Breaking News

DUDUWA 32

~32~

         Yau ma kamar kullum dije ta kammala girkin ta na rana kenan malam liman ya shigo gidan da salama a bakinsa,amsawa dije tayi riƙe da kwanan abincin liman ta ƙara da""

"Barka da zuwa malam ga abincin ka ina zan ajiye maka dama sai tunani nake na rasa inda zan ajiye.


a hankali liman ya ƙaraso daf da dije ya furt"""


ƴar chakare na nan?


Aa malam ta fita,dije ta amsa ware murya liman yayi ya ce"


maza kai min ɗakin ki na ci dije ki hanzarta dan Allah kar ta shigo tayi mun haramiya.



Haram wallahi ba dai a ɗakina ba malam sai dai na kai maka ɗakin amaryarka tun da ai girkin tane ba nawa ba dama na zuba maka ne dan nasan wataƙila ka shigo da yunwa nasan ba dafawa zatayi ta baka ba.



hmmm dije wai yaushe kika koma haka idan nace kiyi ki ƙi yi,in na ce karki yi nan ma sai kinyi anya dije Aljannar danake miki fatan ki shiga anya zaki shiga kuwa.



insha Allahu kuwa malama ina cikin ta tsundum daga maganar gaskiya sai kayi mini mugun fata.


babu wani mugun fata aljannar mace ai tana tafin ƙafar mijinta idan kinbi Allah da Manzon Allah (S'A'W),kinyi wa mijinki biyayya da kyautata masa amma sam bakya mun abinda nake so dije.



ni ɗin malam.


ƙwarai kuwa gashi na ce ki kai mun abinci ɗaka kina tsaya kina min gardama har da wata magana daban kin ko san yunwar dana ibo a waje dije ni bani abinci na,na kai inda naga dama kuma wallahi ki fita idona na rufe dije akan ƙin jin magana ta hmmm,liman ya wafci kwanan abincin sa yayi ɗakin dije da sauri yana gyara labule diji ta bishi da kallo tana.



"Aa fa malam a dinga adalci ana sauƙe haƙƙin da Allah ya ɗora maka.


ki jira ni naga ma ci sai ki kora bayanin da duk zakiyi kuma wallahi ƴarchakare ta shigo gidan nan kika ce ina ɗaka Allah sai nayi miki Allah ya isa ban yafe ba ai rabona ne bana wani ba tunda baki jin maganar mijinki.



ahayye nanaye sarki goma zamani goma ni dije yau amarsun taka kake ɓoyewa malam lalai na yadda mai haƙuri shi ke dafa dutsu har yasha romansa bari dai muga ƙarshen wasan naku.......


"Salamu Alaikum.


    ƴar chakare ta shigo afujajan da ita,dije dake tsaye a tsakar gida ta amsa da"


Wa'alaikumussalam.


dije ta juya zata shige ɗaka ƴar chakare tayi sauri ta sha gaban dije riƙe da ƙugunta ta ce.


"Malama ina abinci na wai ni duk sanda kika dafa abu a gidan nan bani da rabo akansa sai dai ke da ƴaƴanki ku cinye naga nima a gidan mijina nake bake kaɗai ce matarsa ba abani rabona ko rai ya ɓaci yasin.


au Allah to tunda ke matar gidan ce waya hanaki shiga rumbu ki ibo hatsin ki dafa ko akwai wanda kika haifa a gidan bare ya dafa ya zuba miki kici.


ni kikayiwa gorin haihuwa to bari liman ɗin ya dawo na rantse me rabani dake a gidan nan sai Allah sai na ƙulla miki sharrin da gobe idan akace ki faɗa ina faɗa bazaki kuma ba kai gidan ma yasin zaki bari bari liman ya yadawo kiga............."to uwar sharri gani a ɗaka na jima da dawowa wato sharri kike ƙullawa dije baiwar Allah ki kwanta a ƙasa kamar gaske munafukar Allah,yau dai Allah ya toni asirinki muguwa me mugun nufi abu kamar a kife sai shigen ƙarya da ƙulla husuma to naji duk maganganunku dama a nan ɗina kike,liman ya nuna yuwansa da yatsa ya ɗora"ki tattara inaki inaki ki wuce gidan gyatuminki naga alama shigo shigo ba zurfi akayi mun ni kuma na rufta gaba ɗaya ba buncike baki gaji tarbiya da mutunci ba kije na sauwaƙe miki igiya ɗaya tal ƴar bantan uba kawai,ƴar chakare najin an sallame ta ta zube a ƙasa tana ihu da burgima liman ya saketa,dije ta dubi liman fuskarta kamar zatayi kuka ta ce.



"haba malam dukka dukka yaushe kayi auran kuma ka duba yarinta irin ta ƴarchakare idan ka salameta ka maida ita ƙaramar bazawara dan Allah dan Annabi malam ka maida ta tunda ka gane halinta sai ka gyara tsakaninmu mu zauna lafiya ka yi haƙuri malam.



dije!!



na'am malam.



yasin sai ƴarchakare ta wuce gidan su babu wani kome dazanyi da mara tarbiya ta koma chan gidan akoya mata tarbiya da zaman gidan miji ba gantafalfala ba.



kayi haƙuri malama duk zata gyara kar abin ya kai ga haka dan Allah,ki bashi haƙuri mana kin zauna kina kuka.


babu haƙurin da zanyi ta tashi ta kama hanya kawai ni na gama magana ungo ƴar aljanna dije dije ta malama liman dan Allah ki yafe min abinda na riƙayi miki dije a rashin sani na aikata ban san haka shaƙiyar ƴarnan take da munafunci ba,liman ya ƙare batun da duban inda ƴar chakare ke malale a ƙasa tana rusa kuka da bawa liman haƙuri har liman ya fita daga gidan ƴarchakare na ihu dije sai haƙuri take bata tana ta kwantar da hankalinta zata bawa liman ɗin haƙuri har dare liman bai dawo ba ƴarchakare ta ibi abinda zata iba tayi gidan su tana kuka.




       Ko da ƴarchakare ta koma gida ta sanar da abinda malam liman ya faɗa,babanta yasata a ɗaki ya jibgita san ransa ha ɗora da salamar gyatumar ƴarchakare acewarsa uwar ke lalata ƴar duk abinda tayi ita ta janyo dan haka sai ita ma ta bar masa gida a ranar ƴar chakare kwana tayi tana kuka ga bugun datasha ga raraka gyatumarta da babanta yayi.






*******





  Tun daga wannan rana kulu ta sauya halayyar ta, ta shiga nan nan da na dudu kan ya ce tayi masa wanka da wanki kai har goyashi take a baya tana masa waƙa da rawa wai ɗanta mai gari yaji daɗin haka ya shiga yiwa kulu bajinta da kuɗi da kaya da kayan maƙulashe dan duk abinda na dudu yace yana so to fa ita ma kulu zata furta shi take so haka mai gari zai fidda masu gidan rana yayi musu dukka su biyun amma har yanzu na dudu yaƙi sakin jiki da kulu ko wajanta baya zuwa sai idan ta kira shi.

    Ana haka ɗan uwan mai gari ya aiko da katin ɗaurin auransa zuwa burni kuma mai gari ne zai wakilce shi akan komai tafiya ta taso wa mai gari ya shiga labartawa magatakarda da sauran masu zama a fadda har ya bar komai a hanun magatakarda da me unguwa da liman kasancewar da mudi za'ayi tafiyar suka amshi amanar kulawa da ragamar garin KANWA gaba ɗayan ta,ko da mai gari yajewa da kulu maganar tafiyar da farin ciki ta amince har da taka rawa acewar ta mai gari zai taka burni ita ma watan wata rana zata je idan Allah ya nufa biyayya da ladabi kamar kulu zata haɗiye mai gari da na dudu har ranar tafiya ta zo mai gari ya gama shirya komai ya fito ya iske kulu dake rarrashin na dudu yana kuka ya ce.


"To Kulu ga wannan kayan na Na dudu ne sai takalmi da kankanar daya ce yana so dan Allah ki bashi duk abinda yake so kafin na dawo kinga tafiyar nan zata ɗauke mu mako guda kiyi haƙuri da duk abinda zai yi dan Allah ina ƙara roƙon ki riƙeshi kamar yanda zan masa kulu kinji.


    hannu biyu kulu tasa ta amshi kayan da ƙwallon ƙatuwar kankanr ta dubi mai gari dayake dubanta ta ce""


Haba yallaɓai ai ba sai ka bani amanar na dudu ba zan riƙe shi amana har Allah ya dawo mana daku lafiya ai ɗa na kowa ne bari ni da ban taɓa haihuwa ba na ɗauki na dudu kamar ɗan da na haifa dama dakaga bana sonshi wallahi sharrin sheɗan ne da ɓacin zuciya amma komai ya chanja ranka shi daɗe.



to masha Allahu kulu sai Allah ya dawo damu kuɗin dana bari a cikin rigar fulo naki ɗaya na na dudu ɗaya sai ku saya abinda kuke so na san zai isheku har na dawo.


mun gode ranka shi daɗe Allah dai ya kai mana ku lafiya burnin nan ya dawo daku lafiya ince da mudi zaku wuce saboda sha'anin hanya.


da shi zamu mu juyo insha Allahu.


kulu ta ƙara dashe baki tana faɗin.


"gwamma kam ku tafi taran bibiyu ai yafi tafiyar kaɗai ci na dudu ayiwa baba adawo lafiya ko me zaya sayo maka a burni.



mota da jirgi me tashi.


dariya mai gari yayi ya shafa kan na dudu ya ce""ai kuwa insha Allahu zan sayo maka mota me kyau da jirgi amma ba me tashi ba kaji Na dudu na.


na dudu ya gyaɗa kai yana goge hawaye,salama mai gari yayiwa kulu da na dudu mudi ya ɗauki kayansu suka fito ƙofar gida,ƙofar gidan cike da jama'a kowa naiwa mai gari fatan alkhairi da Allah ya kiyaye hanya magatakarda da me unguwa suka rufawa mai gari baya da mudi har bakin mota suka shiga suka zauna sunaiwa magatakarda da me unguwa sallama da hannu har motar ta fara tafiya tayi nisa wa me unguwa da magatakarda suka koma ƙofar gidan mai gari aka cigaba da safga.








_*By*_

_*Maman Dr*_

No comments