Breaking News

ZAN FASA KWAI 24

 *ZAN FASA KWA

              *NA*


*HADIZA BARA'U GIDAN IK

_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_

                *Page 24*

........Bai Kara tunawa da batun wata halitta Wai ita dungo ba asalima tun da ta tafi ya share da lamarin ta inda aka kashe kudi sosai wurin yiwa fulani bikin murnar cikar ta Sha bakwai da haihuwa akayi taro na manyan Yara ta Kuma samu kyaututtuka daga kawayen ta na karatu

Kana biyu da yin bikin yake sanar da izzatu anyi mishi alkawarin bashi kwangilar gyaran wutar lantarki wadda zai samu manyan kudin na tashin zance inda ta cika da murna don duniyar su zata Kara haskawa


Sai dai me ? Maimakon yaji Kiran daga fadar me bawa shugaban kasa shawara Kan abinda ya shafi aikin. Sai ji yayi Wai har anyi kwangilar an gama har ma an Dora da wasu manya har uku Kuma Babu wadda ta fito da sunan shi sai sunan eng AK Wanda a yanzu shike Kan gaba na karbar kwangila daga gwamnatin tarayya abinda ya girguza Kabir mashi har ya gurfana agaban me bawa shugaban kasa shawara


"Ranka ya Dade na tuba don Allah a gafarce Ni idan har da kuskure a cikin aikina to asanar Dani Zan gyara ban San abinda nayi ba aka mayar Dani gefe anyi mini alkawarin bani kwangilar gyaran wutar lantarki Amma sai ji nayi har anyi ta angama menene laifina?


Alh uba Dan yaro ya dubeshi 

"Agaskiya Kabir sunyi bincike ne akanka inda suka gano kana bada rata da yawa har aikin ya zamo Babu nagarta inda sukace aikin eng AK yafi naka nesa ba kusa ba shiyasa suka juya akalar Kan shi Amma idan zaka gyara ba damuwa bace sai nayi maka request  wata ta gaba abaka don nasan wata Kil waccan akasi aka samu


Ya zube Yana godiya da alkawarin zai gyara da haka ya taso ya taho Yana mamakin yadda eng AK ya samu SHIGA fiye dashi matukar kuwa hakan yake nufi to zai ware kwanji sai ya dawo da bara bana Akan harkar shi da ake son yi mishi fin karfi

Izzatu ma tamkar zata fasa kuka Amma tace itama ba zata taba yarda wani ak can da tagama rufe babin shi ya ce zai Kuma sake shiga Rayuwar ta da mijinta ba da sakel wallahi


Aguje fulani take gudu akan hanyar don dama haka take Bata tafiya sannu sai dai tamkar zata tashi sama 

Cikin sa a ta shawo  kwana daidai da wata katuwar mota itama ta shawo kwana Kuma hanyar Dole sai daya ya kauce kafin dayan ya samu zarafin wucewa 

Su duka suka sunno hancinan motocin su alokaci daya sukayi kallon kuda Atare inda atake ta ganeshi gayen Nan ne da yayi Mata Rashin mutunci har sau biyu dama neman shi take sai gashi sun Kuma haduwa inda zai Gane itama Yar zafin Kai ce Tama fi shi zafin Kai don haka sai ta kashe motar Taki fitowa shima ya kalle ta Yana mamakin kaddarar dake hadosu


Suka Kuma yin kallon kuda inda yaga har da harara take Aiko mishi inda yayi murmushi Wanda ya kular da ita shi yaki yin baya itama Taki yin baya kowa na takama da zafin kanshi sai akayi sa a itace akan hanya shi in za a kwana bashi da damuwa ta Gane hakan ne ganin yadda ya tada kida amotar ya bawa banza ajiyarta inda ita Kuma aka fara Kiran wayarta don tana Kan hanyar zuwa bikin kawar tane Kuma itace babbar kawa shiyasa ma ta fito aguje gashi Kuma akwai tazarar da zata iya takawa kasa ba don haka kawai sai ta fito don ganin ya Dora kanshi akan sitiyarin motar Yana lumshe ido tamkar me bacci


Kawai sai ji yayi gilas din motar tashi yayi Kara tatssss

Ya dago da sauri inda yaga ta sauke katon dutsin akan gilas din motar shi wadda ita da kanta ta Gane tafi karfin yaro shiyasa ma ta ke ganin Yana ji da kanshi


Abin ya Bata mishi Rai matuka gaya har Bai San lokacin da ya sauke Mata Marika biyu afuska ba abinda ya haddasa Mata daukewar gani na wucin gadi


Lokacin da ta dawo duniyar mutane ne ta soma wanke shi da manyan asharai kafin ta fasa kuka ta Kira wayar izzatu take fada Mata ga Wanda ke Mata wulakancin Nan ya mareta har idonta ya fice........


"Kina Ina yanzu? Ta kwatanta Mata aikuwa izzatu ta Figo mayafi ta fice tamkar zata tashi sama inda ta Miki hanya sai gata agaban su fulani nata rera kuka

Aguje izzatu ta fito ta soma wanka mishi Mari hagu da dama tanayi tana antaka mishi ashariya amma da yake namijin duniya ne Bai ko motsa ba Yana kallon yadda izzatu ke sauke mishi lodin zagi kala kala................

No comments