Breaking News

TSANGAYAR MALAM 31-32

 _             3️⃣1️⃣-3️⃣2️⃣

Ji yai an damƙi ƙafafunsa an yarɓar a ƙassa,cikin zafin nama ɗan malam ya haye kan malam talah ya danne,malam talah ya soma ƙoƙarin ƙwatar kansa ashe dai yin kuka ma rahama ne gaba ɗaya malam talah ya nemi yanda zai koka ya rasa ɗan malam kuwa da Allah ya bashi sa'a take ya naɗe hannayen

malam talah ya zargo ƙafafuwan da igiya ya ɗaure yadda igiyar bazata cuci jikin malam talah ba,amma babu yanda zai yi ya iya kwancewa idan ba kwance shi akayi ba.

     Jin yanda malam talah ya ɗauru katamau kamar ragon layya ya soma wani irin gurnani yana ƙoƙarin yadda zai yi ya ƙwaci kan sa,abinka da me ɗan ƙaramun jiki tsam ɗan malam ya sunkuce malam talah sai a mashinfiɗar sa ya dire sai a lokacin malam talah ya fara kuka yana istigifari da neman rahama ga Ubangiji cikin tsawa ɗan malam ya dakatar dashi shima sai hakki yake yana huce tsabar kokawar da ya sha da malam talah kafin ya samu ya ɗaure shi tam,cikin tsawa ɗan malam ya ce"


"Idan baka rufe mun munafikin bakin nan na ka a gun nan ba na rantse maka da Allah zan maka ɗaukar daƙiƙa ɗaya ka baje ko shurawa babu"


Ummm naaaayiiii,nayii wallahi nayi shiru ko tari bazan kuma yi ba innalillahi mutuwa wayyo Allah,Allah na tuba ka yafe niiiiii.



"Daka aikata me ya kai bil adama?


"Bazan ɓoye maka ba abubuwa da dama musamman cin haƙƙin da bana wa ba,sai kuma malam talah ya fashe da kuka ɗan malam ya washe bakin sa yana dariya abun nema ya samu,ganin uban haƙoran ɗan malam zaƙo zaƙo daya dashe bakin ya ƙara rikita malam talah sai zufa yake yana makyarkyatar dole ɗan malam ya ja wani benci daga gefe ya matso dai dai kan barsolin malam tala dake ƙyalli ya zauna,cikin murya dashasshiya ɗan malam ya kuma cewa"


  "Kafin taka ta sameka ina son ka sanar dani wani abu.


"ko meye shi zan faɗi maka bazan taɓa yi maka ƙarya ba koda ta sakan guda ce, ni dai abarni da lafiya ta da raina dan Allah La'illaha'ilallahu harira sai takaba wayyo musalele an zama marayin dole.


Ya Kaiii bil adama idan mutuwar ka ta zo ka isa ka hana ne ko ka dakatar.


Wa ne ni, na isa dan ubana,wallahi haƙƙin jamma'ah kawai nake dubawa.


Sam baka san haƙƙin jamma'ah ba daya rataya akan kada ka  sani da baka shiga haƙƙin nasu ba ka cuce su.


Ranka shi daɗe wall.........dakata talah ni ba ranka shi daɗe bane.



Umm yallaɓai.


Ni ba yallaɓai bane ka gyara kalamanka.


Shiru malam talah yayi sai shassheƙa yake yana karkarwa ɗan malam yace"


Kasan me ya kawo ne wurin ka?


Ummm ummm,malam talah ya faɗi haɗe da girgiza kai kan sa na ƙassa dan tsoron haɗa ido yake da halittar ɗan malam ya cigaba"


Na taho daga wata uwa duniyar ce dan in shaida saƙon da aka bani,akan abinda kuka haɗu kuka ƙulawa wani bawan Allah da ba ruwansa da duniya,lahirar sa da neman rahamar Allah yasa a gaba,shiru ya biyo baya daga chan ɗan malam ya ɗora"


"Ya kai ɗan talah ka sanar dani abinda malam balarabe ya aikata muku anan duniyar da kuke son ƙuntattawa rayuwar sa shi bai ƙuntattawa taku ba.



'Shikenan magana ta ƙare kashina yau ya gama bushewa ranka shi daɗe,au yallaɓai,kar ka kuskura ka ƙara mantuwar lamba ka kirani da sunan bil adama ni ba mutum bane,cikin kakkausar murya ɗan malam ya furta nan da nan fitsari ya ƙwacewa malam talah ji kake shaaaaaaaa abinka da gaddi take ya jiƙa shimfiɗar gaba ɗaya sai kukan zuci yake yana ta maimaita "Wala'yahuduhu'hiszuhuma wa'huwal'aliyul'azim,musamman da yaji ɗan malam ya ambaci shi ba bal adama bane yo idan ba aljanin ba wannan sufar ai ganin ta masifa ce babba,karaf ɗan malam ya yankewa malam talah tunanin sa da"


"To Ƙona ni ka huta tunda haka kake da buƙata,amma bari kafin ka ƙoneni ni zan fara ƙone maka barsolin kanka,nan take ɗan malam ya fidda wata ƴar tsumagiya me kai biyu ya dubi barsolin malam talah ya shiga laftawa barsolin tsumagiyar ba shiri malam talah ya soma bayani"



"Hakimi ne yasin hakimi ne ya ƙwace rawanin balarabe,kuma tsabgawa malam talah tsimagiyar ɗan malam yayi nan da nan ya sauya bayani""


Malam balare nake nufi,duk yanda aka shirya ƙula ƙular da yanda suke rabe albarkacin gonar malam balarabe har cewar da hakimi yayi sai sun ƙuntatawa rayuwar sa kaf malam talah ya zayyanewa ɗan malam,ɗan malam yayi murmushin mugunta bayan ya zane kan malam talah da tsimagiyar sa ya ce"


"Saƙo maƙoƙo daga babban mu dake jinsin *TAUFIK*,na daular larabawan Aljannu duk wanda ya kuskura ya sanya rawanin malam balarabe to babu shakka kashin sa zai baushe ya ɗauka a haka ya cinye kuma gabansa zai koma bayansa,bayansa kuma ya dawo gabansa ga ƙahu da zai ɓullo daga kowa ce gaba ta jikinsa kai rayuwar da zai yi nan gaba Allah ne kaɗai ya san......take malam talah ya ɓingire ya some jin tashin hankalin da baitaɓa ji ba,ganin malam talah a kwance ya bawa ɗan malam damar shafe barsolin malam talah da ƙarara har bayan kunnuwan sa da ƙasan wuyan duk ya baje masa shi shana shana a ajiki ya kwance igiyar daga jikin sa ya fita daga ɗakin yayi gida.




     Kafin malam ɗan talah ya farka tini ƙarara da ɗan malam ya sharɓana masa ta ya fara aiki ai tun farkawar sa gidan ya shiga masifa babu abinda malam ɗan talah bai fasa ba yana asosa masa asosa yayi kan wannan yayi kan wanchan haka maƙota da jamma'ah na gidan da harira aka taru da yara sai net ɗin kwanciya aka farka akayi tara tara da ƙyar aka nannaɗe malam talah sai ihu yake yana a sosa masa asosa rawanin hakimi ba shiri aka nemo kura aka saka shi sai ƙofar gidan hakimi da rawanin a hannun harira. 


Tun daga cikin gida hakimi ya tsinkawo muryar malam talah na asosa masa asoso rawanin hakimi,take cikin hakimi ya kaɗa nan da nan yayi bayi bai jima da shiga ba ya fito yayi ƙofar gida,cike fadar take da jamma'ah gefe kuma su malam muttaƙa da ado ne da sauran mazauna faddar sai chan ɓarin haggu malam talah dake cikin net sai asosa yake yana zabura zai ƙwace kowa yayi dummm hankali ya koma kan hakimi da ƙyar ya iya ɗosan ɗuwai ɗinsa kan kujerar ya zauna yana kalon kowa.






…………






Duk dukan da akayiwa sani ƙolo sam bai furta sunan attahiru ba har ɗaurin goro malam nakan buzu yasa akai masa da bulala tamanin kamar yayi sata hakan ya ƙarawa sani ƙolo ƙaimi wajan ƙin bayyana sunan ɗan malam na ainihi ƙarshe da garadan suka kwance shi ma cewa yayi"in da sabo ai an riga an saba,ɗaya gardin ya naushi bakin sani ƙolo take jini ya bayyana zuciyar sani ƙolo ta kuma ƙeƙashewa idan kashe shi zasuyi shi sam bai san sunan ba abinda yake ƙara maimaita wa kenan na kan buzu ya fusata a take ya buje ƙasa ya buga ya kuma bugawa ya baje charbi nan da nan ya tsinkayo ƙwaya ɗaya ya kuma buga ƙasa taƙi bashi abinda yake so ta bashi,ture fefen ƙasar yayi gefe ya miƙe cikin iska ya zari wata ƙatuwar laya dake rataye a bukkar ya dafe yana ambatar wasu irin kalamai masu kama da surƙule ya  buga cinyar sa ta hagu.

    Ko daƙiƙa bai ƙara a bukar ba ya ɓace ɓata daga bukar.😳






_*To Ina kuma su malam me tsangaya aka nufa,dani daku masoya makaranta duk mu duƙufa laluɓo inda malam nakan buzu ya shilla🤔*_




_*Comments/Share*_

No comments