Breaking News

TSANGAYAR MALAM 27-28

            2️⃣7️⃣-2️⃣8️⃣

Iya firgicewa da kiɗimewa malam ƙasimu cinnaka ya kaɗu kwata kwata baya gane fari balan tana baƙi har wata zabura yake yana karkarwa ɗan malam ya dakata daga waƙar  da yake yana takawa ya dubi malam ƙasimu cinnaka ya ɓarke da mahaukaciyar dariya daga chan kuma yaja bakin sa ya tsuke haɗe

da ƙwalalo idon sa dukka biyun ya sauke ajiyar zuciya da ƙarfi ya ce da malam ƙasimu cinnaka dake karkarwa hawaye na gudu a fuskar sa ko magana kasawa yayi sai zare ido yake ya ce"'


"Saƙo maƙoƙo zuwa ga babban limamin garin lambu..............shiru ya biyo baya daga chan kuma ya ɗora""


"ina me sanar da liman cewa" wannan rawani da ke kanka ko in ce aka naɗa maka tabbasa shine sanadin mutuwar ka idan har baka rabu da shi ba nan ba da jimawa ba zaka bar duniyar haihata-haihata bayan kasha wahala ta ƙin ƙarawa,saboda haka kaka tace a shai da maka duk yanda zakayi ka tabbata ka rabu dashi kafin lokacin ka ya riske ka saboda shu'umin rawanine bare kai ɗan taka haye ba ɗan gado ba,sannan dole ne ka dinga zuwa kullum ta Allah kana neman gafara wajan malam balarabe bawan Allah damo sarkin haƙuri idan katashi tafiya kasa yaranka manyan masu jini a jika su garzaya da fatanyar su dan taya bawan Allah nan aikin noma idan ka kasa ɗaya daga cikin biyun nan hmmm kuma ka sanar masa da inda kaje ka kai masa ɗan sa kuma kaje ka dawo masa da shi har gida idan ba haka ba, ba sai na faɗa maka komai ba zan sake waiwayo wa gareka,na barka lfy limamin taka haye sai wani jiƙon idan na waiwayo gareka,kamar wani biri ɗan malam ya shila sai windon malam ƙasimu cikin abinda bai wuce daƙiƙa ba ɗan malam ya ware shi ko malam ƙasimu na nan inda yake jikin sa sai ɓari yake bakin ma nayi ido shata shata da hawaye hanci ya cika da majina ba kyan gani  sai sambatu yake maganganun ɗan malam na yawo a cikin kwanyar kansa.



Tun cikin dare ladiyo ta farka yaran duk bacci ɓarawo yai awon gaba da su a sanɗa ta fito daga ƙasan gadon ta iske malam ƙasimu baje cikin mawuyacin hali ruwa ta yayyafa masa babu adadi sam hankalin sa baya jikin sa gashi dai sanƙamƙam a zaune ido a buɗe amma bai san abinda yake ba gashi ita kanta a tsorace take ƙwaƙwaran motsi idan zatayi sai da dabara har asubahi ta yi,sai da gari ya waye tangargar ladiyo dake ɗaki da yara da malam ta saka ihu me ƙarfi da neman taimakon maƙwafta ai ba shiri sarai da sauran yaranta suka fiffito suna ƙwarawa ladiyo kira hango sarai da ladiyo tayi ta windo take ta kuma kifewa ta sume ɗaki ya ƙara karaɗewa da iface iface duk gidan ya hargitse aka rasa gaba da bayan duk wani bal'adama dake cikin gidan,ana haka maƙwafta sukayi dan dazo a cikin gidan da ƙyar aka iya bale ƙofar yaran duk suka fito a jiga ce suna kuka dan magana ma kasawa sukayi malam ƙasimu kuwa kinkimo shi akayi kamar saƙago aka zaunar dashi daram a tsakar gida ke waye da jamma'ah maganar duniya yaƙi magantuwa sai zare idanun yake yana ƙif-ƙifta ido ladiyo ta farfaɗo karaf idon ta akan sarai ta sake ɓingirewa ta kifa kowa ya shiga salati an sallallami da jajinta abinda ke faruwa.


    Cikin ƙanƙanin lokaci magana ta zaga ko ina ƴan uwan malam ƙasimu suka garzayo gidan dana ladiyo da sauran maƙwafta kowa na tofa albarkacin bakin sa sarai sai kuka take tana ta'ajibun irin abunda ke faruwa ta rasa daga inda matsalar take,musamman da ladiyo ke suma da sunyi ido huɗu jamma'ah suka tasa ƴaƴan ladiyo da tambaya ai buɗar bakin su suka ce""


"Kaka rakiya ce ta dawo jiya da tsakar dare wai zata tafi da baba da inna,saɗaf saɗaf maƙota kowa ya kwashi silifas ɗinsa ya fece gari ya ɗauka fatalwa ta bayyana,Habu ƙani ga malam ƙasimu ya bada shawarar a kifawa malam ƙasimu mari guda uku kyawawa wata ƙila hankalin sa da tunanin sa ya dawo jikin sa irin wannan sai an jigata mutum tunanin sa yake dawowa ƙwaƙwalwar sa ta soma aiki kamar yanda take a dah,take aka fidda mudi saboda manyan-manyan dantsan sa da kafta kaftan yatsunsa mudi ya dage ya ware hannuwan ya kaftawa malam ƙasimu shahararran mari.


    Da mudi da duk wanda ke kusa da malam ƙasimu cinnaka sai da ya jigata duka ta ko ina yake kaiwa duk wanda ya samu yana""


"fari da zamfara yau zan tada firgita..........


   Habu da mudi suka danne malam ƙasimu da ƙyar yana surutai barkatai chan kuma maganar ta ɗauke sai kukan zuci har ya fara fitowa fili,jin kukan malam ƙasimu cinnaka ya tabbatar wa dasu habu hankalin sa ya dawo su mudi da habu suka saushi sai tofa masa miyau suke sana bashi baki cikin kukan malam ƙasimu ya ce"



"Mudi ina Rawani na yake?


Kafin mudi ya magantu ya dubi sarai ta miƙe da sauri ta faɗa ɗakin malam ƙasimu,bata ɗauki lokaci ba ta dawo ɗauke da rawanin a hannu duk ya cukur kuɗe,miƙawa mudi rawanin sarai tayi mudi ya karɓa ya miƙawa malam ƙasimu take malam ƙasimu ya saka ihu haɗe da furta""


"Hakimi dan Allah habu ku kaiwa hakimi kayan sa kuce ni kam na yafe har ga Allah kar ku yadda ya naɗawa kowa a cikin ku dan wallahi hmmm ku tashi ku kai masa,malam ya kuma fashewa da kuka yana sharce majina da hawaye har su mudi sun mike ya sake duban mudi ya ce""



Rawanin hakimi aɗauka akai wa hakimi rawanin sa ne ba nawa ba ni ba ɗan gado bane.



Tofa cikin kowa a wajan ya ɗuru ruwa musamman da su buhari suka shigo gidan suka taru akan mahaifin nasu kowa na tofa albarkacin bakin sa daga ƙarshe dai aka yanke shawarar a ɗauki rawani akaiwa hakimi a shaida masa duk abinda ke wakana ladiyo kam sai ɗaki akayi da ita aka garƙamedan dataga sarai labari zai chanja take zata kife ta baje su mudi suka ɗunguma fadar hakimi da rawanin liman a hannu kamar an ƙwato shi daga bakin kura.


    "Duk yanda abun ya wakana su mudi suka zayyanewa hakimi,shi kansa sai a yau ya iya fitowa fadar ya zauna saboda ƙorafin jamma'ah ya soma yawwa,haka yasa ƴan koran nasa dole fitowa su ma su zauna tare da sharaɗin la'asar nayi kowa zai ɗaye gidan sa dan har gobe basu fasa ganin hoton halittar data ziyarce su cikin idanun su ba,hakimi ya jinjina lamarin haɗe da karɓar rawanin ya naɗawa malam talah daya buƙaci hakan shi da muttaka har ɗauki ba daɗi akayi tsakanin talah da muttaƙa akan rawanin daga ƙarshe dai hakimi ya baiwa talah a take a wajan su mudi suka juya,kamar yanda suka tsara zaman nasu zai watse da la'asar kowa zai tafi hakan kuwa akayi amma sun ɗunguma sunje duba malam ƙasimu da ganinsu dayaga rawanin kan malam talah malam ƙasimu ya fashe da matsanan cin kuka sai ambatar liman liman liman yake yana ta kallon malam talah dake kimkim da rawani akansa har da doguwar addu'ah akan Allah ya bawa malam ƙasimu cinnaka lafiya suka tashi suka baro gidan kowa yayi nashi waje bayan sun maida hakimi ƙofar gidan sa ya shige.








…………………







_*TSANGAYAR MALAM*_



     Tun bayan guduwar su ɗan malam daga tsangaya malam na kan buzu ya ci jinyarsa har Allah ya bashi lafiya garada yasa suka tafi cikin sahara suk ibo masa wata ƙasa da ruwan ƙorama me zurfi abinka da aikin malam take yasa aka zaƙulo masa duk sunayen almajiran da ake kawo masa ajikin wani fatu,kowane ɗalibi da sunan sa da ajami hakan ya bawa malam nakan buzu damar yin aiki akan duk wanda ya fece daga tsangayar malam, kiranye me zafi yayi musu dan har tsidugu ya haɗa cikin safgar aikin ba'afi kwana biyu ba aka dinga tsinto almajirai ɗaya bayan ɗaya ana dawo dasu cikin tsangayar cikin gushewar hankali kaf wa ƴanda suka gudu sai da suka kawo kansu cikin su har da *Sani ƙolo*.

     Bayan duk magudan sun dawo tsangaya malam yasa atara masa su waje ɗaya duk aka bi kowa aka ƙaƙaba masa mari ƙafa da hannu bayan muguwar bulalar da kowa yasha malam ya bada rubutu a ƙoƙo a baiwa kowa ya sha dan hankalin su ya dawo,aiko daga sha kowa tunaninsa ya dawo nan ido yayi tulu tulu musamman sani ƙolo da tunda ya farfaɗo kuka yake yana daya sanin sanin ƙanin mahaifinsa da yayi sanadin kawo shi tsangayar yayi iya dubansa ko zai tozali da ɗan malam sam bai hango shi ba,haka tunanin sa har yanzu bai kawo masa ko bai dawo tsangayar ba ne.


Malam na zaune akan buzun sa na gado ya hallara a filin idanunsa sai hange hange suke dan gano taƙadirin yaron dayayi sanadiyar guntule masa ɗan yatsan sa da yayi,ya ƙudiri aniyar sai ya azabatar dashi dai dai da abinda ya aikata masa amma idanun malam basu hango masa wanda yake da buƙatar gani ba dole sai da yasa akayi wa tarin almajiran ɗaukar ɗaya bayan ɗaya bai tozali da ɗan malam ba hankalin malam ya tashi,ta yaya kowa ya dawo shi bai dawo ba lallai akwai abunda ya sa to ko ma menene zasu zuba dole yaron ya dawo *Tsangayar malam…………………………





_*Bari na barku haka mu haɗu a gaba dan jin ya zata kaya🤔*_






_*Comments/Share*_



_*Comments/Share*_

No comments