Breaking News

FURUCI 19-20

Wani irin yawu Mai kauri da d'aci Iftahal tahad'iye cikin darqewar murya tace " Allahumma rahamataka arju'u falatakilni ilanafsi d'arfatan aynun wa'aslihu  shi'ani kullahu la'ilaha illa  anta " kamar haka tacigaba dayin addu'o'i neman tsari da neman kariya daga dukkan abin cutarwa yana isowa gareta yasha'kure wuyan ta yajefata saman bed yasake nufarta gadan gadan cigaba tayi dayin addu'o'i

yanasake nufota tatofa mishi wata irin 'kara yasaki yana fad'in " kin kasheni lalle kam kijira dawowata idan nawarke anan gaba nasha  alwashin sena kasheki idan nadawo banza kawai " daga haka yafad'o saman bed d'in kamar matacce cigaba tayi dayin addu'o'i tana tofa mishi kamar 20 minutes yatashi zaune duban ta yayi sosai yanayimata wani irin kallo babu zato taji yajawota jikin shi manna mata kiss yayi yace " My wife nagodema Allah dabaki mutuba naje kawo ruwa nasamiki kitashi sekuma bangankiba dan Allah karki sake tafiya kibar ni " jin wannan sunan da maganganun shi yasa Iftahal tagane wannan ba Maher bane Saraki ne sauke ajiyar zuciya tayi tace 


" Yauwa Saraki dan Allah kaceci rayuwa ta kasa Maher yasan cewa yarabani da budurci na da Kai da Maher duk abu 1 ne dan Allah Saraki kacece ni inajin tsoro kar Maher yazargeni Kar yayi tunanin wani ne nakaima kaina Kum....... " Wata irin tsawa Saraki yasakar mata cikin fushi yace " My wife banason  kisakeyimin maganar wani ni bansan wani Maher ba kisani ni duniya ta daban shima duniyar shi daban babu wanda nasani cikin duniya ta se ke My wife karki sakeyimin maganar wani Maher kenan ma akwai wani Wanda kike so Kuma kike ma'amala dashi ko my wife kisani wallahi zan iya yin kisa akan ki sabida Ina tsananin son ki Kuma inada matu'kar kishi  " sake jawota yayi jikin shi ya sassau ta murya  yace " dan Allah My Wife kisoni kamar yadda nike sonki " 


Tureshi daga jikin ta Iftahal tayi cikin kuka tace " dakai da Maher duka abu d'aya ne Saraki maqiya ne kawai suka raba 'kwa'kwalwar ku gida biyu  shiyasa babu wanda yasan wani cikin ku babu wanda yasan mai d'aya yakeyi Saraki amma kass shi Maher yafika zama zahiri dan shi kowa yasani Kai kuwa ni kad'ai nasanka nafison Maher yasan cewa shine yayi min fayd'ey jiya dan Allah Saraki kasanar dashi " ta'karashe fad'ar hakan cikin kuka sosai Saraki yafusata yace " wato akan wani kike zubdamin hawayenki lalle kowaye wannan yacancanta nayime hukunci Mai tsanani da inada dama dana tarwatsa tashi 'kwa'kwalwar nahuta My Wife kirabu da wancan Maher d'in zan baki farinciki Kuma zan baki rayuwa mai cikeda farinciki My Wife dan Allah kimanta dashi " 


Cikin damuwa Iftahal tace  " tayaya zaka iya bani duk abinda nike buqata Saraki kaida bakasan kankaba bakuma kasan iyayen kaba sannan bakasan dalilin zuwan ka USA ba bakuma kasan tayaya ka aure niba kaga kuwa shi Maher yasan duka wannan kaga kenan shine zahiri kuma shine yafi cancanta dayasan ya amshi budurci na " dan Allah kasanar dashi " 


Babu zato kawai seganin shi tayi yana kuka cikin kuka yace " gaskiya ne duk bansan wannan ba My Wife kafin zuwanki banaganin kowa cikin wannan gidan seni 1 amma segaki alokacin inajina kamar yaro 'karami bana sanin jiya ko yau bansan Yaya ma rayuwar takeba bana iya banbance komi ko sunana bansaniba seda kikazo Kika bani suna bansan cewa ni bayaro bane se ajiya kikasa nasan cewa ni babba ne dan Allah My Wife kisanar dani komi amma kimanta da Maher nafishi sonki " 


Sosai jikin Iftahal yayi sanyi cikin damuwa tace to naji amma Kai tayaya zandinga ganinka aduk lokacin danike son hakan se zuwon Maher yatashi sannan Kai 'kwa'kwalwar ka take cigaba dayin ayki  kasanar dani yadda zandinga ganinka duk lokacin danaso amma batare da tashin ciwon Maher ba  " shiru Saraki yayi kamar Mai nazari kafin yayi magana wani haske yashigo cikin bedroom d'in cikin sauri Saraki yayi baya itama Iftahal haka addu'a Iftahal tashigayi kafin wani lokaci wannan hasken yarikid'e yakoma mutun dattijo dubansu yayi yayi murmushi sannan yace 


" _barka da 'kokarin Iftahal gaskiya najinjina miki nine wanda nasanar da Shanwul duk abinda yake faruwa akan Maher yanzuma zansanar dake wasu abubuwan amma kafin Nan kice Saraki yayi bacci cikin zafin rai Saraki yace " babu baccin dazanyi wato nayi bacci kasamu damar cutar da ita ko to wallahi baka isaba idan kaga kacutar da ita to sede idan kasheni kayi " murmushi tsohon yayi yace to ay kokanaso ko bakaso sekayi wannan baccin daga haka yahura mishi iska kafin wani lokaci tuni Saraki yabaje sosai Iftahal taji zuciyar ta tadake duban wannan Tsohon tayi shima yadubeta yace 


" _Yarinya inamai sake sanar dake daki jajurce sosai sabida akwai 'kalubale dayawa akan zamanki da Maher sannan dole zakisamu rud'ani akan Maher dole zakiga kamar kinarayuwa  da mutun 2 ne bayan Kuma 1 ne sekinyi ha'kuri  kimaida maher kamar su 2 ne kamar yadda Kike kiran wannan Saraki to kibarshi ahaka Kuma kiyi rayuwa dashi mai kyau sabida anan gaba idan 'kwa'kwalwar shi takoma tahad'e zai iya tuna yadda kikayi rayuwa dashi a wannan lokacin duk wani abu dakike shakkar shi ko kike ganin baki'iya sanar dashi to duk zesani idan 'kwa'kwalwar shi takoma tahad'e amma ayanzu dole ki daukesu tamkar daban daban kiyi rayuwa da shi akowane yanayi yake  aduk lokacin dakike so yajuya kamar yadda kike so to zan baki wata addu'a dakinyita danufin Maher kike so yajuya ko Saraki shi kenan zai juya amma daga lokacin da yasamu lafiya shikenan ni nabarki lafiya idan natafi kita'bashi zai tashi amma Saraki ba Maher ba Maher Yana bu'katar hutu sosai sannan kiyi duk yadda zakiyi kihana doctor yimai wannan allurar dazeyi idan yadawo Kuma wannan karon bada Sarki Zaid zezoba sabida shi zashi Nigeria wajan iyayen ki_


Daga haka yabata addu'o'i sosai sannan yatafi sosai Iftahal take jinjina wannan lamarin tayaya zatadinga rayuwa da mutu 1 amatsayin 2 sosai lamarin yake bata mamaki had'ida matu'kar d'aure Kai sannan tayaya zata iya hana doctor yin wannan allurar ? tsayin lokaci tanayin wannan tunanin sannan tajuya tadubi Saraki dake kwance kamar maiyin bacci cikin jin d'adi cikin rawar hannu tata'bashi kamar wanda aka furgita yatashi afurgice saurin jawota jikinshi yayi yana dube dubai zuwa can yasauke ajiyar yace 


" My Wife babu abinda yayi miki ko ? " Murmushin 'karfin hali tayi tace " babu abinda yayi min kwantar da hankalin ka " sake rungumai ta yayi cikin sanyin murya yace " mu kwanta ko My Wife am dama dama dama " kallon shi tayi cikin mamaki tace " dama Mai sanar dani mana " sake kallon ta yayi yace " dama inaso musakeyin wannan abun ne najiya  " zaro ido Iftahal tayi sabida sosai tafurgita dan kam bata manta irin azabar datashaba 'kokarin kwace jikin ta daga nashi tashigayi amma Ina yamatseta sosai cikin raunin murya tace " haba Saraki dan Allah kabarni banfa warke daga jinyar daka sakaniba Kuma banaso Maher yagane abinda yafaru dani sabida banida amsar bashi kaga kenan zansamu matsala 


Afusace yaturata tafad'a saman bed d'in yabita cikin hassala yace " banace karki sakeyimin maganar wani Maher ba nine mijinki nahar abada  Allah idan Kika sake yimin maganar wancan sena tarwatsa tashi 'kwa'kwalwar nahuta daga haka yake bakinshi cikin nata yafara kissing d'inta kuka Iftahal tafarayi sabida yadda taji  jikinshi yafarayin rawa hannun shi yad'aura saman breast d'in ta jin shasshekar kukanta yasa Saraki dakatawa cikin muryar lallashi yace 


" Haba my wife meye Kuma nayin Kuma tonaji nabarki shikenan amma gobe zakibani ? Saurin d'aga mishi Kai tayi sake sumbatar lips d'inta yayi sannan yaja musu blanket sosai yarungumai ta cikin 'kirjinshi cikin sanyin murya yace 


" My wife ina tsananin sonki amma zuciyata tanayin zafi idan naji kin ambaci wancan Maher d'in nine mijin ki bashiba dan haka daga yau babuke babu shi kinji my Wife cikin shagwa'ba tace " Ina ay dama ni Babu ruwana dashi Kai ne Mai sakarmin fuska Kuma Kai ne mai furtamin kalmar soyayya nima Ina matu'kar son ka Saraki na " sake matseta yayi cikin jikinshi sabida dad'i ahaka har bacci yayi gaba dasu sosai Iftahal tayi bacci Mai dad'i cikin wannan daran Kiran sallar asalatu yafarkar da Iftahal kallon fuskar Saraki tayi sefaman Shan bacci yakeyi sosai takejin dad'in kallon shi murmushi tasaki tace " Allah sarki Saraki na yanzu zakabar ni nida wannan uban miskilancin " daga haka tayi addu'o'i da wannan tsohon yace tayi 


Babu jimawa Maher yabud'e idonshi ahankali suka sauka kan kyakkyawar fuskar Iftahal saurin janye jikinshi yayi daga nata tamke fuska yayi sosai yace " waye yasaki hawamin saman bed ? " Murmushi Iftahal tasaki tace katambayi kanka Mana Prince Kai da kanka kajawoni Kuma bakaga yadda karungumeni ba ? " tsaki yaja afusace yace " banason shashancin daga yau Kar in sake ganin hakan " cikin d'an damuwa Iftahal tace " to amma naga umarnin Ammin ne hakan tace karmu raba gurin kwanciya " banza Maher yayi da ita yasauka daga bed d'in seda yake bakin 'kofar toilet yace " hakane umarnin Ammin ne amma Kinga wannan cushion d'in to anan zakidinga kwanciya " har yad'aga qafarshi zai shiga sekuma yatsaya yace " waye ya kwashe aman dake gurin nan ? " saurin duban gurin tayi tabbas Babu komi agurin Kuma iya saninta bata kwashe shi ba sosai Iftahal  tayi matu'kar razana amma cikin in ina tace nice " tsaki Maher yaja yace " Wai banace babu ruwanki cikin lalurataba Kinga Iftiih!!!!! banaso kina saka kanki cikin wannan lamarin ki kiyaye tashi kibar bedroom d'in nan " 


Saurin sauka Iftahal tayi tafita sabida tsananin tsoro dan Kam tafurgita sosai tana sakkowa tanufi bedroom d'in ta abinda tagani yasata saurin jabawa gaba d'aya ancanza tsarin kayan bedroom d'in aguje tafito tana kwalama Maher Kira cikin sauri yafito kogama alwala baiyiba kasa magana tayi senuna mai hanyar bedroom datayi Kai tsaye yanufi bedroom yashiga dube dube yashigayi amma baiga komiba Kuma Shirin kayan yakoma yadda yake ahankali Iftahal tale'ka amma setaga yadda Shirin yake tunda haka yake wani irin kallo Maher yayi mata yaja tsaki yabar bedroom d'in 


Comment please

No comments