Breaking News

WANDA BAIJI BARI BA 21-22

                     21&22

        A hankali ta juya tana nuna wa su Arrama halin da ta samu Yusra a ciki, ƙarasawa sukayi suka sameta kwance kamar gawa, gaba ɗaya jikinta yayi ruɗu-ruɗu wasu guraren duk sun farfashe abinka da farar mace jikinta duk yayi jawur, ta gefe guda duk ya tattashi jikinta ya kumbura.


     Su Arrama na juyo da Yusra Umma ta fashe da kuka saboda halin da ta ga ƴarta ta tana ciki, tsoro ne ya ƙara kamata lokacin  ta ga fuskar Yusra ta zama kala biyu, gefe ɗaya yana nan yanda yake sai kuma gefe ɗaya da ya rine yayi jawur.


     Ruwa suka Umarci Umma ta ɗebo musu a kofi, ba musu da saurinta ta juya ta ɗebo ruwa har tuntuɓe take kamar zata faɗi ta miƙa musu, Aramma ne yayi ta addu'a yana tofawa sannan ya fara yayyafawa Yusra.


     Duk saukar ɗigon ruwa jinsa take a jikinta kamar saukar garwashi, aikuwa a zabure ta miƙe da ke jikinta ba ƙwari faɗuwa ta ƙarayi sai, muryarta har ta dashe amma a haka take iya kururuwan neman taimako.

 

     Da sauri Umma ta ƙarasa ta riƙeta tana mata sannu, gaba ɗaya ba wanda bai tausayawa Yusra halin  take ciki ba, Armma ne ya cewa Umma, " Ina ganin idan zata iya ki kamata mu je gurin Malam Liman hakan zaifi sai a san abin yi "


    Umma kallan Yusra tayi ta ce, " Yusra zaki iya zuwa ƙofar gidan Mai Unguwa "


     Yusra da sauri ta rungume mahaifiyarta tana cewa, " Eh Umma nidai muje duk inda zamu amma dan Allah karki barni a gidan nan wallahi Marwan kashe ni zaiyi " 


      Cikin haɗin baki suka ce, " Marwan? waye kuma Marwan? " Yusra da har zuwa lokacin bata cikin nutsuwarta ta ce, " Ni tsoro nake ji Umma amma dan Allah mu fita daga gidan nan " ganin yanayin da Yusra take ciki yasa Aramma yace, " Ku ƙyaleta mu tafi, amma ki riƙe ta sosai " 


      Umma riƙe Yusra tayi ta rungumeta sosai a jikinta a hankali Yusra take takawa saboda tsamin jiki, a hankali suke har suka ƙarasa wajen faɗar Mai Unguwa.


    Tun daga nesa mutane suka zuba musu ido suna kallo har suka isa gurinsu, daga jikin bango aka zaunar da Yusra lokacin Abba ya wartsake daga  halin da ya tsinci kansa aciki, Fadar Mai Unguwa ta kuma cika fiye da lokacin da su Umma suka tafi saboda labari ya zaga gari, kowa burinsa yazo ya bawa idonsa abinci.


     Yusra na zama mutanen gurin suka zuba mata ido a taka wasu daga ciki suka fara ƙus-ƙus, Yusra na haɗa ido da Malam Liman ta sunkuyar kai ƙasa, Malam Liman kallon tsaf yayi mata take tausayinta ya kamashi.


        Malam Liman magana ya fara yi mata, " Malama Yusra ɗago ki kalleni inasan magana da ke " shiru tayi bata bashi amsa ba, maimaita mata yayi amma tayi biris kamar batasan ma yanayi ba.


      Malam Liman sarai ya lura da halin da take ciki ga dukkan alamu har zuwa lokacin a kwai JINNU a jikinta, murmushi yayi ya ɗauke kai gefe ya kalli Abba ya ce, " Malam Auwalu ga ƴarka Yusra mun kawo meye dangantakar halin da ka shiga da yanayin da take ciki "


      Abba numfasawa yayi sai da ya ƙarewa Yusra kallo ƙwallah tana zubo masa ya ce, " Tabbas Matsalar mu na da alaƙa, kuma ba kowa bane silar faruwarta sai ni Mahaifinta " 


   Gaba ɗaya gurin idanu suka zubo masa dan jin abinda zai fito daga bakinsa.


    Alhaji Babba kallan ƙanin nasa yayi yace, " Ai ni nasan duk tsiyar da shaiɗaniyar yarinyar cen take shukawa kaine kake ɗaure mata, hatsabibiyar yarinya mai fuska kamar ta kyanwa Zaki ci Ubanki ranar da kika shiga hannu na..." 


     Maganar Alhaji Babba ce ta maƙale lokacin da ya ga wani hayaƙi na fita daga idon Yusra Mai kama da harshen wuta.




      _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉

No comments