Breaking News

SHARUZZAMAN BOOK 1 PAGE 9

 *BOOK ONE* (1)


                       9️⃣

Gimbiya bilkisu na gaba wasu kuyangi biyu na biye da ita cikinsu har da rumana dake riqe da handbag dinta, wurin wata hadaddiyar mota mai numfashi suka qarasa cikin sauri sarkin mota ya bude mata gidan baya ta shige a gadarance ta zauna ya rufe murfin motar, rumana kuwa ta shige gidan gaba, sarkin mota yaja motar suka fice,tfy suke bisa babban kwalta daya ratsa ta galadima road, motar nasu ta tsaya daidai meera beauty saloon, sarkin mota ya fito da

hanzarinsa ya bude mata murfin mota ta fito, cikin tfyr isa da qasaita ta nufi kofar shiga wannan tafkeken saloon da aka rubuta meera beauty saloon a saman wurin, duk inda ta sanya qafa rumana na biye da ita riqe da handbag a hannu har suka shiga wannan k'ayataccen saloon wanda kusan duk wacce ka gani wurin toh shakka babu matar wani hamshaqin ne ko kuma diyan masu mulki da sarauta sbd gsky babu wargi wurin ya gaji da had'uwa, angelina tana ganin shigowar gimbiya bilkisu ta taho da sauri tamkar zata ci tuntu6e tana mata barka da shigowa tuni ta janyo mata kujera ta zauna, rumana kuwa na ra6e a gefe, angelina ta nuna mata wani seat kan ta zauna amma sai taqi zama don tana shakkar abun da hkn ze iya janyo mata wurin gimbiya bilkisu, tana nan tsaye aka soma wankewa uwar dakin nata gashi sannan aka dawo wankin kafa duk kuwa da irin  sulbi da

 taushin kafar babu alamar wani abu waishi datti bare har takai ga wanki amma abunka da isa irin ta diyan girma duk sati sai tazo an wanke mata kafa, cikin wurin very cool don Ac ne ta ko'ina babu harkar qaranta, babu jimawa angelina ta kammala, gimbiya bilkisu ta miqa ma rumana hannu ta sunkuya cike da girmamawa ta bata handbag dinta ta zuge handbag din ta fito da wasu rafa rafan kudi bugun abuja mutum biyu masu daraja ta miqawa angelina ta sunkuya da bala'in sauri ta sanya hannu biyu ta kar6e kudin tana gdy don tasan wannan kudi sun wuce ladan aikinta kawai bajinta aka mata, har bakin mota ta rakasu saida taga tashin motar nasu sannan ta


 koma cikin saloon din ranta qal, su kuwa daga nan Talhal park suka wuce, gimbiya bilkisu ta nufi bakin ruwa ta zauna ta zubawa ruwan tafkin ido tana tunanin batun aurenta da kullum yake cikin kwaryar ranta, sai gab da sallar magriba suka dawo da kaya niqi niqi don sun shiga talhal shopping complex sun yi siyayyar kayan shafe shafe, don ita bata gjy da kashe kudi tamkar bata son su saidai bata ta6a iya daukar kwandala ta baiwa mabukaqaci sbd kyashi ga kuma rainin arziqi, duk irin bauta da hidima da rumana ke mata bata iya daukar abun arziqi wanda za'a iya mora ta bata, motarsu na tsayawa a

 harabar ajiye motoci shima motarshi ta shigo wato yarima ayman, tunkan ya fito daga motar ta bakin glass din motarshi ya kafe fuskar yar buzuwa da idanu, surely, he loves her but quite sure shima yasan akwai matsala,  be ta6a mafarkin zeyi irin wannan matsiyaciyar soyayyar ba wai yau shine ke son baiwa, baiwar ma kurma mara cikakken tushe, shin meye ke faruwa dani ne, tmbyr daya yiwa kansa kenan, fitowa yyi daga cikin motar sanye yake da wani share sharen yadi kaftan kalar milk colour, hannunsa dauke da wani givinci writch watch brown sai daukar idanu yake, takalmin kafarsa flat ne shima givinci brown, gbdy qamshin turarensa ya mamaye ilahirin wurin, dogarawa dake wurin tuni suka soma zabga masa kirari sbd duk wanda yasan  yarima ayman yasan shi da halin kyauta shiyasa yake da tarin masoya ta inda yasha bamban kenan da yar'uwarsa gimbiya bilkisu, ganinta ne yasa yyi kicin kicin da ransa ya wani dauke kai kamar be gansu ba,  itama saita yatsine fuska tayi gaba abinta

 rumana na biye da ita, saida ya tabbatar sun wuce yabi bayansu da kallo cike da basarwa, wucewa yyi shima ya shige manbilah yana shiga ya tarar da amarya a hakimce a dinning table, gabanta cike da soye soye da girke girke, tana shirin buda baki ne don ita mace ce ma'abociyar azumin nafilah musamman azumin litinin da alhamis baya ta6a wuce ta, murmushi yyi yace" barkanki da shan ruwa first love" murmushi tayi tace" barka dai dan rigima yau kuma da wacce kazoh" dariya ya somayi yana sosa qeya yace" wai yaushe aka tsaida bikin diyarki ne"  tashi daya murmushin dake fuskarta ya dauke diff, cike da fada tace" wai me bilkisu ta tsare mk ne, har wani murna kk sbd za'a yiwa yar'uwarka auren dole" murmushi yyi yace" pls ki dena biye mata, nidai nasan mai martaba bazai ta6a mata za6in da be dace da ita ba" watsa masa wata harara tayi tace" shashan banza, wato kai har so kk mu hada jini da baqin jini, meye abun so ga zuri'ar fulanin adamawa wanda mugun hali a gindinsu ya tattare ya qare, kaf

 masarautun dake nahiyar meye dole sai masarautar adamawa,hk kawai nida haihuwa wata da min iko da ya'ya, idan bk sani ba bari na sanar dakai tunda naga kaidai tunaninka ragagge, wannan hadin auren fulani ita tayi ruwa tayi tsaki ta zuga mai martaba sbd wata 6oyayyiyar manufarta wanda ita kadai ta sanshi, kuma wlh bazata ta6a nasara ba mu zuba ni da ita, shege ka fasa" shiru yyi don ba yau ya soma jinta tana irin wadannan furuci ba, ya rasa dalilin wannan qiyayya da take yiwa fulani...




       Rumana kuwa suna shiga yola ta wuce bakin aikinta, abinci ta shiga kitchen ta hada ta jera ta dauka takaiwa gimbiya bilkisu dake dakinta tana bar barje a saman hadadden bed dinta tana chat da friends nata wanda suka gama Cambridge tare, rumana ta tura kofar dakin ta shiga hannunta dauke da wani faranti mai fadi, shigowarta ne yasa ta dago eyes nata tana kallonta sannan ta maida kanta kan wayarta ta cigaba da chat dinta, sunkuyawa rumana tayi a hnkli ta ajiye farantin ta kalleta ta mata mgn da yaren kuramen data saba mata mgn tace" ga abinci" wata uwar tsawa ta daka mata tace" ke don ubanki wai meyesa baki da hnkli ne ko daman duk kurma hk yake ko kuma kece dai hkn sbd buzancin dake tare dake?" duk da ba jin abunda take fada take ba amma ta fahimci masifa take mata don yanayin yadda take mgn kawai ze fahimtar da ita hkn,  alama ta mata da yarensu na kurame tace tayi hkr, mtsss, taja tsaki ta koma ta kwanta ta cigaba da latsa wayarta, ita kuwa ta juya ta fice a sadade,

 washegari, amarya ta yake hukuncin tunkarar mai martaba sarki da jayayya kan batun auren gimbiya bilksu da yariman adamawa, jakadiya ta mata iso ta shiga turakar mai martaba, duk da kwarjini da haiba irin na sarkin zazzau amma hk ta daure ta dauko masa wannan batu, be dakatar da ita ba har saida takai madakata, sannan yace"  wannan shine abunda kkso sanar dani? " shiru tayi kanta a qasa batare data sake furta komai ba, murmushin takaici yyi yace" toh kije na bawa diyar taki sati guda ta gabatarmin da wanda take son aure"  yana fadar hk ya miqe ya shige ciki abinsa, ita kuwa ta miqe cike da farin ciki har da hamdala, ranta qal ta fice daga 6angaren mai martaba, daren ranar ta gana da gimbiya bilkisu ta kuma sanar da ita yadda sukayi da mai martaba sarki, a maimakon taga diyar nata na murna sai kawai taga tayi shiru alamun tayi zurfi cikin tunani, gyaran murya tayi tace" ko da matsala ne?" ajiyar zuciya tayi tace"nikam

 bani da wanda zan iya gabatarwa cikin sati guda" turus amarya tayi tana kallonta tace" yanzu duk cikin manemanki baki da tsayayye wanda a shirye yake, naga dai ga yarima andal dan sarki bauchi ko shima baki son shi ne" fashewa tayi da kuka sosai tace" wlh ni duk bazan iya auren kowa cikinsu ba, idan har kuwa zan iya auren wani cikinsu toh tabbas zan iya auren yariman adamawa" zaro idanu amarya cike da tsoro tace" anyah aljanu basu shafeki ba kuwa?" tace" ina da wanda nk so kuma wlh ni bazan iya auren kowa ba sai shi" tace" toh ki gabatar dashi mana" cikin sanyin murya da yalwar ruwan hawaye suna tsiyaya a saman fuskarta tace" sau daya na taba ganinshi har yau kuma ban san ina zan sake ganin shi ba" miqewa tsaye amarya tayi da mugun sauri cike da tsantsar firgici tana salati da salallami tace" na shiga uku, zance na ya tabbata kenan aljanu

 sune suka aureki suke shirin hanaki aure yooh idan ba hk ba kujimin zancen banza da rashin hnkli fa" tace" wlh da gaske nk ba aljanu ne suka tabani ba" tace" rufan baki sakarya, wato ba aljanu bane tsabar iskanci ne koh, toh tsaya kiji idan har nice na haifeki ina umartarki cikin satin nan ki bawa yarima andal dama ya turo magabatansa" sake fashewa tayi da kuka ta riqo hannunta cikin sauri ta ture mata hannu ta shige ciki tabarta a wurin tana kuka....




      Batayi qasa a guiwa ba dole ta tuntu6i yarima andal kan maganan ya turo magabatansa wurin mai martaba, saidai kash, lkcin har an tsayar da lkcin bikinsa da rufaidah diyar mataimakin gwamnan borno, wannan abu shi ya qara tayar da hnklin amarya musamman da taga sati gudan da martaba ya dibanwa gimbiya ya tasarwa cikewa, shi kuwa mai martaba sarki yana nan yana jiran yaji daga garesu amma shiru ba wata mgn har sati gudan ta cike, ranar amarya ta

 kuma tunkararsa kan ya qara basu lkci, aikuwa taga tsantsar 6acin ransa yadda batayi zato ba,kuma ya tabbatar mata idan har yana raye aure tsakanin yarima sharuzzaman da diyarsa gimbiya bilkisu tamkar an daura saidai ta hadiyi zuciya ta mutu,  hk ta dawo 6angarenta hnklinta a mutukar tashe don iyakar iyaka ta tsani wannan aure, fulani kuwa tunda aka fara wannan batu taja bakinta ta tsuke bata cewa komai sbd gudun fitina, saidai wani lkcin idan taga yadda gimbiya bilkisu ke nuna rawar kai da nuna ita din itace sai kawai tayi murmushi don tasan tabbas gamonsu da yariman adamawa akwai tarihi mai mutukar qayatarwa.....


*Littafi na biyu na kudi ne*

Alkalamin bintu ne....L


No comments