FURUCI 27-28
🅿 27 to 28
Sha tafarayi setaji yanayin ruwan yacanza saurin cire robar ruwan tayi daga bakinta tasake dubawa jitayi cikinta yafara d'aukar zafi zaro ido tayi dandanan tarud'e tafara salati kafin wani lokaci tuni cikinta yafarayin wani irin mugun ciwo miqewa tayi zata fito amma ina kasawa tayi cikin tana neman
kasayin magana yasa tasaki ihun Kiran Maher sede Kuma shi yayi nisa cikin bacci shiko doctor yanaji amma yayi banza se murmushi kawai yakeyi sosai Iftahal tasake sakin kuka tana fad'in " Maher dan Allah kazo mutuwa zanyi kazo kafin namutu kacemin kana matuqar son wannan babyn dan Allah Prince " tasake qwala kiran kamar cikin mafarki yafarajin Kiran IftahalAhankali yabud'e idonshi sakejin kiran yayi cikin kuka tashi yayi zaune jikin shi duk babu 'karfi sabida baccin bai isheshi ba jiyayi tace " wallahi Prince idan narasa taimakon ka a wannan lokacin mutuwa zanyi shikenan zanmutu batare da Abbana yayafe min ba nashiga 3 "
Cikin sauri Maher yamiqe yafito yana sakkowa qasa yaga doctor zaune a parlour cikin mamaki yatsaya cikin zuciyar shi yace " kode kunnuwanane da dagaske ne ayda doctor yaji dakuma yakirani hmm wannan ciwon nawa kullum sake saban abubuwa yakeyi " juyawa yayi zaikoma dede lokacin yaji muryar ta cikin galabaita tace " Prince dan Allah katashi a wannan baccin kazo gareni kafin namutu "
Cikin sauri Maher yajuyo ya'idasa sakkowa saurin miqewa doctor yayi ganin Maher kallon mamaki yayi mishi sabida yasan wannan allurar bazatabar shi tashi yanzuba Koda kuwa tabarshi yatashi bazai iya fitowaba sabida gaba d'aya ga'bo'bin shi zasu kasance babu qarfi cikin rawar murya doctor yace " Prince lafiya kuwa ? " Wani irin kallo Maher yayi mishi yanufi bedroom d'in Iftahal yana shiga yaci karo da ita kwance saman carpet tariqe cikinta cikin sauri yaqarasa gareta ya tallafota da qyar tad'aga idanta takalleshi tace " dan Allah kakani asibiti " daga haka takasa qaracewa komi cikin razana da furgicin halin daya ganta yayi saurin surarta yafito da ita ganin haka yasa doctor saurin miqewa yanufo yace " Yaya meke faruwa ? " Muje kwantar da ita saman cushion naduba muga maiye matsalar ahankali Iftahal tace " a a Prince nayi imanin shine yasamin guba cikin ruwan danasha seyake yakasheni karka bari yadubani kakeni asibiti dan Allah " cikin yaran Araf take fad'amishi duk wannan shiko doctor baisan abinda takecewa ba wani irin mugun kallon yawatsamishi yace
" Niba sakare bane dazan yarda wani qato yata'bamin mata " daga haka yanufi hanyar fita dasauri yana qwala kiran Shanwul cikin sauri Shanwul yahayo saman karo yaci dasu cikin tsawa Maher yace " jeka tada mota " aguje Shanwul yajuya kafin su sakko tuni Shanwul yatada mota suna sakkowa akabude musu qofar motar suka shiga Shanwul yaja aguje sosai jikin Iftahal yayi sanyi addu'a kawai takeyi shiko Maher yakasa d'auke idan shi daga kanta ahankali tace " Prince Abba na dan Allah Koda namutu kasashi yayafemin wayyo Allah Ummina " kamo hannun ta yayi cikin tausayawa yace
" Babu abinda zai sameki kinji zakiga yafiyar su in sha Allah " suna isa aka amsheta cikin gaggawa aka shiga da ita hana kowa shiga sukayi amma Ina Maher yaqi dole suka barshi tsayin lokaci suna binciken matsalar sannan suka gane qwayar datasha allurori suka shiga yimata shigo wani doctor yayi hannun shi riqeda allura zaiyimata maher yayi saurin riqe hannun shi yace " namiji baya saka hannun shi saman jikin matata bama doctor Sera ko doctor Alina tayi mata sannan kafita "
Ganin babu alamar wasa afuskar Maher yasa doctor yamiqa allurar yafita tsayin lokaci sannan doctor Sera tadubi Maher tace
" Guba madam tasha Kuma mai matuqar had'ari sede anyi sa'a kad'an tasha kuma ankawota asibiti cikin lokaci gashi tanada ciki Allah yatsare su daga ita har babyn yanzu zatayi bacci sosai idan tatashi zatayi amai sosai daga nan zata koma dede "
Jinjina Kai kawai Maher yayi Amma maganar babyn datayi yasashi jin 'bacin rai sabida yatsani tuna wannan kalmar wani irin kallo yayi mata yaja tsaki afili yace " Ni tayaya zan amshi wannan babyn inada tabbacin banida alaqa dashi Iftiih!!! bari kitashi sekin sanar dani uban wannan cikin Kota halin yaya inada masifar kishi sabida haka bazan iya zama dakeba dama can babu niyyar hakan cikin zuciya ta "
Shiko Shanwul dake waje Yana ganin fitar doctor yabita har office bayan tazauna yace " doctor maike damun Gimbiyar mu ? " duban shi tayi tace " kaje kuyi magana da Prince " murmushi yayi yace " hmmm kinsanfa halin Prince sare basanar dani zaiyiba " shiru Doctor Sera tayi sannan tasanar dashi komi sabida tasan shine Wanda Prince yayar da dashi dan ta sanar dashi babu wata matsala sosai yafurgita dajin maganar guba amma dayaji matun ciki seyaji wani irin farinciki musamman da akace yananan cikin babu abinda yafaru dashi amma yashiga tunanin tayaya tasamu guba fita yayi daga office d'in cikin zuciyar shi yace lalle kuwa gimbiya kina buqatar kulawa sosai ciro wayar shi yayi yashiga Kiran layin Ammin bugu 3 tad'aga tana d'agawa Shanwul yagaidata cikin girmamawa yace
" Allah yaqara miki lafiya dama Gimbiya ce babu lafiya muna asibiti ayanzu haka " cikin tashin hankali Ammin tace " lafiya Shanwul badai Saraki ne yayi mata wani abu ba bayan ciwon shi yatashi ?" murmushi Shanwul yasaki Mai sauti yace " a a ranki yadad'e hasalima tun zuwan gimbiya cikin gidan Prince ciwon shi yarage tashi sosai yanzu de doctor tace am gimbiya tana d'auke da ciki am ma ana munkusa samun baby "
Wani irin farinciki Ammin taji wanda takasa banbance kalarshi da yanayin sa cikin yanayin muryar tsananin farinciki tace " yau d'in nan zan shirya tahowa USA Sabida Gimbiya tana buqatar kulawar uwa Shanwul wannan babban albishir dakayimin kanada babbar tukuyci dan haka nabaka dama kafad'i duk abinda kake so cikin fad'in duniyar nan nukuma zanyi makashi kayi tunanin shi kafin zuwana "
Tana gama wayar tadubi aunty Bahijjat dake gefanta cikin farinciki tasanar da ita wani irin ihun farinciki Aunty Bahijjat tasaki dede lokacin Zaffar yashigo ganin shi yasa Aunty Bahijjat fita cikin sauri part d'in mama tanufa cikin farinciki
Tofa wannan irin murna haka gaskiya Iftahal tawani 'bangaran FURUCIN!!! ki Al'kairi ne
Semun had'u zuwa dare danjin yadda wannan masarautar zata kasance shin ko Maher zai yarda yasanar wa Ammin cewa cikin nashine ko itama zai cemata banashi bane
ALLAH YASADAMU ZUWA DARE 8:30 pm Nagode
Comments please
No comments