SHARUZZAMAN BOOK 1 PAGE 11
*BOOK ONE*(1)
1️⃣1️⃣
_*Hjy fatima bintu giwar mata, a jima anayi sai gsky, kece amarya kuma kece uwargida,kece jiya kece yau a gidan Alhaji Bello majidadi, mai sonki ya soki mai qinki kuwa shine da dakon asara*_……………
A hnkli ya koma kujerar dayake zaune ya d'ora kafarsa d'aya kan d'aya, fuskarsa a tamke tamau yana daga zaune yana binta da wani mugun kallo a wulaqance, ita kuwa tana nan durqushe a inda take har yanzu bata motsa ba jikinta kuma be bar rawa ba don a tsorace take sosai sbd ita kanta tasan idan har asirinsu ya tonu aka gane wlh ta banu a wurin fulani kilishi, sanyin Ac ne kawai ke ratsa jikkunansu
falon yyi shiru tamkar mutuwa ta kilma,sai kawai ganinshi tayi ya miqe ya tattara hadaddun tsadaddun phones dinsa dake gefensa a ajiye ya taka a hnkli cike da nuna isa ya fice daga cikin falon batare daya kuma kallon inda take ba yabarta a durqushe a wurin tamkar mutum mutumi, ita kuwa har ya fice tana binsa da kallo tana auna yanayin zubin halittarsa don sai lkcin ta samu nutsuwar masa kallon qurullah, dogon namiji mai cikar zati da haiba irin na zaratan maza, yyi gadon kyau na zallar fulanin usul, murmushi tayi ta soma mgnr zucci," dole mn yyi wulaqanci don yaga yana da kyau" abunda ya daure mata kai shine ita dai bata ga makusa ba tattare da wannan uban izzah da gimbiya bilkisu ke gudun aurensa, tace" toh kodai yana da wani mugun halin ne da bataso" rankwashin kanta tayi da sauri don bata ga ma'anar wannan tunanin da take ba, tana shirin tashi kenan gimbiya bilkisu ta shigo a matsayin itace rumana dauke take da kwandon kayan marmari, turus tayi lkcin da taga rumana ita kadai babu yarima, a tsorace rumana ta kalleta, gimbiya bilkisu tace" ina yake" sunkuyar dakanta tayi qasa, murmushi tayi ta tmbyta da yaren kurame tace" kila kedin ce baki masa ba, ni daman hk nakeso, wataqila yace baya son aure ya fasa" dariya tayi sosai tana dukan kafadar rumana cike da alamun wasa, abun da yyi mutukar baiwa rumana mamaki kenan yau itace gimbiya bilkisu ke yiwa wasa tamkar qawarta, lalle yau gimbiya na cikin farin ciki, batare da 6ata lkci ba suka sake musayar kaya, gimbiya bilkisu ta cire na bayi dake jikinta ta maida nata, rumana ta take mata baya suka fice, aikuwa suna shiga fulani kilishi ta taso da sauri ta riqe hannun gimbiya bilkisu fuskarta dauke da wadataccen murmushi, tuni gimbiya bilkisu ta daure fuska don gani take ta bakin amarya ne akwai abunda fulani kilishi ke buqata shiyasa tafi kowa farin ciki da wannan aure, ita kuwa fulani yanayin yadda taga sauyi a tattare da fuskar gimbiya ne yasa ta dakata batare data riqo hannunta ba tace" ki shiga ki huta" tana fadin hk ta juya ta tafi ta shige ciki, wucewa itama tayi ta shige bedroom dinta, rumana tabi bayanta qoqarin cire akyabbar jikinta take cikin saurin rumana tasa hannu ta zame mata alkyabba taje ta adana sannan ta dawo ta tsaya a gabanta kanta a sunkuye tana jiran taji umarnin da zata bata, kallonta tayi ta yatsine fuska ta daga mata hannu kan ta tafi, juyawa tayi ta fice daga dakin ta nufi 6angarensu na bayi, tana tfy tana shinshina jikinta da kayan jikinta dake fidda daddadan qamshi sbd sanyasu da gimbiya tayi, hk har ta qarasa zauren bayi ta wuce dakinsu, tana shiga ta tarar dasu daure da zannuwa a kirji hannayesu dauke da mafifici sai faman fifita suke sbd uwar zafin da ake fama dashi idan kuma da rana ne hk ake fama da zafin rana, kallonsu tayi murmushi ta nemi gefen asiya ta zauna, cikin sauri saratu dake gefe a kwance bisa wata tsumman katifa ta dago idanu tana kallon rumana tace" jama'a ko ni kadai ce nake jin qamshin da yar buzuwa keyi daga shigowarta fa naji qamshi, Allah yasa dai ba turaren gimbiya take satowa ba idan ba hk ba uban waye ya bata turare" asiya tayi charaff ta chafe zance tace" kedai wlh kin shiga uku, wacce kk yiwa sharrin ba jinki take ba don hk saiki rufe mn baki kin cika mn kunne" daga hannu tayi a zabure da niyyar tsinkawa asiya mari, cikin sauri rumana ta riqe mata hannu tana mata alama kan tayi hkr, fizge hannunta tayi tana yarfewa tana hucci kamar zakanya ta kalli rumana tace" ke kuma don kutumar ubanki kk kuma riqemin hannu wlh saina tagayyaraki keda ita din" wata uwar harara asiya ta doka mata tace" dani dake shege ka fasa, banza gadon tsiya" wannan kalma da asiya ta furta mata tayi mugun baqanta ranta tace" idan kina da kunya baki ambatar tsiya don kuwa kowa yasan ubanki tsumma be bari ba har ya mutu sbd baqin talauci" murmushin takaici asiya tayi tace" ehh, fadi da ihu ki qara da wayyo, iyakarsa talauci amma be lalata diyar kowa ba har ya mutu, uban wasu kuwa har d'an gaba da fatiha aka dire mas....." batakai ga qarasawa ba taji saukar wasu lafiyayyun tagwayen mari har saidai taga tartsatsin wuta, aikuwa itama batayi wata wata ba ta shaqo wuyanta dambe ya kaure, sai lkcin yan dakin suka soma kiciniyar rabasu, rumana kuwa sai kawai ta soma hawaye don ita bata qaunar tashin hnkli shiyasa take da mugun hkr, hayaniyar tasu ce yasa uwar biyu leqowa dakin ta tarar da dambacewar da akeyi, komawa tayi taje ta sanar da uwar bayi, aikuwa sai gasu sun shigo wata uwar tsawa ta doka musu aikuwa ba shiri suka rabu, sai wiki wiki suke da idanu don sun san halinta yanzu sai ta basu horo, aikuwa kallonsu.tayi daya bayan.daya tace" dukkaninku ku biyoni" a tsorace suka miqe suka bi bayanta, wankin bango ta sanyasu tace" bani son ganin datti a jikin bangon nan na gbdy zauren bayi su wanke mata shi tas" kuka suka saka suka zube saman guiwowinsu suna bata hkr amma tayi biris dasu, dole suka miqe suka fara abunda ta sanyasu.......Gimbiya bilkisu kuwa sulalewa tayi ta shiga manbilah, kai tsaye dakin amarya ta nufa, tarar da ita tayi sai safa da marwa take a tsakiyar qaton bedroom din nata, tana ganin yar tata ta taho da sauri ta riqeta ita kuma ta fada jikinta a sankarce tana hawaye, tace" mene ya faru ki sanar dani mn daughter" cikin kuka tace" yanzu kina ganin ana shirin mini auren dole kin kasa aiwatar da komai, yanzu wannan makirar matar ta fiki fada kenan a wurin mai martaba yake mugun sauraren mgnrta" tureta tayi daga jkinta tana harararta tace" yaushe kk zama mara kunya kk mgn da mahaifiyarki irin hk" maida kanta tayi jikin mahaifiyar nata tace" sorry mum, wlh raina ne ya 6aci don na tsani auren nan musamma ma yanzu da naga wanda ake shirin hadani dashi" a zabure amarya ta kalleta tace" me kk nufi da fadin hk" tace" kwata kwata bemin bane, beyi kalar irin mijin da nakeson aure ba sam, kuma ma naji ance yana da mental illness" cike da firgici amarya ta juyo tana kallonta tace"What?!! who told you this nonsense!!........
Just kuyi manage page din babu tsayi pls...
*Littafi na biyu na kudi ne*
Alkalamin Bintu ne.....
No comments