Breaking News

SAI A LAHIRA 13

 


*🎀SAI A LAHIRA🎀*


              *NA*


*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*



               *🅿️age 13*




*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*



*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu'ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*



_ga hanyar da za'a bi Dan siyan book dina HAWAYE  1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_



_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_



 *_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*





*_Ni kuwa me zancewa masoya? Banda kalmar furtawa bare godewa Allah ya Kara rufa man aisiri yasa mu gama lafiya_*






..........Duk yadda malam lamis yaso kulluwar auren nafisatu da mujahid Dole ya ajiye makamanshi tunda Azumi tace Bata San zancen ba wacce gareshi ? Abu daya yasa nafisatu Bata marawa mahaifin ta baya ba shine gaskiya sadik take so Amma da ta rufe ido ta fidda shi kunya 

Dama manufarta da cewa ya Bata lokaci don tasan yadda zata zame sai Kuma Allah ya Bata sa a wani sanadi ya ratso


Maganar mujahid tabi ruwa inda soyayya da sadik da nafisatu taci gaba duk da kasancewar sadik almajiri ne marar karfi sai dai Yana aikin makanike Yana gyaren mota Kuma Allah da ikon shi yasaka mishi nasibi me yawa kasancewar ya iya gyaran sosai Yana Kuma da manyan kwastomomi masu kawo mishi gyara suna Kuma yi mishi ALHERI me yawa fiye da kudin gyaran shi don haka asirin shi arufe 


Sai dai agefe Daya sadik bashi da kwarjini ko na sisin kwabo wurin Azumi kullu cikin kushe shi take 


"Haba me ake da AUREN fakiri irin wancan kullum cikin bakin Mai yake Ni Banga tsiyar da Kika gani akanshi ba ko dayake dogon hancin shi ke rudaki.

Ita dai nafisatu Bata tankawa sai dai tayi shiri abinta don ta gama Gane Azumi so take tayi AUREN kece Raini da miji irin na nunawa tsara Sai dai ita har ga Allah tafi son auren miji me rufin asiri akan me shahara saboda ance masu kudi da yawan su auren su ba hutuwa bace matsaloli ne jibge cikin gidajen su don haka take Jin sadik ne daidai da ita.


Ta dire wa malam lamis kwanon tuwon Wanda saboda tsabar Raini hade mishi tuwon da Miya take don bashi da arzikin da zata bashi tuwo daban Miya da ban Amma duk da haka baya kulawa


Ya Kai lomar farko inda yaji miyar babu gishiri bare Dan magin ajino Moto miyar ta tsurar kukace wadda ko arzikin daddawa Bata samu ba 

Yaso ya tura haka Nan Amma ya Gane ko zai ciwo to sai ya saka gishiri don miyar daga ruwa sai kuka don haka ya nemi a taimaka mishi da gishiri

Azumi wadda ta ke juye girkinta da tayi na daban na shinkafa da taliya ta juyo ta dubeshi


"Dama ka siyo gishirin ne ka ajiye? Ai ban boye maka ba duk yadda kaga na dama maka haka zaka Sha  

"Ba zaiyuwu Ni kullum cikin yi maka cikon cefane ba yadda ka kawo haka Zan girka maka 


Nafisatu najin su don haka tafice ta siyo mishi gishirin ya karba Yana saka Mata albarka sai dai a wannan fitar da tayi Ashe kaddarace ta fito da ita kaddarar da itace silar faruwar abubuwa masu yawa


Tana Zama yaro ya shigo yace Wai ana sallama da nafisatu

Azaton ta sadik ne sai tace aje ace tana zuwa

Azumi taja tsaki  "Kai Allah yasa wannan yaro da shegen naci yake , shegen zance Babu ko sisi sai tsayuwa da karairayi mtsss ta Kuma Jan tsaki, nafisatu ta fito da farin ciki tana murnar ganin sadik sai dai katuwar motar tayi Mata marhabin

Ya fito daga cikin motar Yana Kare Mata kallo inda itama tabishi da kallon wa ye yake kiranta? Ganin ya durfafota yasa ta yarda shine me kiranta.


"Sannu nafisatu Kinga bako Babu sanarwa ko? Ya fada Yana murmushi, ta subkuya ta gaisheshi inda ya amsa Yana karewa fuskar ta kallo lallai Ashe baiga kyawunta ba sai yanzu da yake gabanta 

"Nafisatu gani gabanki naganki ne yanzu ba da jimawa ba Allah da ikon shi Kuma na biyo bayan ki Kuma idan kin  yarda da soyayya ta aure nake so muyi don Ni dai nagani Kuma Ina so. "Da farko dai Ni sunana Alh  bilya barda na mallaki kudi da kaddarori Wanda Ni kaina ban San adadi ba idan har Kika aure Ni duk wani Jin Dadi da Mata ke fatan samu gidan mazajen auren su to Zaki same shi agidana fiye da zatonki shekaruna talatin da Tara saura kadan in cike arba in don haka Zan Baki dama kiyi nazari da shawara akaina in yaso sai ki dibar min lokacin da Zan dawo


Tayi shuru kamar ba zata tanka ba sai Kuma tace mishi

"To Alh na gode da kauna da soyayya sai dai maganar gaskiya an tsayar min da mijin aure sai dai in baka hakuri Allah ya hadaka da wacce tafini nagode kwarai da kauna da soyayya Ina Yi maka fatan alkhairi sai sa da safe

Tayi nufin komawa gida Amma yayi saurin tareta

"Ji Mana nafisatu bakiji abinda nace Miki bane nifa me kudine da Babu abinda ba Zan iyayi Miki ba kar kiyiwa kanki katankatana Mana mutuwar almuru.

Ta bishi da kallon mamaki

"Ai Ni bana kallon daular duniya amatsayin itace Jin dadin Rayuwa. "Jin Dadi na hakika shine samun abinda kake so don haka don Allah ka fahimce Ni Kuma ance kwarya tabi kwarya  nagode sai da safe Bata sake sauraren shi ba ta shige gida abinta 

Ya dubi agogon hannun shi goma saura kwata ba don yasoba ya SHIGA motar Yana kallon gidan kamar zai Kuma hango ta tafito

Sai dai duk yadda yaso ya runtsa bacci abin ya gagara da ya runtse idon shi fuskar nafisatu yake hangowa bai samu bacci ba sai dab da asuba shima baccin kaf din shi mafakin nafisatu ne inda yagane son yarinyar ba da wasa yake Shirin gana mishi azaba ba  shi da kanshi yasan son nata daban yake da sauran Matan da ya aura daya bayan Daya har Tara babu wadda yaji son ta irin na nafisatu Amma Kuma Wai ita din duk cikar shi da batsewar shi baiyi Mata ba

Inda yake jin shi Kuma indai kudi na maganin damuwa to sai ya aurota ko da son ko Babu don ya yarda cewa kudi Babu abinda basayi haka Kuma Babu yaren da basaji abinda baya yuwuwa ma sukan iya maidashi me yuwuwa sai kawai yayi murmushi don har ya soma hango nafisatu acikin gidan shi Kuma matar AUREN shi.....

No comments