Breaking News

TSANGAYAR MALAM 21-22

              2️⃣1️⃣-2️⃣2️⃣

"Ai kawai abar kaza cikin gashin ta domin kuwa idan akace za'afige ta sam ba kyan gani zatayi ba Attahiru,"hmmmm inna kenan idan ke ba zaki faɗa mun ba bari na fita waje na san bazan rasa me labar ta mun ba,ɗan malam ya juya zai fita cikin saure uwaila ta dakatar dashi haɗe da ɗauko kujerar tsuguno

tazo ta zaune,duban ɗan malam tayi dake tsaye ƙiƙam ta ce"

"zauna na faɗa maka yanda abun ya faru amma kafin nan ina son jin inda malam ƙasimu cinnaka ya kai ka,kuma ta yaya ka ƙwato har ka dawo gida Attahiru?


wani guntun murmushi ɗan malam ya sake ya dubi uwaila ya ce"inna kenan labarin dayawa amma bari abaki shi ataƙai ce,Bismillahir Rahmanir Rahim,ya nemi gefe kusa da uwaila ya zauna har da tanƙwashe ƙafa ya ce"


"Wato inna daga nan garin da ƙasimu cinnaka ya kwashe ni bai tsaya a ko ina ba sai.........."haba Attahiru ba malam ɗin sai sunan sa kai tsaye zaka ambata,uwaila ta dakatar da ɗan malam ta zuba masa duban ta ɗan malam yayi da kyau ya ce"


ko a da ban taɓa kiran sa da malam ba bare yanzu da ya shiga sahun manya-manyan maƙiya na,Allah inna idan na tuna kaina na tuna ba a tsokana ta a zauna lafiya,bare kuma an zungure ni zungurar ma ta rashin mutunci da ƙasimu cinnaka yayi mun sai na ji kamar zuciyata zata buga amma maza bisa kan arna tarkon da na naɗa masa ummmmmm Allah dai ya kai damu ga harawa maza na dawa ko a fagen yaƙi.


sakatau uwaila tayi tana kallon ɗan malam ta rasa bakin magana dan duk abinda ɗan malam ya furta zai yi,tofa sai yayi shi ko za'akar shi lalai malam ƙasimu cikin tsaka me wuya da tarkon Attahiru.



"innaaaaaaaa,'ummm ummm na'am Attahiru cigaba da bani labarin ina jin ka.


to ai naga kin tsunduma cikin kogin tunani ne,idan kin gaji na tashi na wuce safga ta,"ni ban gaji ba ina tausayawa malam ƙasimu cinnaka ne,"taɓ wallahi ba abun tausayi bane mugune inna ba mutumin ƙwarai bane niger fa ya kai ni almajiranta.


Niger.....na shiga uku ni uwaila matar malam.


Wallahi inna niger ɗin ma chan cikin ƙauye Allah inna tsangayar ta kusa ɗan ƙaramun gari kuma duk bukoki ne ɗakunan gashi shi kansa malamin gwanki ne dan asama zaki hangoshi yana rito.


Samma kuma Attahiru ban gane.


bari in miki gwari gwari shi baya samma baya ƙasa haka yake zaune akan wani buzun sa ga wani jabgegen charbin sa da yake ja amajiyar danaji ma cewa akai ƴaƴan charbin sun haura dubu biyar da ɗoriya.


Tashin hankali kuma dukka yake iya jan su.


ai taƙadiri ne babba inna wannan idan ba mugunta zaka koya awajan sa ba banga abinda zaka koyo ba.


amma gaskiya malam ƙasimu sam bai kyauta ba ai ga ƴaƴansa ya kwasa ya kai mana sai ƴaƴan marasa galihu gwara da Allah ya kuɓutar mana da kai Attahiru ba wajan zama bane.


hmmmm inna har mari sai da aka samun wai ni Attahiru.


"Lahaula'walla ƙuwatta,ashe azaba aka yi maka ba kaɗan ba a tsangayar?


ba fa acewa komai inna shi kansa malamin ya magantu yaji a jikin sa bare ƙasimu cinnaka ai bazan taɓa manta *TSANGAYAR MALAM*,ba cikin tarihin rayuwa ta,to bari na ɗan miƙe ƙafa wai ma inna dana shigo ɗazu naji kamar Suwaiba na miki wata magana akan ƙasimu me take faɗa maki?


Rashi yayi babba jiya da daddare kakar sa ɗinan tsohuwa tukuf daya ɗaukota daga ƙauyen su,ai ita ce ta rasu tayi kwanan keso kasan mutumin naka duk rashin mutuncin sa yana tsoron mutuwa bakaji rashin ɗa'ar da yayi ba dan jiya ya kwana da gawar shine yau ya fatattaka jamma'ah har da ƴan uwansa wai ba me zaman makoki a gidan sa.


Alhamdulillah,faɗuwa tazo dai dai da zama,inna sai anjima bari na taka idan malam yadawo ki faɗa masa duk labarin dana baki.


ai kamar yaji ya gama amma daga dawowar ka zaka fita kuma Attahiru kabari kayi wanka kaci abinci ka kwanta ka huce gajiya sai ka fita ni wallahi tsorona Allahi tsorona kar hakimi yasa akuma kama ka a maida kai dan Allah ka dawo ka zauna agida muga yanda za'ayi.


   ashe dai su inna ana ƙauna ta,ɗan malam ya saki dariya,uwaila ma dariyar tayi haɗe da girgiza kai ta ce"



So wanda uwa kewa ƴaƴanta kuwa Attahiru ko zaka fitan ka bari zuwa anjima kaji............sallamar Malam ce ta katse maganar da suke,malam na shigowa gida ganin Attahiru ya saki ledar hannun sa da sauri ya ƙaraso daf da ɗan malam yana"



"Attahiru kai ne?.............


ni ne nan malam Allah ya dawo da mu.



Alhamdulillah Allah na gode maka baka dai ji ciwo ba ko,babu abinda ya same ka ke uwaila maza ɗauko abinci ki kawo ya ci ya sha ruwa,duk malam ya rikirkice ya dabar barce ganin ɗan malam,uwaila ta kada baki tace"



Rigimar da mukeyi yanzu kenan ka shigo ka iske mu malam gaka ga shi dan Allah kasa ya zauna ya ci abinci ya huta.


Ai dolensa ma ke dai ɗauko masa abincin ga ledata chan dana yarda ɗako muga in fita in sayo masa lemo da ruwan ledar.


Cikin abinda bai wuce mintuna ba uwaila ta kirɓowa ɗan malam dafadukar shinkafa taji nama da ganyen alayyahu da albasa malam ya shigo ɗauke da ruwan ledar da lemon roba ya dire su gaban ɗan malam daya baje a ƙasa ya fara kwasar watu chan ya chafki lemon sa ko ruwan bai kallaba ya buɗe ya kaffa kai har sai da yaji ba komai a cikin robar ya sauke ya cigaba da danna abincin sa jifa jifa yana kallon yadda malam ya zuba masa ido yana kallon sa.



   Bayan ɗan malam ya ci ya gimtse cikin sa malam ya sa shi gaba shi da uwaila suka dinga tambayar sa yanayin daya shiga shi kuma yana basu labari daga ƙarshe ya miƙe uwaila ta dafa masa ruwan wanka ya shiga yayi ya fito ko mai bai shafa ba ya ɓingire a ɗakin sa bacci me nauyi ya kwashe shi har ɗakin malam ya leƙa ya sake kallon ɗan malam ya fita da tausayin sa falla aransa,ɗan malam bai farka ba sai da malam ya shiga ya tadashi dan gabatar da sallah magarib,bayan ya idar da sallar uwaila ta kuma kirɓo masa tuwon dawa miyar kuɓewa ɗanye da nama zuƙu zuƙu ya kwasa har da lemon sa da malam ya kuma siyo masa ya shanye har da ƙara ruwa akansu,tsakar gidan ya fito nan ma suka baje hira har kusan goma da rabi na dare yayiwa malam sai da safe da uwaila ya faɗa ɗakin sa,wasu kaya ya fida daga buhu ya sanya da wani abu me kama da gashi gashi ya rufe fuskar sa dashi a sukwane ya fita bayan ya jibga kaya kan shimfiɗar sa kamar mutum ya nufi fadar hakimi dake cike da ƴan kanzagin sa sai raha suke suna ɓaɓɓaka dariya su kaɗai ƙafar mutane duk ta ɗauke.



Daga nesa ya fara lanƙwashewa ya banƙare ƙafar sa da hannayensa dukka, gashin dake jikin sa ya mimiƙe ya tashi ya nufo fadar hakimi yan cila ƙafarsa guda ɗaya sai ta kwashi muntina ya kuma jefa ɗayar kamar wata halittar daban, malam ado ya waiwayo ɓangaran kudu kamar ance ya kalla ya hango abu a banƙare na nufo inda suke ƙwalalo idon sa yayi da kyau ya zubawa halittar ido dake tahowa kamar ya basar ya tashi shi kaɗai ya gudu wata zuciyar ta ayyana masa'kana tafiya kai kaɗai zai fara riƙewa gwamma ka zauna ai kan me uwa jawabi kowa yaci gidan su,malam ado ya fara rarrafan ƴan yara ya nufo tsakiyar fada tsulum yana"" 


"to fa yau sai dai ta Allah ba ta mutum ba,ya ƙara kai idanun sa kan abun dake ƙara matsowa a sukwane sai ajiyar zuciya malam ado yake yana zare zaren ido gaba ɗaya hankalin su ya tattar gunsa malam ɗan tala ya ce"


"Malam ado yau yarinta aka tuna ake gwadawa hakimi yanda abun ya wakana?



ai wannan tafi yarinta sai dai uwar ta to ita ce tala kai dai yau kawai ka kama salati ba sauran lokaci dan kowa tashi zata fishe shi.


Kamar ya kenan malam ado.


Kamar dai wayyo Allah na Aljanin dare.


Kusan gaba ɗaya fadar ce ta karaɗe da ihun garada suka ɗunguma sai soron hakimi daya ke a ƙofar gidan suke zama da ƙyar suka iya saka sakata da kuba bayan gwabje gwamjan da sukayi da junna hakimi kuwa tini ya rarrafe ya shige ɗaki ya banko ƙofar sa har da saka sakata su kuwa suna soro ba wanda ya farga,shiru soron yayi duk sun toshe bakunan su numfashin ma ɗauke shi suke sama sama barin da sukaji motsin halitar ya ƙaraso fadar  cikin kowa ya murɗa suka fara kame kaman addu'a shi ko ɗan malam dama abinda yake so kenan ya tarwatsa su gaba ɗaya ya tattara gaba ɗaya takalmansu ya jide a buhu ya bar wajan da sauri ya komo gida yana ɓaɓɓaka dariya da ƙudurin yin abunda yasa agaban sa.










_*Comments/Share🤗*_

No comments