Breaking News

WANDA BAIJI BARI BA 19-20

                  19&20

           Abba zaro Idanunsa yayi yana kallon Alhaji Babba sai dai  bai kawo komai ba, yayi tunanin ko wahalar da yasha ce tasa idanunsa suke masa gizo, Umma da ke gefe kafe Abba tayi da idanu saboda gaba ɗaya kanta ya kulle tsoro da mamakin abun da ya faru ne ya kama ta, musamman da ta ga irin siddabarun da buhun ya dinga yi daga ƙarshe kuma sai ga Abba ya fito.


     Gurin shiru yayi Malam Liman ya kalli Abba ya ce, " Malam Auwalu kai kuwa mai yake faruwa haka gaba ɗayanmu nan munga abinda ya faru kan idanunmu sannan na ganka ɗaure da guru da wasu sauran kayan tsubbu, mai ya kaika cikin buhu ko wani laƙanin aka baka ne? " 


       Abba banda numfashi sama-sama babu abinda yake yi, a wahalce ya cewa Malam Liman, " Malam Liman a taimaka mun da ruwan kafin nayi wani ƙarin bayani " Tukunyar ƙasar dake gefen  rumfar majalisar Mai Unguwa Malan Liman yasa aka ɗebowa Abba ruwa, sai da ya sha yayi ƙat sannan ya ɗauke kansa daga kofin, idanu gaba ɗaya kansa suka dawo yanayinsa duk ya bawa mutanen gurin tausayi, jingina yayi da jikin bishiya sannan ya ce, " Malam Kafin nace komai dan Allah a nemo min ƴata yusra, Allah yasa basu kashe mun ita ba " sai a lokacin Umma tayi farat ta ce, " Ameen dai Malam wallahi Yusra na cikin wani hali ɗazu da na baro gidan anrufeta a ɗaki sai duka ake "


        Sai a lokacin Malam Liman ya tuna da maganar da Umma tazo masa da ita da yake kowa baya cikin kwanciyar hankali, Malam Liman kallan Saminu yayi ya ce, " Saminu ko za'aje a taho da Yusra " Saminu tsuke fuska yayi ya ce, " Allah gafarta Malam kanaji ance tana cen zaneta ake amma ni a turani " 


      Mai Unguwa sai a lokacin ya ɗago ya ce, " Kai Saminu Gafarta Malam yana magana ana musa masa, rashin ɗa'a zaka nuna mana " Mai Unguwa yana rufe baki Alhaji Babba ya ɗauka, " Ni bansan lokacin da yaran yanzu suka lalace da rashin ɗa'a ba, yara basa ganin uban kowa da gashi abun har ya fara zuwa kan Ulama'u magada Annabawa, kai Amma Allah wadaran naka ya lalace tir da halinku " 


     Saminu duk inda ɓacin rai yaje ya kai nan, saboda irin maganganun da su Mai Unguwa suka gaya masa cikin jin haushi ya ce, " Tun da ni bani da ɗa'a ku masu ɗa'ar ai sai kuje maganar gaskiya kowa ai kansa ya sani haka kawai naje a halaka ni, naga kai ranka shi daɗe da aka ja ka zuwa sama ba ihu ka dinga yi ba sai da ka tafi da ɗan rakiya, amma ni ka tura ni inda ake dukan mutane " 


      Mai Unguwa a harzuƙe ya fara magana, " Kai Saminu ni kake gayawa haka? Wallahi dole horo mai tsanani ya hau kanka  " Alhaji Babba ya ce, " Eh tsageranci zai nuna mana ba ya ga mun zauna shimfiɗa ɗaya ba " 


    Saminu ɗauke kai gefe yayi yana maganganu ƙasa-ƙasa alamar magana mara daɗi yake faɗa akan su Alhaji Babba, Malam Liman yana ganin tarzomar tayi yawa yace, " Shikenan a bar maganar ni bari nabi mahaifiyar yarinya muje na gani " Mai Unguwa na ganin Malam Liman zai miƙe da sauri ya dafe ƙafafuwan sa yana cewa, " Ka dubi Allah Malam Liman karka barmu agurin nan " Malam Liman yana shirin magana sai ga Hulunan su Alhaji Babba da rawanin Mai Unguwa nan sun dawo, suna ganin tahowar hulunan kowa yasa hannu yana dafe kansa, Mai Unguwa da Alhaji Babba har rige-rige ɗaga babbar rigar Malam Liman suke wajen tura kansu ciki, cikin akasi kuwa suna saka kawunansu ciki suka yi gware kusan tare suka furta, " Wayyo Allah " cen gefe hulunan suka warwatsu kowanne da inda tashi ta kalla, Rawanin Mai Unguwa cen bakin wata kwata ya faɗa tare da hularsa.


      Malam Muhammadu ne ya cewa Malam Liman, " Allah gafarta Malam bari muje nida Aramma mu taho da ita " Gyaɗa kai Malam Liman yayi sannan ya cewa su Mai Unguwa, " To ku ɗan sakeni na zauna tunda su Aramma ne zasu tafi " Ba kunya sai ga su Alhaji Babba sun fito kowanne yana muzurai, sauran mutanen gurin sai a lokacin suma suka samu sukunin ɗago da kansu suna kalle-kalle.


      Aramma da Malam Muhammadu ne suka tashi suka tafi suna gaba Umma na biye dasu a baya har suka ƙarasa, a ƙofar gida suka tsaya Umma ta yi musu iso suka shiga lokacin da suka shiga gidan shiru suka ji kamar babu kowa a gidan, ahankali Umma take tafe tana leƙawa da ka ganta zaka lura da halin tsoron da take ciki, tana zuwa ta tura ƙofar ɗakin da Yusra take ciki.


       Cikin tashin hankali ta zaro idanu musamman da idanunta sukayi mata mugun gamo.


INA MUKU FATAN ALHERI SISTERS🥰🥰🥰🥰


_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉

No comments