Breaking News

DUDUWA 34

~34~

Kulu ta jima a kwance a ƙasa bata farfaɗo ba har kusan magariba shima sai da Na dudu ya ciko buta biyu da ruwa yazo kanta ya dinga kwara mata yana"inna ki tashi inna,da ƙyar kulu ta iya rarrafowa ɗakin ta a tsakar ɗakin ta baje tana sallati ga yunwa na damunta ta laluba inda ta ɓoye ƙwalon kankanar da mai gari ya bata ta bawa na dudu taji wayam babu kankana a wajan sai hawaye wani na bin wani kulu ta furta""


"na shiga uku ba zabbi babu kankana ga dukan dana sha,shiru tayi tana nazarin waya ma doke ta kamar wuce aka tsikara ta miƙe tsaye jikin ta har karkarwa yake ta shiga leƙe tsakar gidan ta tagarta tana kuka iya ciki.


wasu ƙafafuwa kulu ta hango dogaye suna doso tagar da take leƙawa kan kace kwabo kulu tayi ƙarƙashin gado tana"


"Gwaggo ibrahimu yawale tsahare da sahura ku taimake ni........kukan ciki ya fito fili gaban kulu sai faɗuwa yake jikin ta na ƙara karkarwa da dana sani fal aranta na zama gida ɗaya da Na...kulu bata ƙarasa faɗa ba ta toshe bakin ta karma ta ambaci sunan Na dudu a kuma ranƙwale ta,kuka ne yazama abin cin kulu da ruwan shan ta ta haɗa majina da hawaye sai kiran sunan wanda tasani take a zuciyar ta har aka fara kiran sallah,ai wani sabon kuka ne ya kuma ƙwace mata tunowa da da fashin sallar da takeyi ga fitsari daya addabi mararta da ƙishirwa da yunwa kamar zasu karta ga duhu ya fara kunno kai tashin hankalin da kulu tashiga ba zai musaltu ba a wannan rana a zaune ta kwana data rufe ido ƙafafuwan data hango suke bayyanar mata a idonta tayi kuka ta gaji ta huta ta kuma ɓarkewa da wani sai Addu'a kulu ke yi safiya tayi.

    A nan ƙarƙashin gadon kulu ta saki fitsari ta janyo ƴar butar ta datake ajiyewa a ƙasan gado Allah yasa da ruwa rabin butar a ciki nan da nan kulu ta kafa kai ta kwankwaɗe shi tas ta haɗe da fashewa da wani sabon kukan jin babu inda ruwan ya toshe mata.




……………………………………






        Cikin kwana uku rak idan kayi tozali da ƴarchakare sai ka tausaya mata gaba ɗaya ta fita hayyacin ta kullum malam jibo sai yasa ƴar chakare a gaba ta wanke masa kaya ta wanke gidan da wanke wanke kai har bangon gidan sai ƴarchakare ta wanke shi tas da bayi duk da turɓaya ce a ƙasan ga tuƙa tuwon safe da rana da na dare ko koko malam jibo bai yadda ƴarchakare ta sha ba daga tuwo sai tuwo kuma da kanta zai sa ta ta sirfa dawar ya kai niƙa idan wahala tai wahala sai dai kaga ƴar chakare na kuka tana roƙon malam jibo bazata sake ba zata zauna lafiya a gidan liman idan ta koma,malam jibo yayi murmushi ya ce ai hutu taje yi gidan aure ba ibada ba tunda ta dawo gidan su to tayi hutun mai dalili.


haka ta ɓangaran gyatumar ƴarchakare ta zo bikon malam jibo yafi sau goma sakamakon saka ta abakin da akayi a ƙauyensu ko ina tayi sai ace ta kashe auran ƴarta ta kashe nata wasu ma har ƙarawa suke da ai satar hatsi ta saka ƴar a gidan miji suke kaiwa kasuwa maganganu marasa daɗin ji malam jibo yaƙi saurararta gidan sa ma gaba ɗaya ya hanata shiga bare tayi tozali da ƴar tilon ƴarta shalele ƴar chakaren malam liman.









_*By*_

_*Maman Dr*_

No comments