WANDA BAIJI BARI BA 13-14
13&14
Cikin Mamaki Umma ta bi Alhaji Babba da kallo har ya kusa ficewa daga tsakar gidan, da sauri ta rufa mai baya tana tafe tama ƙwalamai kira, " Yaya Babba! Yaya Babba! lafiyz mai yake faruwa ne? Jama'a ku taimaka mai nake gani haka " Umma haka ta ƙarasa har ƙofar gida tan neman agaji, Alhaji Babba ko waiwaye bayayi duk yanda mutane suka zo dakatar dashi sun kasa, yana cikin gudu babbar rigarsa ta taɗe shi baiyi aune ba ya gungura gefe ya faɗi da rufda ciki.
Mutane ne suka taru akansa sai a lokacin Umma ta ƙaraso Amadu shi da Labaran sunzo wucewa suka ga taron mutane suna leƙawa suka hango mahaifinsu ne kwance sai maida numfashi yake, abinka da jikin girma ga ƙiba ga kuma gudun da yasha.
Buɗawa sukayi suka shiga cikin tashin hankali suka fara yiwa mahaifinsu sannu, Alhaji Babba ko amsa musu baiyi ba ya fara yunƙurin tashi da ƙarfinsa.
Umma da ke gefe ta ce, " Yaya Alhaji ka bari ka huta karka tashi jiri ya kwasheka " Alhaji Babba ɗagowa yayi ya watsawa Umma mugun kallo sannan ya sa hannu biyu ya hamkaɗe hannun Amadu, da yake sun san halin mahaifinsu suka ɗauka ko wahala ce ta sashi yin haka cikin halin ko'inkula Labaran ya riƙo kafaɗar Mahaifinsu ya ce.
" Bi a hankali Alhaji " Alhaji Babba a ƙufule ya cewa Labaran, " Zanci Uwarka sakarmun hannu " Labara cire hannunsa yayi jiki a sanyaye ya koma gefe, Alhaji Babba miƙewa tsaye yayi sai da ya ƙarewa mutanen gurin kallo kawai suka ga ya ƙara bazama a guje.
Da sauri suka rufa masa baya cikin zafin nama suka rirriƙeshi, aikuwa kamar jira yake ya fara zazzaga musu ruwan masifa.
" Ku sake ni aljanu karsu kama ni duk wanda ya hanani tafiya Allah ya isa, ku kyaleni ni naga abinda na gani " Wani daga cikin ƴan kallo yace, " Kai wannan tsohon fa da alama fa wannan tsohon yana cikin yanayi bakwa gajin irin sumbatun da yake yi "
Alhaji Babba na jin haka yace, " Ubanka ne yake cikin yanayi " saurayin nan cikin tsiwa ya ce, " Tsoho ka iya taku fa wallahi karka kaini bango "
Amadu na shirin yin magana sukaji wani yaro ya ce, " Lah kunga buhu yana tafiya " gabaɗaya hankulan mutanen gurin komawa yayi inda yaron nan ya nuna musu, aikuwa take mutane suka hau zaro ido da mamaki, tsoro ne ya kamasu lokacin da suka fuskanci tunkaro su buhun yake yi.
Alhaji Babba na jin an ambaci buhu ya tuno da buhun da ya gani akan rijiya aikuwa da sauri ya zabura yana cewa, " Wallahi kowa yayi ta kansa wannan buhun na aljanu ne " Alhaji Babba na rufe baki gaba ɗaya mutanen gurin suka tarwatse kowa yayi ta kansa.
Umma da batayi nisa da gida ba da sauri ta juya gida tana ƙoƙarin rufo ƙofa maƙociyarsu Larai ta faɗo domin neman agaji, da sauri Umma ta rufo ƙofa tana maida ajiyar zuciya.
Suna shiga ciki ta fara ƙwalawa Yusra kira domin ta shaida mata abinda yake faruwa, ihun da Umma ta fara jiyowa daga cen ɗakin Yusra ne yasa ta shiga da sauri dan ganin maiyake faruwa.
Tana zuwa ƙofar ɗakin ta samu ƙofar a rufe ta window ta leƙa dan ganin mai ya samu Yusra ga mamakinta sai gani tayi Yusra ita kaɗai take ihu tana tsalle tana cewa ta daina.
Abinka da farar Mace jikin Yusra duk yayi jawur, da alama bulala take sha ta ko'ina ga ƙofa taƙi buɗuwa, Larai na ganin haka cikinta ne ɗuru ruwa da gudu ta juya ta nufi kofa ta fice jikinta na rawa.
Umma da take ta tambayar Yusra me yake damunta, lura tayi da alama Yusra bata ma san mai Umman take faɗa ba saboda kururuwar neman agajin da take yi.
Ganin tsaiwar ba zata fushshe da Umma yasa ta juya ta fita tana neman taimakon mutane, abinda ya bata tsoro unguwar tsit kake ji babu kowa da Alama wannan buhun ne ya razana su kowa ya nemi maɓoya.
Shawarar zuwa gidan Mai Unguwa ce fa faɗo, kai tsaye cen ta wuce tana zuwa ta samu dandazon mutane a gurin, Mai Unguwa yana daga Kan kujera yana sauraron abinda jama'arsa ke faɗa game da sabon labarin ta'ajibun da ya sauka a unguwar.
Umma na zuwa ta fashe da kuka tana sanar da shi halin a Yusra take ciki, sai da ya gama sauraronsu tsaf sannan yace.
" Jama'a Salamu Alaikum, duk munji labaran hikayar da kuka zo mana dasu masu kama da tatsuniya " Murmusawa yayi sannan ya cigaba da cewa, " Munyi mamakin yanda ake nema ayi wasa da hankulanku a matsayinku na magidanta masu hankali, wannan ba komai bane fashe rufa ido da kayan siddabaru "
Alhaji Babba Haushi ne ya rufeshi amma sanin matsayin Mai Unguwa a gurinsu yasa ya gimtse fushinsa ya ce, " Ranka shi daɗe a duba dai lamarin nifa nafi zargin lamarin nan na fusatattun Aljanu ne, domin haka kawai bazamu wayi gari da wannan lamarin ba sai dai idan tsokano su akayi "
Mai Unguwa gyara zaman rawaninsa yayi sannan yayi murmushi yace, "Aljanu fa? Aljani ya bayyana a unguwa ta, Aljanun sunci gidan su ni zasu gwadawa hatsabibanci? Kai Saminu a ina Buhun Aljanun yake in wargaza amiyrsu " kafin saminu ya bada amsa Mai Unguwa ya hango wani fuskar Jaki a jikin wani mutum da ke cikin jama'a, idanunsa guda huɗu ne sai dai jikinsa irin na mutane ne ƙafafunsa masu kofato ne.
Da ƙarfi yaji cikinsa ya kart masa gabansa ya faɗi take gumi ya fara keto masa.
*FATAN ALHERI GAREKU MASOYA NAYI MAMAKIN YANDA LITTAFIN NAN YA SAMU KARƁUWA INA GDY MASU COMMENTS ALLAH YA BAR ƘAUNA❤️❤️❤️❤️❤️*👏🏼👏🏼👏🏼
_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
No comments