SHARUZZAMAN BOOK 1 PAGE 16
*BOOK ONE*(1)
Adda shatu na fitowa daga 6angaren fulani innoh taga rumana a raku6e tamkar wata marainiyya, tausayinta taji sosai tasa hannu ta riqo hannunta tana mata murmushi batare data furta mata komai ba don tasan ba jin mgn take ba don hk ta ja hannunta suka nufi 6angaren baturiya, suna shiga suka tadda falon cike maqil da yayyin yarima suna maida zance kan abunda ya faru d'azu tamkar fad'a fad'a hk suke mgnr, ganin shigowar adda shatu da rumana ne yasa sukayi shiru amma kusan dukkaninsu da
mugun kallo suke bin rumana domin suna ganin tamkar zubar mutuncin wannan gida ne wai yariman adamawa shine da auren baiwa kuma kurma, adda shatu bata tanka musu ba ta wuce da rumana wani d'aki ta zaunar da ita sannan ta fito ta kira wata baiwa mai suna lawiza tace" ki shiga ki gyara gimbiya ki sauya komai tattare da ita ki maida shi mai kyau" cike da nuna girmamawa ta amsa umarnin adda shatu ta miqe daga durquson da tayi ta shige d'akin, qarewa rumana kallo tayi tasa hannu ta cire d'ankwalin kanta nan ne kuma tasha mamaki yadda taga wasu dogayen kalba an tufkesu wuri guda tana warwaresu tace" masha'Allah!" don gashin ne ya sakko har tsakiyar gadon bayanta gashi mai santsi da cika baqi qirin, bayan ta gama ware kalbar ne tasa wani babban comb ta soma taje mata gashin yana qara tsayi sosai har kusan duwawunta, lawiza tace" ikon Allah, ashe har yanzu akwai mata masu tsawon gashi irin hk" ita dai rumana tana daga zaune ba jinta take ba,bayan ta gama ne taja hannunta suka shige bathroom inda ta soma sanya sinadaran wankin gashi kala kala tana wanke mata gashin dashi yyi qal, sannan ta fara wanke mata k'afa da sinadarai masu sanya sul6in k'afa, daga kuma ta cika ruwan wanka ta sanya masa sinadaran wanka ta mata alama ta shiga tayi wanka sannan ta fita ta rufo mata kofar,rumana ta tsaya tayi wanka sosai don qamshin da ruwan wankan ke fitarwa yyi mata dad'i sosai, tana fitowa daga wankan lawiza ta sanya hand dryer ta soma drying gashin nata sannan ta shafeshi da mayukan gashi, daga ta shafe mata jiki da body cream masu kyau da tsada, abunku da jinin buzayen usul tuni tsantsar kyawunta da farar fatar jikinta suka soma shek'i, gashi tubarkallah ba'a iya tsawon gashi da kyau ko kuma hasken fata ta tsaya ba, aa, tana da zubin jiki mai kyau irin wanda turawa ke kira hourglass fiqure, tana da siririn waist da hips masu fad'i ga kuma manyan tsayayyun boosts nan na welcome, manyan bom bom nata kuma suna bye bye, lawiza sake baki kawai tayi tana qarema surar jikin wannan yar kurma kallo, tabbas ikon Allah dayawa yake, idan ya haneka wani abun sai kuma ya baka wani abun, adda shatu ce ta shigo d'akin turus kawai tayi tana kallon rumana ga gashin nan nata ya baje a tsakiyar gadon bayanta sai sheqi yake da d'aukar idanu, cikin sarqewar murya tace"tubarkallah masha'Allah ! tubarkallah!!" qaramin akwatin dake hannunta ta dire a saman bed d'in ta bud'e ta fito da wani rantsatstsen leshi ja mai adon golden an masa dilkin riga da skirt, tace" kina da girman hips Allah yasa wannan skirt d'in ya miki" undies ta fara miqa mata ta sanya sannan ta bata kayan ta saka, duk da kunyarsu da take amma hk ta daure ta saka, skirt d'in yyi mata charass tamkar saida aka gwadata kafin a d'inka, saidai fa yyi masifar tona asirin manyan hips d'inta, rigar ta sanya itace ma bata kamata sosai ba, adda shatu dakanta ta fesheta da turare masu asirtaccen qamshi, lawiza ta d'auki wani qaton band ta tufke mata dogon gashin kanta sannan ta murza mata d'aurin d'ankwali, gashin nata yad'an leqo ta qasan d'ankwalin, powder kawai adda shatu ta sanya lawiza ta shafa mata a beautiful face nata sannan ta sanya mata pinck lip gloss a lips nata, su kansu da suke mata tsayawa sukayi suna kallonta, babu wanda ze kalleta yayi zaton kurma ce, wasu awarwarayen golds adda shatu ta sanya mata sannan ta yafa mata qaton mayafi sai tashin qamshi take, riqe hannunta tayi suka fita falo inda suka taras falon ya kuma cika da ahlin gidan suna ta gutsiri zomar zance d'aya don bala'i, fitowarsu ce ta sanya falon yyi difff! tamkar mutuwa ta qetara, gbdy babu wacce suka zubawa idanu sai yar buzuwa, kyawunta ne kawai yake dalle musu idanu, yaron fulani habiba mai suna junior ya taho da gudu yana riqe mata hannu yace" woow! mum look at this beautiful aunty, i like her" dariya wasu sukayi cikinsu wasu kuma saidai kawai kallo, cikin d'akin baturiya adda shatu ta shiga da rumana, suna shiga suka taddata tana karatun wani littafin addu'oi, d'ago dakanta tayi ta kalli rumana, cikin sauri rumana ta durqusa a gabanta ta sunkuyar dakanta qasa don hkn ita shine alamar gaisuwanta, kad'a mata kai baturiya tayi alamar ta amsa gaisuwanta, sannan ta maida kanta ta cigaba da duba littafin dake hannunta, adda shatu ta kalli baturiya tace" nenah d'iyarki na neman albarkarki gata nan gabanki" shiru tayi bata tanka ba kuma bata kuma d'agowa ta kalli rumana ba, murmushi adda shatu tayi tace" nenah wannan abu ya riga daya faru kuma yarima dakansa ya nuna yana son auren yarinyar nan, kamata yyi mu rumgumi qaddara don tunda hk ta kasance daman Allah ya qaddara matarsa ce, ki d'aure ki sanya mata albarka" bata tanka musu ba ta miqe tabar musu d'akin don ita har yanzu zuciyarta bata gamsu da auren wannan kurmar baiwa da yarima yyi ba a matsayin matarsa shiyasa ba zata ta6a kar6arta a matsayin suruka ba, ita kanta adda shatu taji kunyar abunda baturiya tayi shiyasa jikinta yyi sanyi ta kalli rumana dakanta ke sunkuye tana son mata mgn amma ba dama don tasan bata jin mgn, takarda ta d'auka da biro tayi rubutu kamar hk' rumana jiya mai martaba lamid'on adamawa ya d'aura aurenki da yarima wanda dayawa cikin ahlin wannan gida basu maraba da wannan aure shiyasa zaki fuskanci tarin qalubale, dftn zakiyi hkr har lkcin da ahlin wannan gida zasu amshi qaddarar aurenki da yarima yyi' tana gama rubutun ta miqa mata farar takardan ta karanta, shiru rumana tayi cike da tarin tunani musamman kan rayuwarta, shekarun baya tabbas irin wannan aure na rashin sani aka mata tsakaninta da alhaji badaru yanzu kuma ga wata
sabuwa wai ita d'in dai itace ta auri mijin gimbiya yariman adamawa wanda ko cikin mafarki yarima ba tsaran aurenta bane, saraki ai sai sarauniya, lalle wannan qaddara data had'ata auren mijin gimbiya bata yiwa rayuwarta adalci ba, shikenan ita hk rayuwarta zata qare ana mata kutse sbd tana kurma, hawaye ne masu zafi suka soma sakkowa daga idaniyanta, adda shatu ta dafa kafad'arta tana girgizata alamun rarrashi ta miqa mata tissue ta goge hawayen nata sannan tajata suka fice, suka tarar falon babu kowa duk sun watse hkn yasa ta nufi 6angaren mai babban d'aki wato yagwalgwal tana riqe da hannun rumana, suna shiga suka tadda wata baiwa na dama mata fura, kallon adda shatu yagwalgwal tayi tace" shatu ina kk samo wannan d'iya mai kyau" dariya adda shatu tayi tace" itace amaryar jikanki" murmushi yagwalgwal tayi tace" masha'Allah lalle wannan jika nawa ya iya za6en mai kyau" gbdy sukayi dariya, rumana kuwa kanta na qasa tana durqushe, hannu yagwalgwal tasa ta d'ago da ita tace" Allah yyi muku albarka kin ji mai kyau, ki haifawa jikana yara masu kyau irinki" dariya adda shatu tayi tace" lalle kam wannan tsohuwa burinki dayawa yake" dariya yagwalgwal tayi duk mgnr da suke cikin fillanci suke don ita yagwalgwal ma bata iya hausa ba, kallon rumana tayi tace" kiyi hkr da halin wannan jikana nawa don bashi da kirki ko kad'an, tsiyatakunsa yawa garesu" adda shatu tace" kin dage sai mgn kk ita kuwa wacce kk yiwa zancen ba jinki take ba" murmushi yagwalgwal tayi tana watsa goronta tace" wataran kunnenta ze bud'e zata jini da yardar Allah" fura tasa aka dama mata aka kawo gabanta aka ajiye, alama adda shatu ta mata da hannu kan ta d'auki furan tasha don tasan halin
yagwalgwal ta tsani ta bawa mutum abu yaqi ci, tuni ranta yake 6aci, tana kallon rumana ta d'auki furan ta fara sha, wani dad'i taji sosai tace"masha'Allah, Allah yyi miki Albarka" adda shatu tace" ameen" yini sukayi a 6angaren yagwalgwal daga nan adda shatu ta yiwa amarya rumana rakiya 6angarenta bisa umarnin mai martaba lamid'o, dayake abu ne na gidan kud'i a ranar akayi ordern dubai furnitures na ubansu aka sanya mata a 6angaren da mai martaba sarki ya bata, dayake gidan nada mutuk'ar girma, sun sanya 6angaren yarima a tsakiya, 6angaren gimbiya bilkisu na dama ita nata yana haggu, hk aka sanya mata bayi masu mata hidima.......
Yarima kuwa shi cikin duniyarsa ma ya mance shaf wai matansa biyu, dayake babban architecture ne yana da babban construction company nasa mai suna Nelda Construction Company, yana zaune a office nasa yana busy akan aikin zana wata babbar gada da za'a gina a tsakiyar birnin abuja mai suna tripple square fly over, aiki ne na hamshaqan biliyoyi, yarima haydar ne ya shigo cikin office bayan ya fito daga wani meeting da suka shiga tare da shareholders na jullius barger, kallon yarima yyi yace" sha kuruminka mijin mata biyu" ko d'agowa ya kallesa beyi ba ya cigaba da abunda yake, yarima haydar ya wuce ya murd'a na'urar coffee ya cika wani small mug nasa da black coffee ya koma gefe ya zauna bisa wata lumtsatstsiyar leather seat yana sipping black coffee nasa yana dariyar shaqiyanci, shi kuwa gogan yana gama abunda yak ya dire file d'in ya miqe ya fice abinsa ya kyaleshi, yana fitowa sarkin mota ya bud'e masa mota ya shige ya shiga yaja suka nufi gida, 6angaren gimbiya bilkisu kuwa sai safa da marwa take ita kad'ai a tsakiyar bedroom d'inta ta kasa zaune ta kasa tsaye wai taya ya ma zata had'a kishi da baiwarta, wlh da badan tana tsananin son yarima sharuzzaman ba da ta jima da komawa
masarautarsu sbd wannan shararren wulaqanci da cin mutunci da yarima ya antaya mata, kawai so take tayi tozali da yar buzuwa ta shaqeta ta mutu har lahira, shegiya munafika, abunda ta fada kenan a fili, wayarta ce tayi ringing ta nufi wurin wayar ta d'auka, sunan hajja amarya ta gani 6aro 6aro a jikin screen d'in wayar, cikin sauri har hannunta na rawa ta d'auki wayar, muryar amarya taji cike tsantsar tashin hnkli tace" ina son duk yadda zakiyi ki tabbatar kin 6atar da tarihin wannan baiwar taki domin dalilin wannan baiwar d'an'uwanki na neman hallaka kanshi jiya ya dawo qasar nan cike da tashin hnkli ya nufi wurin mai martaba wai yana son ya aura masa wannan kurman baiwa idan ba hk ba rayuwarshi zata iya shiga garari, ni kuwa ko mutuwa zeyi wlh bazan ta6a amincewa ya auri qasqantacciyar baiwa ba kuma ma kurma tamkar matan aure sun qare, shiyasa nake umartarki ki hanzarta shafe tarihin
wannan yarinya don annob......" kukan da gimbiya ta fashe dashi ne ya dakatar da ita daga qarasa furucinta tace" kukan me kkyi ke kuma?" cikin kuka tace" mum rayuwata na cikin bala'i mum zuciyata zata iya bugawa, tabbas wannan kurman baiwa annoba ce, ko kinsan yanzu kai d'aya nk da ita cikin gidan aurena" cike da rashin fahimta amarya tace" me kk nufi?" sake fashewa da kuka tayi tace" yanzu matsayin kishiyata take, ta auren miji mum! ta auren miji!...." ta qarasa zance kuka yaci qarfinta, ita kuwa amarya wayar ce ta subuce a hannunta sbd tsananin razana da tayi da jin kalmomin dake fita daga bakin gimbiya, This is unbelievable......no! no!! may be i heard it wrong...abunda take fad'i kenan tana girgixa kanta cike da tsantsar tashin hnkli, meye ke faruwa ne...yarima ayman ya haukace musu kan dole sai an dawo masa da rumana kuma ya aureta, can kuma taje ta aurewa d'iyarta miji......da karfi ta furta wlh wannan duk cikin makircin fulani ne kinyi da yar halak.....fita tayi da sauri tamkar zararriya........
Yarima ayman kuwa ya hau kan hanya ya nufi garin adamawa, don ya rantse sai yarima ya sakar masa mata, kuji qarfin hali irin wannan......hmm, lalle akwai sauran zance cikin wannan sarqaqqen labari.......
*Littafi na biyu na kud'i
Alkalamin Bintu ne......
No comments