SHINE SILAH 1-5
🌹☘️🌹☘️🌹☘️🌹☘️
*SHINE* *SILAH*
🌹☘️🌹☘️🌹☘️🌹☘️
NA
*FATEEMAH* *S* *OMAR*
Marubuciyar📝
*DR* *AMEENAH*
*KANWAR* *MATATA*
*AURAN* *JAREEMEE*
*BAKIN* *GIDA*
*KANSHI* *KAWAI* *YA* *SANI*
And now
*SHINE* *SILAH*
Labarin Shine Sila kirkiraren labarine banyishi dan wata ko wani yaji haushi ba
Wadda na 'batawa ya yafemun
Abuda na fada na kuskure Allah ka yafemun
BISMILAHIR RAHAMANUR RAHIM
🅿 1️-5
..........................📖Zaune take a parlour ta 'dora 'kafa daya kan 'daya tana kalon TARKON KAUNA a Arewa24 tanata murmushi dan duk inda Film na Love yake to nan NAJMA tafi kauri dan tana zaune wani sa'ilin saikaga tanata hawaye
phone dinta ce tayi kara taduba taga message ne jikita har rawa yake taduba taga NAJIB ne jikita har rawa yake ta bude ta karanta tana murmushi reply tamishi ta kwanta ta 'dau pilow na kujera ta rungume a jikinta tana murmushi haka har aka gama TARKON KAUNAR 9:00pm ta mik'e tana tafiya kamar bata so taje ta kwanta ta kuna Data tashiga WhatsApp tafara cart da TAURARONTA Najib sunjima suna misayar kalamai da zasu farantawa juna rai kafin yace ta kwanta yamata addu'a ta kashe datar ta rungume phone 'din ajikinta tana ajiyar zuciya tana tunanin Tauraron nata har bacci 'barayo ya dauketa
Washe gari
Bata iya tashi da kanta ba yadda Ummi tasaba ita tazo ta tasheta bayan ta tashine tayi Sallah taje Kitchen ta ha'da musu bearkfast tazubawa Kannenta a lunch box ta ajiye musu a parlour lokacin har sun gama shifinsu sun fito Namijine ya zo gabanta yace "Yaya Najma dan Allah yau kizo ki dakomu daga School in an tashi"
Murmushi Najma tayi tace "insha Allah Annur nizan zo na dakoku" dariya yaron yayi ya duba yaga ba kowa kusa da su murya can kasa yace "karfa kizo ke kadai kizo da ancle Najib dan Allah bazan fad'awa Ummi ba"
Dariya tayi tace "karka damu dashi zamuzo" "promise" "i promise you" ya mana mata kiss a kumatu yace "bye bye'' itama ta daga mishi hannu suka fice
room 'dinta ta koma tayi wanka ta karya ta 'dauko phone takira masoyinta kalemun zuciyarta Najib
Kwance yake akan bed yana rike da wayarsa
black Beauty ne gashi dogo da ganin jikinsa kasan 'dan hutune kuma gana ganinshi irin mazan nane 'yan duniya masu son ayi rayuwar 'karya
murmushi naga yayi ya kara wayar a kunanshi yace "hello my life" murmushi naga yanayi yace "okay badamu idan kinshirya kimun magana saina zo mu 'dakosu" "nima nagode my Wife"
Ajiye wayar yayi yana cije lips 'dinshi a hankali ya furta "akwai lokaci yarinya" yayi wani kaya tacan murmushi ya 'kara gyara kwanciyarsa
5:30pm tafi to sanye da hijab 'dinta har 'kasa ta rataya jaka taje tasamu Ummi a 'daki tace "Ummi zanje 'dako su Annur a School" kalota Ummi tayi tace "dakin bari Nura yaje" "A'a Ummi tunda nariga nashirya kibarni naje kawai" "tom" kawai Ummi tace ta 'dako kudin mota tace Aa tabarshi da kudi a gurinta "to Allah ya kiyaye" "ameen Ummi" tace tana fitowa ta tafi
Tayi tafiyar 'kasa me nisa kafin taji anyi hon a bayanta tsayawa tayi ya 'karaso ya bude mata motar tashiga
yaja motar suka bar gurin
Tunda tashigo motar yake kalota hankalishi gaba 'daya baya kan tuki yana kanta ajiyar zuciya ya sauke yace "my life so nawa dance idai kinsan gurina zakizo ki daina sa wannan hijab 'din" kaita girgiza tace "kaima kasan cewa nayi da Ummi School zanje dako yara taya zanyi kwaliya amma aikasan inzuwa kayi gida tana bari nasa mayafi" ninfashi ya sauke yace "koma mene nan da 4weeks ne anyi angama sai a daina mun katanga dake"
Kai ta dukar kawai batace komai ba yayi murmushi yace "wai kunya kikeji?" kaita girgiza alamar Aa yace "ko yanzu bagya son aure na" "A'a fa nace" kwashewa yayi da dariya yace "ai wallahi aka fasa auran nan saikinyi jinya yarinya" hararar wasa ta watsa masa tace "harda kai ma" "ni ba abunda zanyi kece dai a ruwa" ya 'kara maganar yana 'daga mata gira daidai time 'din da yayi parking a get 'din School din Najma ta fito ta shiga ta fito da Annur da Noor suka shiga bayan motar tashiga gaba suka tafi
a mota Annur yaringa masa hira suna dariya ya dako Sweet yabasu suka amsa suna murna Najma tace su shanye su bata ledar sukayi bayan sun shanye tajefar
a bakin titi ya zubesu Annur suka fito ta bude motar zata fito ya riko hannunta yace "my Wife zaki tafi ba abunda zaki bawa mijinki" murmushi tayi tace "mekake so na baka" ajiyar zuciya yayi yace "alkawari kawai nakeso kimin" "wane iri alkawari?" "kiyimun alkawarin zaki kulamun da kanki kuma idanunki baza su kali kowane 'da namiji ba saini''
Dariya tayi tace "nafarko dai na dauka amma na biyu yayi tsauri" "nikuma na biyun nafi damuwa dashi" kaita girgiza tace "nayi alkawarin bazan Kali wani namiji da sunan soba, shikenan?" dariya yayi yace "wow ina mamakin a akeyi kike karantar abunda kecikin raina" "sabuda abunda yayika shi yayini" "hakane My Life sai na sake ganinki" "to Allah ya kaimunkai gida lafiya" "ameen'' yace tafi to yaja motar saida taga ya kule sannan taja Hannun yaran suka tafi gida
Suna shiga suka tadda Ummi da Yaya Nura a tsakar gida suna hira da gudu yaran suka fada jikinsa suna dariya
zama itama Najma tayi tana murmushi kalonta Yaya Nura yayi yace "jiya meya hanaki bacci naganki har 12 online" ina- ina tafarayi cikin fushi yace "Najma ki kiyayeni karkiga ankusa bikinki kike fito da sabun dabi'u toni bazan lamunta ba shi kanshi Najib 'din yabari a kaiki gidanshi sannan yayi iko dake" shiru tayi Ummi tace "ayi hakuri ke kuma karki kuma" ''to Ummi" mikewa tayi zata shiga 'daki taji Ummi tace "naga yau kunyi saurin dawowa ba wuyar abun hawa kenan?"
Ido ta zaro gumi yana keto mata tana girgiza wa Noor kai da take cewa "A'a Ummi yau Yaya Najma da...............!
Karku manta yanzu muka fara my Fan's kudai ku cigaba da kasancewa dani taku meson farin cikinku
COMMENTS
AND
SHARE
by
*XAHRA*
No comments