YAR AMANA (NUSAIBA YAR AMANA) 40-41
*NUSAIBA*
*'YAR AMANA*☘️☘️
*PAGE 40-41*
_____ Cikin mamaki IKIRAM tace "lalle NUSAIBA gaskiya ki sake tunani domin kuwa sam baku dace da JALALULDEEN ba"
Hhmm IKIRAM kenan haka kike gani amma nikam JALALULDEEN shine za'bina shi nakeso domin kuwa asonsa nayi nisa banajin qira"
"Lalle NUSAIBA Allah yaganar dake amma da zakiyarda da tayin da namiki da kindace wlh dan kuwa Yayana mutum ne nagartacce"
"Mmmmmtttttsss 'YAR AMANA tayi tsaki tawuce tatafi tabar IKIRAM.
Haka de rayuwa taci gaba da tafiya soyayya na taqara nisa tsakanin JALALULDEEN da 'YAR AMANA inda JALALULDEEN yake ta qara ingiza soyayyarsa azuciyar 'YAR AMANA.
Yauma kamar kullum 'YAR AMANA ne da JALALULDEEN suke hira acikin lambun gidan, inda suke zaune akan wasu kujeru masu kyau iskan gurin ne yake ratsasu yana sanyayasu cikin sauqin so JALALULDEEN ya kalli 'YAR AMANA yace "yace NUSAIBA ina tsoron ranar da za'arabamu" tashi 'YAR AMANA tayi ta dafe qirji tace "A'a JALALULDEEN karkasa zuciyata ta tarwatse domin kuwa zuciyata zata iya fashewa idan kanamin irin wanan maganar"
Shima Tashi yayi JALALULDEEN ya fuskanceta ya tsareta da idanuwansa masu rikitar da ita, sanan yace "tabbas NUSAIBA inaji ajikina za'arabamu sai de ina tsoron zuwan domin kuwa bazan iya jurewa ba bazan iya jure rashinki ba My Love"
"A'a JALALULDEEN bazan bariba tabbas bazanbari arabamu ba, to wama zai rabamu ne da kake irin wanan zancen"?
"Ni ai nasani habibaty baza aban keba domin ni talaka ne kukuwa Abbanku mai dukiya ne"
Kuka 'YAR AMANA tasa tabar gurin aguje tayi 'bangaren Anti Amarya, tana kuka.
'Dakinta tashiga takifu akan gado tana kuka, itako Anti Amarya dake zaune a parlour tana sawa Yasmin kaya sake baki tayi tabi d'akin 'YAR AMANA da kallo, tana mamakin to meyasa NUSAIBA kuka haka kama hanun Yasmin tayi tashiga d'akin 'YAR AMANA tsayawa Anti Amarya tayi ajikin gadon da NUSAIBA ke kai, cikin sanyin murya Anti Amaryar tace "NUSAIBA lafiya me akayi miki kika shigo kina kuka haka?"
'YAR AMANA kuwa cigaba da kukanta tayi bata kula Anti Amarya ba, zama Anti Amarya tayi abakin gadon Sanan tace " magana fa nake miki Nusaiba"
Cikin kuka 'YAR AMANA tad'ago ta dubi Anti Amarya tace "anti wai za'arabamu da JALALULDEEN?"
"Bangane ba NUSAIBA za'arabaku kamar yaya waye zai rabaku"?
"Anti shine da kansa yace min shi yanaji ajikinsa za'arabamu nikam Anti idan ba Yaya JALALULDEEN bazan iya rayuwa ba"
'YAR AMANA ta qarasa zancen tana shesheqar kuka.
"A'a NUSAIBA ki kwantar da hankalinki bazan bari hakan tafaru tabbas bazan bari ba, domin kuwa nasan kunason junanku kuma ke Alheri ce arayuwar JALALULDEEN sbd haka ki share hawayenki kinji NUSAIBA"
murmushi 'YAR AMANA tayi tace "Shikenan Anti Ngd sosai ina matuqar alfahari dake da kuma baffana domin kud'in na mussaman ne arayuwata.
*Italy*
A Italy kuwa ABUDULJABBAR kwana biyunan yakasa gane kansa domin sha'ar 'Ya mace nema take tafi qarfinsa duk da azimin da yakeyi, qiran dr Musa yayi awaya yasanar dashi komai, nan dr Musa ya haushi da fad'a yana cewa "haba ABUDULJABBAR kasani fa kai mutum ne mai lafiya tayaya kake tinanin zaka iya rayuwa ba mace? Hakan kuwa bazai yuwuba matuqar kai cikakken namiji mai lafiya ne sbd haka yakama kadawo gida ka rungumi matarka"
Rintse ido ABUDULJABBAR yayi sanan yace" ni nayiwa kaina alqawarin bazan kuma kusantar FINAH ba danni nacire tama ababin ratuwata"
"A'a abokina karkace haka kasanifa har yanzu FINAH tanan amatsayin matarka sbd haka mekake nufi ne? Tabbas kana cutar da ita tsawon shekaru nawa yanzu baka tare da ita please ABUDULJABBAR kayi tinani wlh inbanda Matarka tana sonka tabbas da yanzu tafara biye-biye dan kuwa sam yawancin matan basu da haquri sbd haka kadawo gida ABUDULJABBAR mekake nema wanda baka samu ba iye"?
"Hmm Dr Musa kenan baza kagane bane nifa na haqura da FINAH domin kuwa bata da amfani agareni bawani so da takemin da tana sona da bataqi had'a jini daniba"
"To naji ABUDULJABBAR tinda hakane ka qara aure"
Ras,Ras, gaban ABUDULJABBAR yafad'i tinowa yayi da 'YAR AMANA matarsa, nan yayiwa dr Musa sallama ya katse wayar yafad'a tinanin 'YAR AMANA
Inda Azuciyarsa yake cewa "Ashefa ina da wata mata daban? Wata zuciyar kuma tacemar to mezakayi da wanan kucakar bagida jiyar yarinyar wanda har abada baza tata'ba waye waba, ai kawai ka haqura kanemi wata yafimaka"
Tsaya wa yayi yana tuno kamanin NUSAIBA nan kyawunta da yarintarta da surorin jikinta suka masa qawanya akai yaji yakamu da son yarinyar da kuma muguwar sha'awarta tabbas daddy yayi min gata da bebari nasaki yarinyar nan ba da yanzu ya zanyi balle yanzu nasan taqara girma zata iya dani" ABUDULJABBAR ya fad'a yana shafa kansa, nan kuwa yasa aransa tabbas Nigeria zai tafi kwana nan domin yasamu ya kawar da matsalar dake da munsa.
Yau kam MUM d'in FINAH ce tazo da kanta inda take ta tijara akan sai tatafi da FINAH, itakuwa FINAH fir taqi binta tace ba inda zata, MUM ce takalli Mum d'in FINAH tace " haba Hajiya tinda taqi mana kibarta dan Allah tayi zamanta ad'akin mijinta
Cikin masifa Mum d'in FINAH tace " eh kace haka tinda ba 'yarki bace to wlh nagaji da sa'ido 'yata daya dal tana zaman rashin miji, shi gantalalan d'anaki yanacan yana shashancinsa shine zakice nima nabar 'yata tazama shashasha irinsa to kinyi qarya sbd haka FINAH maza ibo kayanki mutafi"
"Nifa Mum kiyi haquri domin ba inda zani koda zanshekara dubu inanan inajiran mijina"
Salati MUM d'in FINAH tayi tace " oh ni 'Yasu wanan wani irin sone haka kode asiri sukayimiki? To wlh inma asirin sukayimiki sai nayi maganin abun........
Hhmm muje de zuwa
Please zanfita awasu group da nake post, domin group sunyimin yawa sbd haka karku daina ganin post kuyi tananin banayin update ne, sbd haka zaku iya neman littafin awasu group in ana kaimusu, ko kuma duk maiso tayimin magana tawan number 08114867197 insata a ainihin group din da nake post kullum, amma fa idan kinsan kin iya sharhi.
Dan idan kinkaranta kiyi mini shere a Sauran groups please
*ASSTAGAFIRILLAH WA A TUBU ILAIKA*

No comments