Breaking News

DUDUWA 30

 _            _*🧞‍♂️NA DUDU🧞‍♂️*_

          _(cigaban Duduwa)_

~30~

    Ta inna idan tanai masa waƙa har kumburin burodi take ki ransa dashi kullum mai gari na hanyar zuwa duba na dudu da kayan arziƙi fal a ledar.

     kulu duk ta rame ta fige tsabar tasawa kanta fitina babu abinda yake cin ran kulu sama da na dudu ya tsaya mata a ƙahon zuciyarta taƙi jinin taji an kira sunan Na Dudu kullum addu'arta Allah yasa Na Dudu yabi gyatumarsa inda ta tafi,yaro kam sai hawa yake kamar buhun burodi ga lafiya kamar ƙara masa auki ake kullum girma yake yana ƙara wayo idan ka dubi fuskarsa bazaka iya tantance mai gari dashi ba sak suke kama sai dai girman jikin daya ibo na Duduwa gaɓɓansa sak nata ba maraba.




………Kwanci tashi ga mai rai ba wuya Na dudu har ya cika shekara uku a gun inna taɓara da shagwaɓa babu wace Na dudu baya yi ko harara inna bata masa sai aikin lallami da bashi duk abinda yake so har zance ya je kunan mai gari da yaso amsar shi inna ta roƙi mai gari yabarshi idan Allah yayi lokacin ta yayi sai ya koma gareshi gaba ɗaya,mai gari yaji tausayin inna ya bar maganar har inna ta fara jinyar ajali.



Allahu Akhubar daran da Na Dudu ya cikashe shekara biyar a wannan dare inna ta ce ga garinki jama'ar Kanwa sunji mutuwa bare na dudu kuka yasha shi ba kaɗan ba haka maƙota da abokanan arziki ana cika kwana bakwai na dudu ya koma hannun mai gari da zama aka bawa na dudu duk abinda inna ta mallaka a nasiharta kenan kafin ta rasu.

    




………





Ɗakin Duduwa nan mai gari ya gyarawa na dudu ya kashe masa kuɗi kam ba a magana har sabon fenti yasa akayiwa ɗakin aka sayo ledar da katifa ƙatuwa aka malale masa su a ɗakin da kayan sa cikin buhu,mai gari ne ya fito daga ɗakin riƙe da hannun Na Dudu suka nufi ɗakin kulu da sallama,har kulu ta buɗe baki zata amsa sallamar tayi ido biyu da na dudu gumtse bakin ta tayi ta ƙara haɗa rai tana duban mai gari dake shirin zama a ƙasa shima na dudu ya zauna a ƙasan kusa da mai gari kamar yanda yaga mai gari yayi kafin mai gari ya buɗe baki na dudu ya chafe da.



""Inna kululuwa ina yini.


daban yini ba zaka gani kuma a gidan uwar wa kaji ana kira na da kululuwa kai ina ma ka iya gaishe da mutane bayan an sangarta ka an taɓarɓara ka eyyi.



Ranka shi daɗe ne yace idan munzo na gaida ki kuma ke ɗin inna ta ce.



yau naga lalata tun kan ka kwan a gidan har an fara kitsa maka makirci samfir samfir,zo nan wajan,kulu ta yafito Na dudu da hannu zuwa gabanta ta ƙara haɗe rai haɗe da zaro masa ido waje tace""


 "Kar in kuma ji ka kira ni da inna,innarka na chan ƙarƙashin ƙasa an bunne ta,kulu ta daki ƙafarta a ƙasan ɗakin ta ɗora da"kuma ba sunana kululuwa ba kar ma naji ka kirani da kowane irin suna dan ni ba uwarka bace bana kuma san iskanci da lalaci kasake kayi ba dai dai ba wallahi dukan mutuwa zanyi maka na lahira sai ya fika jin dadi dan bana saurarawa kowa ya raina ni kaji ni ko.


Na dudu ya kaɗa kai yana duban kulu ido da ido,ƙara zare masa ido kulu tay ta kai ɗan yatsanta kan idonsa ta ce.


""dubi ja'iri ido ƙuru yana kallon ka ko tsoro babu sai na tsokane idanuwan kazama me ɗaya da rabi.



"Haba kulu duk wannan jawabin bai miki ba har sai kin haɗa da cin zali ko kin manta da ina wajan suk idanunki sun rufe tsabar masifa.



wato masifa nake masa daga faɗan gaskiya ko, sai na zuba ido yaro ya raina ni kana ji kan ganin abinda yake faɗa kayi zuru kana kallonsa to wallahi ba dai a gidan nan ba.


me ya faɗa miki na raini tsakani da Allah naga har gaidaki yayi.



wacce gaisuwa,gaisuwar daka kwarkwara masa tun kan ku shigo ka kitsa masa ƙarya da gaskiya to ni wallahi bazan ɗauka ba bada Hauwa kulu ba ato.



hmmmmmm.


mai gari ya faɗi yana mai girgiza kai kulu tayi ƙwafa ta ce""



gyaɗa kai da kyau maganar ciki ai ba magana bace.



kinga kulu dan Allah mubar wannan abun gaban Na dudu dama kawoshi nayi amana ki ɗaukeshi kamar ke kika haifeshi.........'"tsaya tsaya malam kamar me naji ka ce sake maimaitawa naji?



cewa nayi ki ɗaukeshi a matsayin ɗanki kamar ke kika haifeshi.



tabɗijam amma yasin kama raina min wayo mai gari ɗan kishiyar zan ɗauka amana har na rike kamar ɗan dana haifa hahahahahhahah wannan tatsuniyar gizo akwai daɗin sorara amana ai sai liman ko me unguwa naga sune aremu muje bikin.



ran mai gari ne yakai ƙololuwar baci ya rasa abinda zai furta ya miƙe daga zaunan da yake ya ɗauki Na Dudu a hannu suka fito daga ɗakin kulu sai bala'i take tana babu kashin ɗan gardin da zataci bata haifi nata ba,bazata ci na wani ba dan haka tun wuri mai gari yasan yanda zai yi da Na dudu,mai gari yana ji yasa kai yafita daga gidan da Na dudu a hannunsa.


       Ɗakin mudi mai gari ya faɗa kasancewar waje akwai jama'a ya dire Na dudu a gabansa yana kuka me ban tausayi ya rasa me ke masa daɗi a rayuwa,hanna Na dudu ya ɗaga ya fara sharewa mai gari hawayen dayake saukowa daga kumatunsa yana""



"Ranka shi daɗe ka dena kuka inna ta ce babu kyau kuka kaji.


mai gari ya rungumo Na dudu jikinsa yana.



"Na dena bazan kuma kuka ba na dudu mutuwa tayi mana yankan ƙauna ta ɗauke Duduwa ta ɗauke Inna😓😓😓😓😓😓😓😓😓😓😓😓


Kuka sosai mai gari yake Na dudu na rungume dashi har bacci ya ɗauke shi,share hawayen mai gari yayi ya ɗauki Na dudu dayaga yayi bacci suka fito fadda mai gari ya shimfiɗar da na dudu a kusa dashi ya shiga tattaunawa da mutane, ya jima a wajan ana hada hadar jama'a kafin ya koma cikin gida komawars ne  ya buƙaci abincin sa da na dudu kulu ta kwaɓe baki ta ce"


Abincin ka ko abincin na dudu?


cike da hanzari mai gari ya furta""


Na mu gaba ɗaya ni da shi nake nufi.



ban dafa dashi ba sai dai naka rabon.


to abani nawa rabon sai muci tare dashi.



tsigai tsigai kulu ta shige ɗakin girki ta ɗauko abincin mai gari ta zo gabansa ta dire, gefe guda ta koma ta tsaya mai gari ya kalle ta yace"



ki tafi mana tunda kin kawo mun abincin ko akwai wani abun ne kuma.



ko ɗaya na tsaya ne kawai dan naga zakici abincin nawa ko bazaka ci ba.



me zai hana ni ci kulu yunwa mukeji sosai da na dudu tun safe rabanmu da saka hatsi bakin salati.


Ummmm.



kulu ta furta ta zubawa na dudu ido har da harara da zare masa ido,bayan mai gari ya zuba abincin ya yi bisimillah ya ibo abincin a hannunsa ya kaiwa na dudu bakinsa kenan kulu ta saka hannu ta doke hannun mai gari abincin ya zube a ƙasa a fusace mai gari ya miƙe yayi kan kulu zai bugeta,sai kuma ya fasa ya tsaya yana maida numfarfashi tsabar ɓacin rai kulu ta kuma sa ƙafa tayi fatali da abincin tana zarewa Na dudu ido daya saka kuka tun da kuli ta buge hanun mai gari,masifa ta shiga yi"




In dai na cika sunana Hauwa kulu wlhy bazan dafa abinci wannan ɓakutun yaron yaci ba sai dai dakai dashi ɗin duk kuyi asara amma babu abinda zai saka na zuba ido ina kalo ka bashi abinci a baki kamar jariri,ai daka sake ka bugeni hmmm bazaka gane wacece kulu ba sai a lokacin wallahi sai na rama akan ɗan tayinka wai duk akan wannan abun mai gari ka tsaneni,kulu ta nuna na dudu da yatsa mai gari ya ɗaukeshi yana kuka suka kuma ficewa waje.



bakin kasuwa mai gari ya wuce da na dudu a hannu bayan ya rarrashe shi yayi shiru ya siya musu nama da guratsa me yawwa da ruwan leda suka juyo gida suka dawo duk wanda ya dubi mai gari a ranar yasan babu lafiya har bakin kasuwa ya taka da kansa abun babba ne a cewar magulmata.



bayan sun dawo ne mai gari ya shiga ɗakin na dudu anan suka zauna ya fara bawa na dudu gurasar da nama yaci sosai ya sha ruwa ragowar mai gari ya cinye haɗe da shan ruwa ya shiga lalaba na dudu har yayi bace shi kuma ya tashi yafito waje,alwala ya ɗauro ya dawo ɗakin ya shimfiɗa dadduma ya ɗauki tsawon lokaci yana sallolo da Addu'a akan abubuwan da suke faruwa har na dudu sai da yayiwa Addu'a bai idar ba kulu ta faɗo cikin ɗakin ta shiga shin shine shin shine ledar gurasar ta ɗauka ta buɗe haɗe da yin ƙwafa ta yar ta riƙe ƙugu ta tsaya tana jiran mai gari ya idar.


idar da Sallah mai gari yayi,ya shafa addu'a ya miƙe ya fara shirin kwanciya ko kallon inda kulu take bai yiba ya tafi kusa da Na dudu ya kwanta bai ɗauki muntuna da kwanciyar ba kulu ta tako dai dai kansa ta haɗa hannuwanta biyu ta tafa da ƙarfi dai dai kunan mai gari.



        ""Tasssss,kake ji mai gari ya wanke kumatun kulu da wawan mari ta hantsila gaba ta miƙe a zubure tana ihu da ya yi sanadin tashin na dudu daga baci a firgice mai gari yayi kanta yana masifa da taga da gaske yake tayi ɗakinta a guje ta zari mayafi tana kuka tana "gidan mu zan kwana sai an bimin haki na,kulu tayi waje.







******







Tun da ƴar chakare ta lura da dije ta ɗauke ta ta ajiye a gefe ta sauya zanni idan girkin ta ya zagayo sai ta kwashi ƙafafuwanta ta fuce tun safe sai bayan la'asar ta dawo lokacin dije ta gama girki abin taƙaicin ma data shigo gidan kwano zata ɗauka tayi madafa ta take kwanon da abinci ta zauna taci har yayi mata yawa daga dije tayi magana sai ta ce"kitso naje da ƙunshi malam ne yace yana son yaga nayi,dije sai tayi shiru da abu yayi abu dije ta kai ƙarar ƴar chakare wajan liman ya kuma ɗaure mata gidi ya ƙara harda yiwa dije faɗa akan tasawa yarinyar mutane ido tsabar kishi da masifa😆








_*By*_

_*Maman Dr*_

No comments