Breaking News

YAR AMANA 11-12

 👩‍🦰👩‍🦰👩‍🦰👩‍🦰👩‍🦰👩‍🦰👩‍🦰👩‍🦰

*NUSAIBA 'YAR AMANA*

Page 11&12

__Shi kuwa ABUDULJABBAR baima tsaya sauraransu ba ya shiga motar sa yabar gidan, tuqi ya keyi amma ransa a'bace yake matuqa sbd da rainin hankalin da su Alhaji Halliru Suka kawo masa nason su bashi cin hanci domin ya rufamusu asiri suci gaba da wadaqa da kud'ad'en talakawa, wani wawan burki yaja ya tsaya agefen titi, yana huci hanunsa yad'aga ya doka akan sitiyarin motar sanan yace " Alhaji Halliru! Alhaji Qasimu! Alhaji Biliyaminu! Bazanta'ba qalekuba kusha tabbas sai kungirbi abunda kuka shuke kud'ad'en talakawa da kuka kwasa tabbas sai kundawo da shi" tsayawa yayi na wani mintoci yana nazari sanan ya tuqa motar ya nufi gida ransa a'bace.

'YAR AMANA kuwa yanzu abun duniya duk ya isheta domin kuwa yanzu bata isa tafita tallar nono ba tadawo sai yaran rugartasu sunrakota suna mata waqar wai karuwa ce ta dawo daka karuwanci har qofar gidan su suke rakota suna mata waqar tayi karuwanci haka zasu zuzugureta kuma tashiga gida Gwaggo ta had'a mata dukka, shi ko Baffa bai iya komai saide ido yana so yayi magana ma amma yakasa ji yakeyi kamar andene masa baki, ita kuwa 'YAR AMANA rayuwar rugar tasu duk ta isheta domin kuwa yanzu bata da wani 'yanci arugar kowa ma gudunta yakeyi dan kuwa takoma tamkar mujiya bata da halin shiga cikin jama'a har d'aukar karatun tadena zuwa domin kuwa Gwaggo ta riga da tamannamata baqin fenti mai wuyar goguwa dan kowa kallon karuwa yakeyi mata agarin sbd tallar nonon da take tafiya alhalin bata da aure,  gashi bata siyarwa har dare yayi kullum sai dare take dawowa rigar shi yasa kowa ya tsaneta domin kuwa ko matan auren masu tallan nono basa kaiwa dare sai ita Shi yasa kowa yake mata zargin karuwace dama gata da jikin girma Allah yabata,  qirjinta sai qara cicika sukeyi tamkar zasu fashe shi yasa hatta Gwaggo itama tafara zargin da gaske 'YAR AMANA maza takebi dan haka Gwaggo take bi gida gida a rugar tana cewa ita 'YAR AMANA ta isheta domin kuwa tafara bin maza, ai kuwa matan dake rugar kowa da irin shawarar da yake bata akan nau ikan azabar da zata nayiwa 'YAR AMANA harma tagaji tagudu dan kanta tabar rugar, ai kuwa Gwaggo tad'auki shawararsu dama abun take sonji kenan, kullum kuwa da irin azabar da takeyi wa 'YAR AMANA, sanan tallan nono kuwa kullum ba fashi sai ta jeshi kuma bata isa tadawo da sauraba domin kuwa Gwaggo tace " inma kwana zatayi to ta kwana inde zata kawo mata kud'i haka de rayuwar 'YAR AMANA taci gaba da kasancewa cikin tsanani da talla,  yau kam tun asuba Gwaggo ta tashi 'YAR AMANA ta d'auki tallan fura domin kuwa yau Monday kasuwar rugar tasu keci dan haka k'atuwar k'warya Gwaggo ta cikawa 'YAR AMANA da Nono da kuma wata madaidaiciya asama ta fura,  haka 'YAR AMANA ta d'auki kwaryar tana rinjayarta kamar zata fad'i ga duhun asuba dan ko wayewa gari baiga ma yiba ta nufi kasuwar garinasu.




_________________________


Shi kuwa ABUDULJABBAR yau wani aiki ne ya taso masa a Abuja domin kuwa yana ma Office qiran aikin ya sameshi  a ma'aikatarsu dake Abuja dan haka cikin sauri ya tatara komai nashi ya nufi gida domin yaje ya shirya ya nufi Abuja, yana shiga parlour d'in gidan ya tarar da Mum d'insa da matarsa FINAH zaune a parlour suna kallo inda FINAH tayi matashi da cinyar Mum ita ko IKIRAM tana school abunta, Sallama yayi ya shigo cikin parlour d'in da saurinsa amma ba wanda ya amsamar domin kuwa sai cika da batsewa sukeyi tinsan da da Daddy yasa baki acikin magarsu Mum take fushi dashi, itama FINAH sai cika da batsewa takeyi, da sauri ya haye sama ya sanja kaya yasauqo hanunsa riqe da jakar aikin sa wanda yake adana duk wasu muhimman bayanansa.

Gurin Mum ya nufo ya duqa a gabanta yace  "Mummy  zanyi tafiya ki samin albarka yanzu nan qiran gagawa ya sameni zuwa Abuja" banza tayi dashi tamkar ba ta ji shiba, itako FINAH sai harara take watsa masa.

Cikin rawar murya ABUDULJABBAR yace " Mum dan Allah me namiki ne kike fushi dani ? please kiyimin magana dan Allah ko zansamu nutsuwa"


"Tayaya ka ke zaton bazanyi fishi da kaiba ABUDULJABBAR tinda sbd kai daddynka yake maganar qarin aure sbd da na maka fad'a akan zaka qara aure shine nima wato kishiyar hardani bata wuce kaina ba tayaya bazanyi fushi ba iye?"

Cikin muryar tausayi yace " kiyi haquri Mum shi daddy ma ya manta da maganar kinsanshi ba mutum bane maison ha yaniya sbd haka ki kwantar da hankalinki ba abun da zaifaru"

Kallonsa Mum tayi sai taga d'anata duk ya bata tausayi domin kuwa har rama yayi a kwananan, itade tasani tabbas FINAH bata dace da rayuwar d'anta ba inde ayanayin d'abi'une domin kuwa sam d'abi'un FINAH basu masa ba, amma ya ya iya dolene yayi haquri domin kuwa ita tana son FINAH dan kuwa iyayenta manyan mutanene kuma FINAH kyakyawar yarinya ce wanda zata sama mata jikoki kyawawa. Sbd haka dolene yayi haquri da halin FINAH.

Cewa tayi "Shikenan ABUDULJABBAR yaushe zaka dawo daga Abujan?"

"Mum ayau d'inanma qila zandawo komin dare". "To Shikenan Allah ya kiyayemin kai aduk inda kake" cikin jin dad'i yace " Amin Mum nagode"

Itako Mum tashi tayi tabar gurin ta nufi sama, Mum na tashi itama FINAH tatashi  zata bar gurin, shi kuwa ABUDULJABBAR kamo hanunta yayi ya tsareta da ido yace " haba Nafisa mijinkifa tafiya zaiyi ko Allah ya kiyaye hanya babu?"

Wani mugun kallo ta masa sanan tace " ina ruwana da kai me kake tsinanamin inbanda baqin ciki" 

" haba Nafisa me yasa zakice haka? Ki sanifa komai da yake faruwa a gidan aurenmu lefinkine sbd haka ki gyara halayenki ni kuma zanmiki koma menene"

Warce hanunta tayi tabugamar tsaki mmtttssss zata bar gurin yasake jawota tafad'o jikinsa nan yarungumeta ya fara kissing d'inta tini FINAH tanemi tinaninta tarasa harta lulula wata duniya ita kam tasani mijin ta d'an baiwane domin ya iya soyayya iya soyayya yasan ta inda zai bi da mace,  saide mugun jan aji da ya masa yawa. Shi kuwa ABUDULJABBAR ko da yaga FINAH ta naneman zaucewa dan haka sai ya kyalleta akunan ta ya rad'a mata "Akwai kud'i a d'aki"  da saurinsa yafice yabar gidan.

Kwalla taji ta fito a idonta domin kuwa itakam tana son mijinta domin kuwa ya iya kula da mace shi yasa take masifar kishinsa,  gashi duk kudin iyayenta basa gabansa hakan bai hanashi ya ajiye mata kud'ad'e masu yawa ba, itakam ta san samun miji irin ABUDULJABBAR babban da ce ne, tana cikin tinani ta ji ringing d'in wayar ta tana d'agawa ta ga Abbanta ne ke qiranta d'auka tayi bayan sungaisa yake tambayarta ABUDULJABBAR dan haka tace mar yanzunan ya tafi Abuja, tambayarta yayi yaushe zai dawo nan tasanar dashi da yace yau zai dawo komin dare, dan haka ya mata sallama ya kashe wayar.

Ashe Abban FINAH tare yake da su Alhaji Biliyaminu, nanfa yasanar dasu komai, ai kuwa suka sheqe da wata mahaukaciyar dariya inda Abban FINAH yace " lalle ABUDULJABBAR yau kam sai de uwarka ta haifi wani duk da kuwa 'yata tana sonka amma dolenta tayi haquri domin kuwa zata samu wanda ya fika"

Nan Alhaji Halliru ya qira yaransa akan su tare ABUDULJABBAR akan hanyarsa ta dawowa kafin ya shigo gari suyi gunduwa-gunduwa dashi.

Nan kuwa yaran Suka a minta da wanan Aikin, inda su Abban fina ranar wuni sukayi suna partyn matsalarsu ta kawar.



¤¤¤¤¤¤¤.      ¤¤¤¤¤¤¤



A 'bangaren 'YAR AMANA bata samu dawowa gida ba sai dare domin kuwa yau sai mangariba nononta yaqare kasancewar masu sai da nono sunyi yawa akasuwar yau, dan haka kuwa ko da ta taho gida duhu yayi ga lokacin da munane shukoki duk sunfito guri yayi duhu hanyar ba alamun haske ko kad'an, haka 'YAR AMANA ta ringa ratsawa ta cikin duhun ciyayi da shokoki har takusa shiga cikin rigartasu  domin kasuwar acan bayan rugarsu take , sai taga wasu gungun matasa, atsatsaye, aqalla za sukai su 6 nan gabanta yashiga dukan tara-tara, amma haka ta rumtse ido tazo zata wuce tagabansu domin ba wata hanya da zata bi,  kawai sai taji ansa mata qafa, ai atake kuwa ta zube a gurin, tafad'i qasa da 'bas, suka matasan dariya suka kama yi mata, cikin kuka 'YAR AMANA tace " dan Allah me namuku? kubani hanya inyi tafiyata" 

Babban sune yace " ke  karuwar banza anufinki ba musan me kike yi bane to bara kiji dukkanmu nan sai munbiya buqatarmu dake, kowa sai ya kwanta dake anan gurin domin ya zama dole muma mud'ana ba wai ki ringa kaiwa mazan wasu rigarba, ai muma muna so yaude kam dolene muma ayi damu" kuka 'YAR AMANA tasa tana cewa " wlh ni ba 'yar iskaba ce dan Allah kuyi haquri kubarni intafi ni banma san me kuke nufiba" babban nasu cewa yayi zaki sani yau dan ubanki maza kusa mana ita cikin duhuwarcar" haka maza biyu sukaja 'YAR AMANA tana ihu tana komai sukayi cikin duhuwar da ita...............


Hmm duk mai so cigaban labarin zai biya #300 kacal ta wanan number account din


4203060435 Lubabatu yahaya Gambo kuma atura shedar biya ta wanan number 08114867197 domin neman qarin bayani atuntu'beni da wanan number dake sama, please idan kinsan ba siya zakiyi ba karkiyi min magana.

Sai najiku masoyan asalin😍😍😍😍

DOmin kuwa anan ne Mummyn MINAL zata ga nata masoyan🥰🥰


*ASSATAGAFIRULLAH*🤲

No comments