SHARUZZAMAN BOOK 1 PAGE 5
5️⃣
Hawaye ne suka soma kwaranya daga k'wayar idaniyanta batare data furta komai ba ta saki takardar dake hannunta ta fad'i k'asa ita kuwa ta wuce a hnkli ta shige bedroom, innaro kuwa duk jikinta yyi sanyi hk ta tsugunna ta d'auki takarda ta juyata don ba iya karatu tayi ba bare tasan abunda ke rubuce a jiki,saidai jikinta ya bata koma meye ke k'unshe a takardan toh ba alheri bane, bin bayan rumana tayi ta shiga bedroom d'in ta tarar da ita ta zauna a k'asa ta sanya fuskarta a tsakanin cinyoyinta tana wani irin gunjin kuka sai tsuma zuciya, sunkuyawa tayi kusa da ita cike da tausayawa ta dafa bayanta, zumbur tayi ta d'ago da fuskarta ta cire hannunta daga jikinta ta mik'e tabar wurin ta haye gado ta kwanta,
muryar indo mai aiki innaro taji daga parlour yasa ta juya fice daga d'akin da sauri, cike da girmamawa indo ta sanar da ita alhaji nason ganinta a parlournshi, toh, kawai tace mata ta d'auki hijabinta dake saman cushion tabi bayanta, kai tsaye 6angaren alhaji badaru ta wuce,sallama tayi ta shiga ta tarar dashi a hakimce a babban parlournshi,yana zaune a doguwar kujerar daya saba zama,tare yake da wasu mutane su uku duk suna zazzaune a k'asan carpet suna aikin shirya wasu rafa rafar kud'i na y'an dubu dubu a ghana must go, shi kuwa alhaji ya hakimce bisa kujera yana basu umarni, shigowar innaro ne yasa alhaji ya sallamesu suka fita tare da jakar kud'in ita kuma ta nemi wuri ta zauna tana sauraronshi, hannnunta rik'e da wannan takarda, kallonta yyi ya kalli wannan takardan dake rik'e a hannunta yyi wani gajartaccen murmushi yace"basai na miki wani k'arin bayani game da wannan takarda ba domin alamu sun nuna kinsan me ta k'unsa" cikin sauri tace"Aa, ina buk'akar k'arin bayani daga bakinka game da wannan takarda" yace"na saki rumana saki uku!!! shine abunda ke k'unshe cikin wannan takarda dake hannunki" cike da tsantsar kid'ima had'i da rud'ani ta d'ago idanu ta kallonshi tace"daman kaaureta na kwana d'aya ka saketa sbd wata 6oyayyar manufa irin taka shine ka za6i ka maida min da d'iya bazawara" dariya yyi yace" ki nutsu ki saurareni, bana auri rumana bane da niyyar sakinta na aureta ne don ina sonta kuma soyayyar da nk mata ne yasa na saketa don bani son ganin igiyar ajali ta zargeta" ranta a mutuk'ar 6ace tace"tun farko kasan da hk ta aureta ko wani ne ya maka dole, sbd yanzu ka samu abunda kk buk'ata shine ka saketa" ta k'arasa mgnr tare da fashewa da kuka yace" ki adana wannan zancen sai zuwa gaba, ko ta6a d'iyarki banyi ba don dana kusance data ta jima da zama tarihi don hk na za6i na saketa saidai bana saketa bane a matsayin na rabu da ita, aa, zan cigaba da rayuwa da ita tamkar ina aurenta tare da sauke mata duk wani hakki da miji ke saukewa matarsa hkm itama zata cigaba da kasancewa dani tamkar mijinta har ma ta haifamin y'ay'a,a idanun duniya ina son mu kasance tamkar da igiyar aure a tsakaninmu shiyasa nkson wannan sakin da nayi mata ya zamto sirri a tsakaninmu" har ya rufe baki kawai kallonshi tare da tsantsar tsoro, fargaba da kuma rud'ani game da furucinsa tace" kana nufin zaka cigaba da zama da rumana bisa tafarkin *ZINA*
har ma ta haifa mk shegun y'ay'a wannan itace manufarka shiyasa ka saketa" murmushi yyi yace"madallah, da wannan kyakykyawar fahimta naki"ranta yyi masifar 6aci tace" idan har ka shirya aikata wannan mummunan zunubi toh ina tabbatar mk da cewa saidai da wata amma badai da rumana" yace" gujewa buk'ata ta daidai ko mini gardama, daidai yake da rasa rayuwar y'arki kije ki k'ara tunani" yana gama fad'a mata hk ya mik'e tare da d'aukar takardan nan dake yashe gefe guda ya yagata gutsi gutsi ya watsar ya wuce ya soma hawa matattakalar bene sai kuma ya waigo ya kalleta yace" ki tabbatar kin adana wannan babban sirri dake tsakaninmu amma hkn gargad'i ne ba shawara ba" hayewa saman nasa yyi yabarta a wuri guda tamkar an dasata, dak'yar ta iya motsawa ta mik'e ta soma jan k'afarta ta fice daga parlourn, jiri na d'ibanta hk ta samu ta k'arasa ta shige 6angarensu tana shiga ta zube bisa tiles tana fitar da
numfashi sama sama tana hawaye, rumana dake tsaye wurin dinning area ta k'ureta da idanu da gudu ta nufo wurinta ta rik'eta ta rumgumeta a jikinta tana mata alama kan mene ya faru, rik'e hannunta tayi ta dafa sosai ta zauna daidai, lkcin tana son sanar da rumana wasu abubuwa daya kamata ta sani saidai ta rasa ta yacce zata fara gashi rumana ba mgn take ji ba, alamar ta soma mata da hannu da ido cikin yarensu na kurame, ita kuwa rumana tana kallonta idanunta na fidda ruwan k'walla, zuciyarta fal take da tausayin mahaifiyar tata, tari ne ya sark'e innaro ba gaggautawa, mik'ewa tayi da sauri ta bud'e fridge ta d'auki ruwa ta tsiyaya a cup ta kawo mata ta amsa tasha kadan, dayake tana da hawan jini wannan abu kuma daya faru yasa jinin nata ya k'ara hawa sosai, kamo hannun rumana tayi ta rik'e gam sai motsa baki take tana son mgn amma ta kasa, hkn da rumana ta gani ne yasa ta fita da gudu aikuwa tayi sa'ar ganin mustapha yana k'okarin fita da mota ta nufi wurinshi da sauri tana hakki ta sanar dashi innaro ba lfy, bin bayanta yyi suka nufi 6angaren nasu yaga halin da innaro ke ciki, saurin daga waya yyi ya sanar da alhaji badaru abunda ke faruwa, umarni ya bashi kan ya kira likita yazo ya dubata, yace"ranka ya dad'e kamar jikin nata yyi tsauri sosai da buk'atar a wuce da ita asibiti....
" bekai ga k'arasa mgnr nashi ba yaji ya daka masa wata gigitacciyar tsawa yace" nace ka kira likita ya dubata a gida" batare daya jira wata mgn ba yyi hanging call d'in, rumana kuwa ta k'ureshi da idanu tana son taji abunda alhaji ya fad'a, yanayin fuskarsa kawai ya bata amsa, kallon yyi yace" alhaji yace na kira likita ya dubata" shiru tayi sai kuma tace"amma da mun wuce da ita asibiti kawai" yace" toh kije ki same shi kozai amince da hkn" shiru tayi tana tunani shiko mustapha ya d'aga waya ya kira likita yazo ya duba innaro, jimawa kadan Dr.samir ya shigo d'auke da briefcase d'insa, yanayin kawai daya ga innaro ciki tunkan ya dubata yace"gsky da buk'atar a wuce da ita asibiti heart attack ta samu" kiran alhaji yyi dakansa ya sanar dashi matsala, yace'shikenan a wuce da ita asibitin amma kar rumana ta bisu" fita da innaro sukayi suka sanyata cikin mota, rumana na biye dasu tana kuka tana k'okarin shigewa mota, mustapha ya dakatar da ita yace"kiyi hkr ki zauna a gida, alhaji yace kar mu tafi dake" yanayin yadda yake da hannu yasa ta fahimci basu son tfy da ita ne, kuka ta fashe musu dashi ta nace dole sai ta bisu, mustapha ya nuna mata idan bata hkr ba komai ze iya faruwa da innanta, hknne yasa taja da baya, bintalo da indo sune suka shige motar mustapha yaja maigadi ya bud'e musu gate suka fice, motar Dr.salim na biye dasu a baya, suna k'arasawa hospital d'in aka fito da innaro da niyyar wucewa da ita ciki, saidai tuni nurses da likitocin da suka taho amsarta sukayi turus, Dr.salim da sai lkcin ya shigo hospital d'in ya k'araso wurin, shima yana ta6ata ya soma girgiza kai, mustapha yace"mene ya faru
likita" yace"saidai hkr kawai domin ta rigamu gidan gsky,Allah ya amshi abinsa, sudden heart attack ta samu" indo da bintalo dake gefe suka soma fidda hawaye cike da tausayi da kuma jimami, rumana kawai suke hange, innaro tamkar jigo take a rayuwar rumana gashi wanda yafimu sonta ya amsheta, hk suka dawo gida cike da tashin hnkli, lkcin da wannan lbri ya tadda rumana sumewa ta din gayi ta zama tamkar mahaukaciya, tayi kuka, tayi kuka kamar ranta ze fita, kwanan innaro bakwai da rasuwa, tfyr gaggauwa ta samu alhaji badaru zuwa germany, tuni yasa aka yiwa rumana visa su wuce tare da ita, rumana kuwa tunda innaro ta rasu ita kadai take kwana a 6angarensu neman hanyar gudu kawai take saidai ko'ina akwai tsaro, securities dake tsaron gate basu ta6a barinta ta fita batare da izinin alhaji ba, yau da dare, bayan ta tabbatar babu kowa a compound d'in gidan ta lek'o wurin ajiye motoci ta hangi motar mustapha ta tabbatar yana gdn be tafi ba kuma tasan zuwa anjima ze fito ya fice da motarsa hkn yasa ta lalla6a ta cikin flowers ta shige parking space taja murfin motar a hnkli tajita a bud'e ba key hkn yasa ta shige cikin motar da sauri ta rufe, tana shiga ta fad'a booth d'in motar ta ciki tayi lamo tamkar ba mutum, mustapha kuwa ya jima be fito ba dg 6angaren alhaji har ta fara tsoron kar dai yau anan gidan ze kwana, wurin sha biyu sai gashi batare da tunanin komai ba ya bud'e motar ya shige ya mata key, securities suka bud'e masa gate ya fice, shi mustapha yana zaune ne shida iyalinsa a k'ofar rigasa, gidansa d'an k'arami ne,mota d'aya ce zata iya shiga, a kofar gdn nasa yyi parking d'in motar ya shi
ga cikin gd ya bud'e y'ar gate d'in gdn sannan ya dawo ya kuma shigewa mota ya shige ciki yyi parking, bud'e motar ya sakeyi ya fice yaje ya rufe gate yasa saka sakata sannan ya shige cikin gida, saida
tabbatar ya shige ciki sannan ta bud'e booth a hnkli ta fito ta wuce wurin k'ofa ta zare sakata ta fice, tana fita taga gari shiru babu kowa sai haushin karnuka, sai kuma motsin y'an vigilante dake kai kawo suna tsaron unguwa, gudun kar su ganta yasa ta shige wata lambatu mara ruwa ta take ta tfy ciki har
tazo wani gd ta hango soronsu ta fito daga wannan lambatu ta shige soron gd dayake babba ne, samarin gdn na gama, tana ganin shigowar wani saurayi yana shiga ya rufe gdn,soron da duhu sam be lura da akwai mutum ba ya bud'e d'akinsa dake soron ya shige abinshi, asubar fari,ta fice daga soron wannan gida ta samu tabar wuraren unguwar.......
Hk har gari ya soma hasken lkcin kuma ta fad'a wurin masallacin sarki tabar kofar rigasa, gefen masallaci akwai almajirai irin tsofaffin nan suna zama suna fara musamman ranar juma'a, gefensu ta nema ta zauna, wata tsohuwar almajira dake gefenta ta juyo tana kallonta tace"y'an mata lfyrki lau kuwa" rumana kallonta tayi batare da tasan abunda take fad'a, fuskanta sukayi rumana kurma ce bata mgn, saurin iya dudu tayi ta mik'e ta rik'o hannun rumana tayi gefe da ita, tace" y'an mata duk da ban sanki ba amma bazan ta6a barinki ki fada har bara ba, kina dakyau sosai komai ze iya faruwa dake, sake jan hannun rumana tayi suka soma tfy, ita kuwa rumana na biye da matar, hanyar gdn sarkin suka nufa suna shiga wannan gdn iya dudu sai gaisawa take da jama'a alamun sun nuna ita d'in sananniya ga hadiman gdn, hk suka din ga k'etare manyan soraye har suka shiga 6angaren bayi, hannnun wata
tsohuwa iya dudu ta rik'o suka ja gefe suna mgn cikin sirri tana nuna mata inda rumana take, kallon rumana tayi sosai sannan ta kalli iya dudu tace"anya kuwa zan d'auki yarinya ban san daga inda take ba na sanyata cikin jerin bayi" iya dudu ta marairaice murya tace" ki taimaka mata jakadiya, idan muka kyaleta bamu san kuma ina zata fada ba kin ganta dai dakyau kamar diyar aljanu" jakadiya tace"toh koma dai aljannar ce?" iya dudu tace"ah haba, wanne mutum" dakyar jakadiya ta amshi rumana bisa yarjejeniyar kome ya faru toh iya dudu zata dauki nauyi, iya dudu ta amince da hkn.......
Alkalamin Bintu Ne....
No comments