Breaking News

TSANGAYAR MALAM 25-26

            2️⃣5️⃣-2️⃣6️⃣

""Ummmm ummm ummm"ɗaga kai ladiyo tayi samma ta hangi malam ƙasimu cinnaka zaune a cikin duruwar kayan sa takure kamar zai dunƙule sai zare ido yake yana gallawa ladiyo harara alamar ta rufe shi ta bar wajan,murya a daƙile ladiyo ta ce da malam ƙasimu"



"ikon Allah yau su malam an shiga sahun burrai,"au dama nan ka haye na nemeka samma ko ƙassa na rasa to Allah ya toni asirin ka baza ta taɓa saɓuwa ba kana samma mu muna ƙassa saukowa zaka yi duk mu taru mu bita wato kai kaɗai kake da buƙatar ranka mu namu ran ko oho bari kaga ikon Allah,nan da nan ladiyo ta warci ƙafar malam ƙasimu ta somo janyo shi ta ƙarfin tsiya tana mitar sai dai dukkan su kaka rakiyar tayi awon gaba da su baza su tafi su bar malam ƙasimu shi kaɗai ba,malam ƙasimu cinnaka yaga babu sarki sai Allah da gaske ladiyo janyo shi zata yi bai san sanda ya sauke ɗayar ƙafar ya kutufi bakin ladiyo da ita ba,ladiyo ta saki ƙafar malam ƙasimu cinnaka tana ihu tana gunji da juya yuyen kai haɗe da talafo bakin nata matsin wani abu ya ɗan taɓa kofar chan kuma ihun sarai ya soma tashi a guje ladiyo ta rarrafa ƙasan gadon malam ƙasimu yaran suka bita gaba ɗaya kowa na kukan ciki dan sun toshe bakunan su gaba ɗaya,daga samma malam ƙasimu ke ta maimaita "La'ilaha'illallahu Muhammadur'rasulullahi,ladiyo tayi charaf da baki ta amshe da,"(S'A'W) shikenan su yaya sarai an rigamu tafiya Allahu Akhubar ,ta saki kuka me tsuma zuciyar me sauraro yaran ma gaba ɗaya suka bare baki ɗakin ya karaɗe da koke koke malam ƙasimu sai kutuntuma musu na maguzawa yake shi kar su falasa shi kaka rakiya tayo ɗakin ta haɗa har dashi ya shiga uku,su ko kamar ƙara musu mai ake har wani dashe baki yaran suke suna wayyo Allah su kaka rakiya ware ware,malam ƙasimu yaga kukan su ladiyo na ƙara bunƙasa atake ya bare bakin sa shima ya soma nashi yana yi yana kalon tagar ɗakin sa dan sun rufe ƙofar da sakata.


Ta windo ya hango wata iri yar halitta me munin gani tafiyar ta kaɗai abun tsoro ce,bare uwa uba jikin halittar da gaba ɗaya gashi ya tsaitsaye ya lilliɓe ta nan da nan fitsari ya ƙwacewa malam ƙasimu idanuwan suka ƙara tulu tulu hawaye na sauka yana sharcewa da hannun sa gaba ɗaya karatun ya gudu chan aka duro cikin ɗakin deffffff,gashin jikin ɗan malam daya tashi ya tsaitsaya da wakeken takalmin ƙafarsa da ladiyo tayi ido huɗu da shi ta tafi luuuuu ta sume tsabar fargabar da ta daki ƙirjin ta ya ran suka ƙara karaɗewa da matsanancin ihu da neman wajan ɓuya har aka samu aka si durowar malam ƙasimu cinnaka ta wangale sai ga rawanin malam da babbar rigarsu duk a hannunsa fuska ta cika da majina da hawaye dawa Allah ya haɗa ɗan malam ai nan da nan ya ɓuɗa.


Cikin murya me amo da dukushewa ɗan malam ya soma wata iri yar lanƙwasa yana banƙarewa haɗe da takawa yana""


     """Fari da zamfara yau zan tada firgita..........


""""""Fari da zan fara ƙasimu zai fidda sanƙama.........



""Fari da zamfara shi zai tadda ɓakuta yaran duk su ɓakuce..........








_*Kuyi haƙuri da ɗan wannan next page insha Allah akwai Read More da yawa*_

No comments