Breaking News

DUDUWA 33

_~33~

    "Kulu ce rungume da Na dudu a jikinta jiyo dawowar su me unguwa ya tabbatar mata su mai gari sun ɗauki hanyar zuwa burni kulu tasa hannu ta yafito Na dudu daga jikin ta ta tureshi haɗe da faɗin""""

        "Kai matsa chan karka shafan majina ji shi da ƙaton kansa kamar na gyatumarsa ɗan bantan uba daga ni sai kai a gidan yau na niƙaka yanda rai na yake so maza ka wuce ɗakin ka kabani waje ka tsare ni da na mujiyoyin idanuka,sim sim na dudu ya faɗa ɗakinsa kulu ta tattara kayan da mai gari ya bata ta sawa na dudu da ƙwallon kankanar duk ta shige ɗakinta dasu ta samu maɓuya ta ɓoye,sake fitowa tayi ta nufi ɗakin na dudu kai tsaye ta faɗa cikin ɗakin.


      Kulu na shaga ɗakin ta iske na dudu zaune akan katifar sa sai wasa yake da kachau kachau a hannunsa fusgewa kulu tayi ta ranƙwashi kan ta ce"


Waya saya maka wannan har ka samu damar yin wasa da shi sai kace akan ka mai gari ya gama haihuwa komai a rakito a yaɓa maka gaka ɗan so,tashi ka ibo min sauran ko na zane ma jiki yanzu yanzun nan ja'iri me fala falan kunnuwa.



Na dudu ya kwaɓe baki zai yi kuka ya ce"


"Ni ba baba na ne ya saya min ba ki bani abuna nayi wasa.



na ƙi na baka lalai ma yaron nan har ka iya lanƙwasa magana ka karkace ka tsula ƙarya idan ba gyatumi bane ya saya maka to waye ya baka kai da ko ƙwar gida baka zuwa tsabar rashin basira da jakanta.


ban sani ba.


na dudu ya furta kai tsaye ido kulu ta zaro waje haɗe da yafitar takalmin ta ta shiga rafkawa na dudu tana zaginsa yana kuka yana ya dena bazai ƙara ba kulu ta mammake shi dan kanta ta gaji ta ajiye takalmin ta kwashe duk wasu kayan da mai gari ya sayawa na dudu ta bar masa kala ɗaya tal ta kwashe kuɗin cikin fulon shima tayi ɗakin ta dasu ta bar na dudu na kuka har bacci ya kwashe shi akan katifar tasa.


Har kusan la'asar kulu bata ɗora sanwar rana ba, bata da kuma niyar ɗorawa ga yunwa ta adabi na dudu ya rasa inda zai yi ya rarrafo ƙofar ɗakin kulu daya tashi daga bacci ya ce""


"Inna yunwa nake ji ki bani abinci na ci.


ban dafa ba ko ni zaka kwaɗa ka cinye tunda yunwa kake ji baiwar kace ni na dafa kaci sai sanda naga damar yi yunwar ta kassaraka nace ɗan bantan uba ka wai komi abinci abinci sai kace ciki ka kawo duniyar.


kuka na dudu yasaka ya ɗauki hanyar waje da gudu kulu miƙe ta fito ta janyoshi ɗakin sa ta zanneshi da bulala ciki da bai ta ce kuma ce masa sai yayi baccin dole har guri ta samu ta zauna tana jiran na dudu yayi bacci a hankali kuwa bawan Allah baccin ya ɗaukeshi kulu ta miƙe ta koma nata ɗakin ta zari mayafi ta fuce daga cikin gidan bayan ta ƙule gidan ta waje.


   ko da ta fito bata iske kowa ba a mazaunin jama'a tayi bakin kasuwa kanta tsaye siyayya kam babu wace batayi ba na kayan ƙwalama har cefane tayo da zabbi manya manya guda biyu yankakku da kayan miya jingim ta dowo gida ta shiga hada hadar ɗora girka farfesun zabbi da shinkafa fara,shinkafa kulu ta dafa ta shirya farfesun da ta ɗanɗanashi yafi a ƙirga ta haɗa komai da komai ta kai ɗaki ta ajiye ta kwaɓe kayan jikinta tashiga bayi dan yin wanka. 

      Koda kulun ka ta fito daga wanka ta koma ɗakin ta mai ta shafa ta zaro riga tishet da zani da ɗankwali ta saka ta je madafa ta ɗauko rubar cin abinci ta nemi waje ta bararraje yawunta har tsinkewa yake zata kwashi farfesu ko ta kan na dudu bata bi ba ta ɗora hannu akan tukunyar farfesun har wani lumshe ido take ta buɗe da ƙarfin ta,cikin saure kulu ta saki murfin tukunyar ta sake buɗe tukunyar shinkafa ita ma abinda ta gani a ta farfesun haka ta sake gani da gudu ta miƙe ta fito daga ɗakin nata ta faɗa ɗakin Na dudu tana masifa nan ma turus ta kuma yi ganin Na dudu na bacci kashirɓan bata yadda da baccin nasa ba ta nufoshi gadan gadan ta shiga shinshina bakinsa ta dawo hannuwansa nan ma bai yi mata ba ta dinga dube dube a ɗakin ko ina ta wargaza shi ko zataga abinda take nema samma ko ƙassa bata ga komai ba ta daddage ta ɗumawa Na dudu dundu a baya dayayi firgita ya farka yana kuka tsawa kulu ta daka masa tana""


""Ina ka kai mun abinci na da farfesu na?



shiru na dudu yayi mata sai ma ƙara ƙarfin kukan sa da yayi,haushi ya kama kulu ta fusata ta fito daga ɗakin tayi madafar abinci,muciya ta saɓo a hannu ta dawo ɗakin ta ɗaga muciyar sama zata sauke wa Na dudu aka,aka sauke mata wani irin duka a baya ta baje a wajan tana ihu.


  Banda ihun da kulu ke yi har da fitsarin wahala ta soma ganin komai na ɗakin biyu biyu ta fara jan jiki a haka zata gudu,ko taku ɗaya bata kai ga yi ba aka kuma rotsa mata dukan a ƙafafuwanta ta darshe tana wani irin gurnani.






***** 



  "Dokoki baban ƴarchakare ya shinfiɗa mata da sharaɗi me razanarwa idan yaga ƙeyar ta a waje ba dukka ba yankata zai yi kowa ma ya huta tunda shi ya haifeta ba wani ba,tsoro da firgici ya shiga zuciyar ƴarchakare banda haƙuri da koke koke babu abinda take ga shi me ƙwatar ta bata gidan,malam jibo ya fito ya kule gidan ƴarchakare na ciki tana kukan dana sani malam Jibo yayi gidan liman zuciyarsa fal da wasi wasi,yana isa gidan ya yayi sallama liman ya fito suka zauna a mashinfiɗi liman ya kwashe duk abinda ƴarchakare ke aikatawa a gidansa ya zayyanewa malam jibo ya jimanta abun sosai ya ƙara da bawa liman haƙuri da ɗaukan mataki akan hakan a ƙarshe ya nemi liman ya dubi Allah ya mai da ƴarchakare ɗakin ta na aure,liman yayi shiru yana tunani maganar chan dai ya amsa zai mai da ita amma abarta ta koyi hankali tukun kafin ta dawo gidansa,malam jibo yayi godiya yace shima hakan yayi masa dan zai saita a hanya dama gyatumar ta ke taɓarata yanzu kuwa bata gidan,liman ya ce kayya ashe daga wajan tsohuwa aka samu matsalar nan malam jibo ya shiga labartawa liman hali irin na babar ƴarchakare da son abin duniya har kawo salamar ta da yayi zuwa gidansu liman ya ce ba'ayi haka ba shima malam jibo yayi haƙuri ya dawo da mai ɗakinsa da ƙyar malam jibo ya amsa da to sukayi sallama kowa yayi nashi waje.



*Ina godiya masoya kuyi haƙuri da jina shiru kwana biyu na shiga wata safgar ne amma kuna rai na wallahi🥰*










_*By*_

_*Maman Dr*_

No comments