ƙoramar wasu litafan tsafin ya ɗebo guda biyu ja da baƙi, baƙin ya fara jefawa cikin wannan jinin dake cikin ƙwarya sannan ya zura kansa yana karewa Ƙwaryar kallo dake ta zaɓalɓala.
Sai da ya gama kallo tsaf sannan ya ɗago da kansa da yayi gumi sharkaf ya fara mata bayani, " Tabbas cikin biyun za'a iya gudanar da ɗaya amma biyun bazasu iya wanzuwa akanshi ba, zamu iya nakashi ta kowacce siga haka nan zaki iya sawa a fitar dashi daga cikin masaurautar amma shi ne kuskuren da zaki fara tafkawa a rayuwar ki, domin kuwa ta wannan silar dukkan asiran da kika binne za'a binciko domin kuwa allura ce zata tono garma"
Fulani Maryama harta fara jin daɗi ƙarshen maganarsa ya sa ta shiga damuwa, kallansa tayi cikin rashin fahimta ta ce, " Bangane mai kake nufi ba? " mayar da ƙwaryar yayi cen gefe ya ce, " Abinda na gani kenan zaɓi ya ragewa mai shiga rijiya..., kowanne zaɓi kika ɗauka yana da nashi ƙalubalen da zaki fuskanta ki nutsu da kyau ki saurare ni inba haka ba zakiyi gudun gara ki faɗa gidan zago "
Jakadiya dake gefe tayi tsuru sai raba idanu ta ke cikin zuciyar ta ta ke faɗin, " Lallai Fulani Maryama kema ba ƙaramar makira ba ce, amma ajuri zuwa rafi....., Ai bahaushe ya ce inzaka gina ramin mugunta gina shi gajere, amma lallai wannan Ɗa na Zaliha ya zama kainuwa dashen Allah, wata ƙila shi ne zai zama magajin Izza muga ta tsiya, dama ance kayun Ɗan ƙwarai ya gaji Ubansa "
" Ina sauraren kowacce kalma da zata fito daga bakinka kuma kowacce zan saka ta amazaunin da ta da ce " Fulani Maryama ta faɗa.
Miƙe ƙafafunsa yayi da gaba ɗaya gashi ya rufe su sannan ya fara mata bayani, " Zabi na farko zamu iya baki garin maganin da za'a zuba masa a ruwan wanka, sai kuma na turare wanda ita Zaliha tana fara Naƙuda zaki turara mata, karki bari yaro ya faɗo ba tare da kin turara shi ba, to idan kika yi haka bazai iya gani ba, baizai iya tafiya ba da magana ba ke komai da kika sani sai dai ayi masa, saboda zai kasance a kwance sai dai duk abinda za'a furta zai ji shi babu abinda zai iya wanzarwa "
Murmushin jin daɗi Fulani Maryama tayi ganin haka yasa boka ya ce mata, " Sai dai akwai sharaɗin da zaki kiyaye, akwai wata da na gani tana jingine da shi, zata shigo cikin gidan masarautar ku tana ƙasƙantacciya kuma Baiwa muddin kika bari ta shigo cikin gidan sarautar, abubuwa marasa daɗi zasu fara faruwa gareki kuma duk ranar da tayi tozali da shi, a ranar aljanun dake riƙe da ƙafafunsa zasu tarwatse alƙadarinsu zai karye, idan kika yi sake ta ɗau wani abun ci ko abin sha ta bashi da hannunta to a ranar suma aljanun da ke riƙe da bakinsa zasu gushe zai fara magana, sai dai aranar zai fara wani irin ciwo kamar zai mutu zai yi ta amai ba ƙyaƙyƙyautawa kamar zai amayar da ƴan hanjinsa, hakan zai ɗaga hankalin Mai martaba har yasa anemo wanda ya bashi wani abu tunda shi zaiyi tunanin guba ce aka bashi, amma ba haka bane amayar da gubar da take jikinsa yake ta tsawon shekaru da zaki bashi "
Ajiyar zuciya Fulani ta sauke sannan ta ce masa, " Wace ce yarinyar? Kuma daga wane gurin zata xo? Babu damar dakatar da zuwan nata? Ya za'ay na gane ita ce dan na ɗauki matakin daya dace akanta?? "
" Daga ni har sauran matsafan duniya babu wanda ya isa ya ja da yarinyar domin ita ɗin FILSIFI ce, abinda muke kira da FILSIFI kuwa aharkar bokan ci, tarraya ko haɗakar shuɗaɗɗun ruhika mabanbanta daga jinsi Mabanbanta, zo ki duba nan " ya ƙarasa faɗa yana buɗe mata wannan jan littafin da ke gefensa.
SALON LABARIN DABAN YAKE🌚🌚🌚 KU GARZAYO KARKU BARI BAKU LABARI🌚🌚
_BINT ADAM CE_😉
No comments