Breaking News

FURUCI 23-24

Cikin matu'kar razana Iftahal tadubi Doctor Sera tace " doctor wai dagaske cikine dani ? " sake tabbatar mata doctor tayi sosai hankalin Iftahal yatashi d'an dedeta natsuwar ta tayi sannan tace 

" Am doctor kibani allurar bacci idan naje gida zanyima Prince sabida bayasamun bacci sosai

tambayoyi doctor tashiga yimata sosai sannan tabata cikin mutuwar jiki Iftahal tafito Koda tafito babu ko alamar Maher agurin sosai hankalin ta yasake tashi tunanin mafita tashigayi amma tarasa wasu irin hawaye masu zafi taji suna sakkowa daga cikin idanunta tsayin lokaci tarasa abinyi isowar wata mota tasa Iftahal d'an ja baya cikin sauri Shanwul yafito yanufo inda take ganin tana zubda hawaye yasa Shanwul saurin cewa " gimbiya lfy ? " Saurin share jawayen nata tayi sannan tace " lfy Lau kaina yakeyin ciwo " jinjina Kai yayi badan ya gamsuba cikin girmamawa yace " Prince ne yace nazo nad'aukeki amma nayi mamakin haka sabida naga shima gida yayi " d'an murmushin ya'ke Iftahal tayi tace " kajika sekace bakasan halin Prince ba dubani akatsaya yi shine yace shi bazai tsayaba " jinjina Kai Shanwul yayi kafin yace wani abu Iftahal tanufi mota dan batason sakeyin wata magana cikin sauri Shanwul yabu'de mata motar tashiga a cikin motar Iftahal tahad'a wannan allurar cikin sirinji bayan tagama tadubi Shanwul tace 


" Doctor ya iso kuwa ? " Cikin sauri yace tun bayan fitar ku babu jimawa jin haka yasa Iftahal saurin cewa dan Allah kayi sauri ka kaini gida " jin haka yasa Shanwul sake taka mota suna isa tafito cikin sauri tanufi ciki tana shiga tahangi doctor yana neman jijiya zeyimai allurar cikin sauri ta'karasa fige allurar tayi saurin juyowa doctor yayi shikuma Maher yami'ke wani irin kallo yashiga yimata saurin dedeta kanta tayi tace 


" Haba Prince kasanfa nace maka daga yanzu nice wadda zandinga yima allura tunda kasan abunda nike karanta kenan amma shine kaqi jirana ? " 


Rai 'bace Maher yace " bashi allurar nan tun kafin ranki ya'baci " ganin yadda yahad'e fuska yasa Iftahal miqa mishi tajuya tabar gurin tana shiga bedroom tasauke ajiyr zuciya had'ida fad'in nagode ma Allah Prince yau sede kasha bacci kawai doctor in sha Allah muguwar allurar ka tadena shiga cikin jikin Prince fiddo da allurar tayi tana dubawa alokacin da ta amsa kasancewar hijab ne jikinta yasa tayi saurin canza allurar data baccin data amso a asibiti 


Zama tayi bakin bed tashiga tunanin yadda zatayi wajan fahimtar da Maher kuka tasaki Mai tsuma zuciya se ayanzu tayi nadamar rashin sanar da Maher batun fyad'en a parlour kuwa sosai doctor hankalin shi yatashi yayi yazon Iftahal tagane komine amma dayaji abinda tace se yad'an samu natsuwa Yana amsar allurar yayi saurin yima Maher sabida Kar akuma samun wata matsalar ana gama allurar Maher yami'ke yanufi bedroom d'in Iftahal yana shiga tayi saurin mi'kewa cikin zafin rai da dakakkiyar murya yace 


" Ke yazama dole kisanar dani uban wannan cikin naki idan kuma kikaqi to wallahi zanyimiki hukunci mafi muni a rayuwar ki sekinyi nadamar sanina ke bama nadamar saninaba har nadamar zuwanki duniya sekinyi " wani irin kuka Iftahal tasaki ta durqushe saman gyuwoyin ta a gabanshi 


Tofa danjin mak Iftahal zatace se Allah yahad'a mu a page nagaba gobe in sha Allah kuyi ha'kuri da wannan 


Comments please yawan comments yawan typing

No comments