Breaking News

SHARUZZAMAN BOOK 1 PAGE 12

 *BOOK ONE* (1)


D'ago dakanta tayi tana kallon  k'wayar idanun mahaifiyar tata dake kanta ta kafeta dasu cike da tsantsar tashin hnkli tana buk'ata jin qarin bayani, murmushin takaici tayi tare dasa hannu tana goge hawayen dake saman fuskarta tace" wlh mum ba k'arya na miki ba, na jiyo wannan zancen ne daga majiya mai k'arfi domin kuwa wacce ta sanar dani wannan sirrin cousin d'insa ce, musamman ta taho tun daga adamawa ta kirani a waya muka hadu da ita a meerah's gym ta sanar dani wannan issue din, sun 6oye hknne ga mai martaba don na tabbata dayasan hk shima bazai aminta da wannan auren ba,

shiyasa ma kk ga fulani kilishi na farin ciki da aure sbd tasan mahaukaci zan aura" shiru a amarya tayi na wasu daqiqai tana auna lamarin cikin kwakwalwarta tana nazari, idan kuwa hk wannan batu yake aikuwa za'ayi tashin balagar tsuntsaye a gidan nan don wlh d'iyata bata ta6a auren mahaukaci, duk a cikin ranta take ayyana hkn, a zahiri kuwa miqewa tayi kawai ta gyara laffayar data nad'e jikinta dashi ta fice da sauri, uwar biyu da lantai na ganin fitowarta suka miqe da hanzari daga inda suke suka rufa mata baya, kai tsaye ta sanya uwar biyu ta kira mata jakadiya, babu jimawa sai ga jakadiya tana isowa ta zube tana kwasar gaisuwa a gabanta, dayake bata gaisuwa take ba, kawai tace" ina son ki shiga turakar mai martaba kimin iso ina son ganawa dashi cikin gaggawa" zumbur ta miqe tace" Allah yaja da zamanin sarauniyar babban babban birni, martaba sarki yana ganawa da baqi ne a halin yanxu" juyawa tayi ta koma 6angarenta saidai ta kasa zaune ta kasa tsaye har saida jakadiya ta shigo ta sanar da ita mai martaba sarki ya sallami baqin nasa, cikin azama ta kuma fita ta nufi 6angaren nasa batare da 6ata lkci ba jakadiya ta shiga ta mata iso sannan ta shiga, ganinshi tayi zaune bisa wata kujera irin ta zaman sarakai, sunkuyawa tayi gabansa ta dunqule dukka hannayenta tana masa jinjina irinta sarakai, yanayin kallon daya mata ne ya bata tabbacin ya amsa gaisuwanta duk kuwa da ba mgn yyi ba,m, sunkuyar dakanta tayi qasa sbd kwarjin daya mata tace" Allah yaja da zamaninka nazo gareka ne dauke da lamari mai tsaurin gaske wato shi wannan d'an sarki da muke shirin baiwa diyarmu aurensa ya bayyana ashe yana da ta6in hnkli amma iyayensa suka 6oye hkn garemu, na duba lamarin nan ne naga taya gimbiya zata iya rayuwar aure da mutumin dayake da cutar hauka" tunda ta fara mgn be dakatar da ita ba kawai kallonta yake har takai aya sannan yyi wani irin murmushi mai wuyar fassaruwa yace" har yanzu baki ajiye makaman yaqinki bane na neman ruguxa wannan aure toh bari kiji na sanar dake abunda baki sani ba,wannan yaro koda a bola yake kwana qarshen hauka kenan toh shine za6ina ga diyarki, saiki koma ki sake shirin dakatar dani na aurar da diyarki tunda kin isa ko kuma ki sanyata ta bijirewa umarni na" gabanta ne ya  buga ta dago idanu tana kallonshi, gani tayi fuskarshi ta bayyanar da tsantsar 6acin rai, saukar da murya tayi tace"Allah ya huci zuciyarka sarkin adalci, ina son don Allah adalcinka ya tabbata ga gimbiya, ka gafarceni ranka ya dade amma don Allah ayi ga wannan al'amari kar ayi garaje" miqewa yyi tsam ya shige ciki ya kyaleta a wurin a durqushe ta kasa miqewa sbd yadda zuciyarta take a chunkushe" saida ta dauki tsawon sa'oi sannan ta tashi ta fita, wucewa tayi yola,gbdy kowa yyi mamakin ganinta a hanyar shiga yola don saita fi shekara ko fiye ma bata leqa yola ba saidai idan wani sha'ani ake, tana shiga 6angaren ta tarar sai shirye shiryen biki suke ba kama hannun yaro, hknne ya kuma baqanta ranta, bayi kuwa sai zubewa suke suna gaishe ko kallosu batayi take wucewa har babban falon fulani ta kuwa tarar da ita kishingide ana mata tausa, ita kanta tayi mamakin ganin amarya jiddo a 6angarenta amma yanayin fuskarta kawai ya tabbatar mata batazo da lfy ba, bata kai ga qarshen tunaninta ba, ta tsinkayi muryarta cikin dodon kunnenta tace" na rantse da Allah idan har diyata ta auri mahaukaci toh bazan ta6a yafe miki ba har saina dauki kyakykyawan fansa" murmushi fulani tayi tace" wannan zancen da kkyi ba nan bane mahallinsa don hk ki ficemin daga sashe tun ranki be 6aci ba" tafawa ta farayi tana kad'a kai cike da mamaki don batayi zaton hk daga wurin fulani ba tace" ehh, lalle kam dole ki fadi hk sbd burinki ya cika, saidai ina sanar ki tuna har yanzu fa wasan be qare ba kuma ba'a sanin maci tuwo sai miya ta qare, muje zuwa" tana fadar hk ta juya tabar sashin ranta a mugun 6ace...




        6angaren yarima sharuzzaman kuwa yabar masarautar zazzau ne cike da tarin tambayoyi musamman akan gimbiya bilkisu wacce action dinta shine yafi komai bashi mamaki, tunanin yadda take bashi hkr yake da hannayenta batare data furta koda kalma guda ba tamkar wata kurma, saidai be kawo a ranta cewa kurma bace don yana da tabbacin idan har kurma ce dole mai martaba sarki ze sanar dashi kuma ma dai bazai taba za6a mishi kurma a matsayin abokiyar rayuwa ba shiyasa beyi wannan tunanin ba sam, jinginar dakansa yyi a jikin seat yana shaqar daddadan qamshin air freshner din dake cikin motar hade da sanyin Ac dake ratsashi wanda ya hadu da qamshin turarensa na kelvin klein yasa komai ya zama so cool........




          Yarima ayman kuwa lamarin soyayyar rumana kullum qara tsiro take tana rassa a cikin farfajiyar zuciyarsa wanda hkn ke tsananta bugun zuciyarsa, saidai yana mutuqar taka tsantsan wurin qoqarin 6oye sirrin son rumans dake addabar zuciyarsa don baya son sanyata cikin tashin hnkli, ana cikin hk admission dinsa ya fito inda ze tafi ukrain  karatar ilimin taurari wanda hk shine sha'awarsa but yanzu sbd rumana sai yaji baya son zuwa ko'ina, amma zuciyarsa ta basa tabbacin nan da shekaru uku kamar yau ne insha'Allah har yaje ya dawo babu abunda ze faru da rumana sbd shi tunaninsa yana ganin rumana yarinya ce shar  har yaje yyi shekara ukunsa ya dawo, shirye shiryen tfy yake abinsa, tunaninsa idan ya dawo ya fitar da ita waje don a nemo mata mgnrta.....





Shirin biki sosai ake a wannan masarauta, an gayyaci manya manyan masu kidan hausa kala kala daga jihohi daban daban wadanda zasu nishadintar da mutane, rana bata qarya saidai uwar diya taji kunya yau juma'a itace ranar daurin auren gimbiya bilkisu da yarima sharuzzaman, biki ne na ya'yan sarakai dole duk ta inda ka hanga ka gano manya rawunna, ga kuma qosassun cikin gwamnatin qasa duk sun hallara.......

*Littafi na biyu na kudi ne*

Alkalamin Bintu ne....

No comments