Breaking News

SHARUZZAMAN BOOK 1 PAGE 15

 *BOOK ONE*(1)

                     1️⃣5️⃣

Fulani habiba ta kallesu tace"tabbas akwai lauje cikin nad'i a wannan al'amari baku ganin ita wannan d'in kamar kurma ce ma" adda shatu ta sake kallon rumana tana son sake tabbatar da zancen fulani habiba, ajiyar zuciya tayi tace" dole sai mun dangana da zuwa wurin mai martaba don  na kasa gane me hkn ke nufi" surutansu ne ya farkar da gimbiya bilkisu daga daddad'an baccinta, zumbur tayi ta miqe zaune gabanta na fad'uwa musamman da tayi tozali da yar buzuwa tare da wad'annan manyan mata

tasan shakka babu asirinta ya tonu, adda shatu ce ta tako a hnkli ta matso wurinta ta zauna a bakin gado tana kallonta sannan ta nuna mata inda rumana take tace"wace ce wancan kin santa?" d'aga musu kai tayi alamar eh ta santa, tace" tana d'aya daga cikin kuyangi na" adda shatu tace" toh meye yakaita 6angaren magajin gida matsayinta na baiwa sannan meye ya had'ata da sanya kayanki don tabbas wannan kayan shine a jikinki lkcin dana miki rakiya d'akin mijinki" fashewa tayi da kuka tace" wlh nima ban sani ba kuma bani kk kai d'akin yarima ba domin ina fitowa daga wanka na umarceta ta kawo min abun sha toh tunda ta kawo min wannan abun sha ban kuma sanin inda kaina yake ba sai yanzu da hayaniyarku ta farkar dani" gbdy dukkaninsu sun kasa kwakwkwaran motsi sbd tsananin mamaki domin duk sun yadda da furucin gimbiya bilkisu, adda shatu kan tana cike da kokwanto domin tabbas ita tazo d'aukar amarya kuma bata ga kowa a d'akin ba bayan gimbiya bilkisu, ita kuwa fulani habiba ranta yyi masifar 6aci batare da wani tunani ba ta sake kwashe rumana da mari tana kallonta a zafafe tace"na rantse da Allah sai kin biya abunda kk aikata da rayuwarki" adda shatu tayi saurin dakatar da fulani habiba tace" ki dakata habiba, mubar wannan mgn sai zuwa safe don akwai buk'atar cikakken nazari kan wannan al'amari,ita wannan baiwa fa kurma ce" juyawa sukayi duk suka fice, adda shatu ta kira babban dogarin dake kula da d'akin tsare masu laifi tace"  ka tafi da wannan baiwa d'akin tsaro sai zuwa safiya ka taho da ita fadar mai martaba" cike da ladabi yace" an gama ranki ya dad'e" kai tsaye aka wuce da rumana zuwa wannan wuri, ranar zuciyar kowa cike take da tunani har garin Allah ya waye, ita kuwa gimbiya bilkisu ko runtsawa kasayi tayi tana cike da tunanin abunda ze iya kasance, su kuwa yayyin yarima cike zuciyoyinsu take da tsoro da fargaba domin suna ganin kamar yarima ya ta6a wannan baiwa sbd ganin da sukayi tana d'ingishi, basu sanar da yagwalgwal abunda ke faruwa ba hatta baturiya bata san abunda ya faru ba sai washegari da mai martaba lamid'o ya kira taron gaggawa, babban falon mai lamid'o cike yake da iyalan wannan gida, dayake daman wadanda ma ba'a qasar suke ba duk bikin yarima ya sanya sun zo shiyasa suka cika wurin tam, mutum d'aya ne baya nan wato yarima wanda babu wanda yasan ina ya shiga, gimbiya bilkisu da rumana sun bayyana gaban wannan alhali, rumana kam kuka take sosai, adda shatu ita ta sake bayyana abunda ya faru daren jiya sannan lamid'o yyima gimbiya umarni ta fad'a abunda ta fadawa su fulani jiya, sunkuyar dakanta qasa tayi da sauri  don wannan alhali sun mata kwarjini, shiru tayi ta kasa furta komai, mai martaba lamid'o na shirin mgn kenan yarima sharuzzaman ya shigo cikin falon, fuskarsa murtuk tamkar besan wata aba wai ita dariya ba, sanye yake da wani yadi yyi kyau sosai, gbdy idon kowa ya koma kansa har ya nemi wuri ya zauna, ita kuwa gimbiya har yanzu kanta na qasa ta kaa d'agowa ta kalli kowa, lamid'o ya kalleshi yace" meye ya faru jiya ka fita cikin dare kabar iyalinka " d'ago da idanunsa yyi ya kalli lamid'o yace" na saketa saki d'aya abunda nazo na sanar daku kenan" gbdy yayyinshi dake  falon suka mik'e tsaye suna kallonsa cike da firgici a fuskokinsu, yagwalgwal kuwa salati ta somayi da sallallami, adda shatu tasha gabansa da sauri tace" magaji kana hauka ne meke faruwa da hankalinka, lamid'o zaka watsawa qasa a idon duniya" murmushi fulani innoh tayi tace" idan an fad'a yaro nada ta6in hnkli ku soma qaryatawa yau dai gashi ya tabbatar da hkn gaban kowa" gimbiya bilkisu kuwa wani dad'i ne ya ziyarci zuciyarsa lkcin da taji ya furta mata kalmar saki hkn yasa ta d'ago dakanta ta kalleshi, aikuwa wata uwar zabura tayi cike da tsantsar tashin hnkli tana goge idanunta don ta tabbatar ba gixo suke mata ba, tuni tayi saurin durqushewa gabansa ta fashe da kuka tace" wlh na tuba ka gafarceni duk cikin rashin sani ne, na tuba" saita kuma da fashewa da kuka tana qoqarin riqe masa hannu, gbdy furucinta ne ya d'aurewa kowa kai duk suka zuba mata idanu, shima kanshi yarima kallonta yake cike da d'aurewar kai, wata muguwar tsawa ya daka mata yace" wace ce keh?"  tace" nice matarka wacce ka aura wacce baiwata ce" ta nuna masa rumana dake can gefe a takure, kowa cikin wurin kansa ya d'aure, waziri yace" kowa ya nemi wuri ya zauna" kowa ya koma wurin zamansa cike da rud'ani, waziri ya kalli gimbiya bilkisu yace" ki sanar damu abunda ke faruwa" durqusawa tayi a gaban lamid'o ta soma musu bayanin abinda ya faru tiryan tiryan, yagwalgwal ta doka salati tace" toh bari kijih na fad'a miki wlh yariman adamawa sharuzzamanu yafi qarfin wulaqancinki kuma zamanki dashi ya qare daga yau tunda har izqilancinki yakai hk ke ba d'iyar arziki bace, sam baki chanchanci shigowa cikin alhalinmu ba" miqewa tayi a fusace ranta a mugun 6ace ta fice, falon yyi shiru kowa yana auna girman wannan kuskuren da gimbiya bilkisu ta tafka, gyaran murya lamid'o yyi ya kalli gimbiya bilkisu yace" d'iyata tabbas kin aikata mummunan kuskure ga mijinki ki nemi afuwarsa bisa wannan abu da kk aikata masa"miqewad tayi ta nufi wurin dayake zaune ta durqusa bisa guiwowinta tana kuka tace" don girman Allah kamin afuwa ka gafarceni bisa wannan kuskuren  dana aikata gareka, na tuba"  shiru tayi kanta a qasa tana kuka, shi kuwa yarima har yanzu be dena jinjina wannan cikakken wulaqanci da gimbiya bilkisu ta aikata masa ba, tunani kawai yake ta yadda ze rama, lamid'o ya kalli yarima yace"ina so ka gafartawa matarka ka maida igiyar aurenka akanta" yace" na maida ita" murmushi lamid'o yyi, yarima yace" ranka ya dad'e ina neman wata alfarma ina son auren wacce baiwar ta kasance mace ta biyu gareni" rass! rass!! gaban gimbiya bilkisu ya buga tayi sumar zaune domin wani mugun firgici ne ya shigeta, lamid'o kuwa shiru  yyi kafin ya kalli waziri yace" a kira masa liman"  nan take baturiya tayi zumbur ta miqe tace" ranka ya dad'e meke shirin faruwa badai aura masa baiwar za'ayi ba, kurma ce fa" murmushi lamid'o yyi yace" ban buqaci kowa ya kuma cewa komai ba" komawa tayi ta zauna, kowa yyi shiru, babu jimawa sai ga waziri sun shigo tare da liman, kallonsa mai martaba lamid'on adamawa yyi yace" yarima ne ze qara mace ta biyu sai a d'aura wannan aure yanzu" tunda lamid'o yyi gargad'in kar wanda ya kuma mgn hk kowa yyi shiru, cikin hukuncin Allah babban limam ya d'aura auren rumana da yariman adamawa sharuzzaman kan sadaki naira dubu d'ari biya cur, mijin adda fulani  sadaunar adamawa shine yyi saurin biyan sadaki, gimbiya bilkisu kuwa tashi tayi da sauri da niyyar sulalewa ta fice, jiri ya kwasheta ta zube a wurin a sume, hankali ya koma kanta cikin sauri aka soma qoqarin ceto rayuwarta dayake akwai yalwar medical doctors a wannan ahli,  fulani jamila itama likita ce,  tana farfad'owa lamid'o yace su fita da ita zuwa 6angaren fulani innoh, kai tsaye yayyinsa mata suka wuce da gimbiya 6angaren fulani innoh, shi kuwa yarima hkn yyi masa dad'i domin yasha alwashin sai ya ganar da ita kurenta, kuma wlh yyi rantsuwa sai baiwa ta fita matsayi tunda har tayi gangancin ta6a izzarsa, gimbiya bilkisu kuwa zan iya cewa reshe ne ya juye da mujiya domin tashi d'aya ta fita hayyacinta, cikin rashin sani Allah ya bata abunda take bege kullum shine yanzu zatayi tarayya da qasqantacciyar baiwarta akansa, inahh, abunda bazai ta6a yiwu ba kenan, abunda ta furta kenan a fili, hawaye na ambaliyar gangarowa daga idaniyarta, tace" na rantse da Allah nice ajalinki" rumana kuwa duk wannan abun daya wakana a fadarsa lamid'o bata fahimci aurenta aka d'aura da yariman adamawa ba, shiyasa ana fita da gimbiya tabi bayansu, tsayawa tayi a k'ofar shiga 6angaren fulani innoh ta raku6e, wata zuciyar tana qara jaddada mata cewa tana cikin babban rikici tunda har itace silar faruwar komai.......



 


 


 6angaren yarima ayman kuwa  baya qasar yana ukrain akayi bikin yar'uwa gimbiya bilkisu saidai bayi biyu daya sanya su sanya masa idanu kan rumana wato dagorinsa habibu da wata baiwa mai suna lantai suna nan suna sanar dashi komai kan rumana, sun sanar dashi gimbiya zata tafi da rumana adamawa don hk yasa habibu ya sanya lantai cikin jerin bayin da mai martaba ya bawa gimbiya don ta cigaba da sanya idonta kan rumana, aikuwa hknne ya faru lantai na cikin jerin kuyangin da gimbiya bilkisu ta taho dasu, lantai ta samu lbrin wannan auren bazata daya afku da rumana tsakaninta da mijin uwar gijiyanta wato gimbiya bilkisu, abu kamar al'mara, saida ta tabbatar da sahihancin wannan zance kafin ta yiwa dogari habibu waya ta sanar dashi abunda ke faruwa, shima cikin gaggawa yyiwa yarima ayman waya don ya sanar dashi wannan al'mara, sai yyi rashin sa'a wayar taqi tfy, yyi ta trying amma waya bata shiga, dole ya hkr amma yyi dabara tura masa da saqon voice mail, yarima ayman kuwa jarabawa suke gbdy shine yasa ya kashe wayoyinsa don baya son damuwa, yau itace rana ta qarshe daya gama rubuta exams ya fito ya nufi gida, yana shiga ya tarar cook nashi ya gama shirya masa lunch ya jera masa a dinning table, wucewa yyi  kai tsaye ya shige bathroom yyi taking cold shower before yyi taking lunch nashi, yana fito ya shirya ya sanya black boxer da wata armless riga kalar ja ya nemi d'aya daga cikin tsararrun  leather seats din dake tsagaye a falon ya zauna yana kallon wasan real madri da machester city,  tunawa yyi ya janyo phone nashi ya kunna, messages suka soma shigowa babu iyaka, viewing messages d'in ya somayi,   karaff! Allah yakai idonsa kan saqon dogari habibu, kunna voice mail din yyi da sauri yana sauraron abunda yake sanar dashi, cikin sauri yyi dialing number dinsa ringing biyu yyi picking a gigice yake qara tmbyrsa, ya sake sanar dashi abunda ya faru da rumana, rufe idanunsa yyi shiru, dogari habibu nata mgn amma yaqi respond, sai can ya fesar da wata iska daga bakinsa yace" ina son ka hanzarta shiga adamawa ka taho da rumana zazzau yau yau din nan" yana gama fadar hk ya tsinke wayar ya tashi da mugun sauri ta kwashi visa dinsa ya fice......

*Littafi na biyu na kud'i ne*


Alkalamin Bintu ne.....

No comments