Breaking News

NIDA KE 2

age 2️⃣

   

         "Kai bakin ki da dadi kamar xuma me kika saka ne......??"

yayi mata tambayar yana lumshe sexy eyes d'insa, shiru tayi sanadiyar nunfashinta dake neman daukewa tipppppppp suka jita ta fadi sumammiya sai kunfa ke fita a bakinta dogon tsaki yaja tareda juyawa kan.table d'in wani kwalbar giya yasake dauka ya bude ya kafa kai saida ya sanye shi tassss kafin yace

   "ku kaita asibiti idan kuma ta mutu ku binne ta...."

ataik'aice yayi maganar cikeda gadara nan ya xauna yacigaba da shaye-shayensa




"luba lafiya kuwa firdausi bata dawo ba har yanxu naga duk sauran yaran sun dawo kuma naje makarantar su sau biyu ban ganta ba..?."

yayi maganar da alamar damuwa tafff a fuskarsa wacce ya kira da luba dake xaune a saman tabarma tana cin abinci ta tabe baki tace 

"mtsssw malam duk kabi.ka isheni tun daxu sai faman yi mun tambaya daya kake toh ni.ina ruwana da inda taje nasan dai wannan lallatacciyar yarinya shashasha ba inda xataje sai dakin gardi inba haka ba ai duk abokan dawowarta gida sun dawo...."

cikeda mamakin maganganunta yake kallonta saida ya saita kansa kafin yace

"haba luba wannan ba rayuwa bace kinfi kowa sanin halin firdausi baxatayi wannan mugun abun da kike xarginta dashi ba..."

  "tsiyar banxa ai ba'a shaidar yaro..."

      "nasanda hakan amma firdausi baxayi hakan ba..."

     "maganar banxa baxaka gane hakan ba sai ta dauko maka abun xagi..."

tana fadar hakan ta tashi daga wajen ta nufi dan madaidaicin kitchen d'insu ta barshi nan tsaye 



b'angaren firdausi kuwa bayan sun kaita asibiti doctor ya dubata ya tabbatar musu da tsoro ne yasata wannan dogon suma nan yayi musu gargadi da abar barin tana jin tsoro sosai bayan doctor ya sallame su nan suka jata xuwa mota kuka tafara masu mugin tsawa suka daka mata nan taja bakinta tayi shiru tareda hadiye kuka me mugun daci da xafi , a inda suka barshi nan suka sameshi lokacin kuwa duk ya gama da kayan shaye-shaye dake kan table din tun daga nesa yake kallonsu.har suka iso kallonta yayi.yace 

   "xaki iya tafiya amma ki shirya kawo mun kanki.....dan wallahi koh mutuwa kikayi sai na ci ki matsawar dai xanga gawarki....dan haka nabaki nan da xuwa gobe idan baki xoba xan sa ubanki ya kawo mun ke nan.....kuma a gabansa xanyi abunda xanyi dake....matsiyaciya kawai...."

duk wannan maganar da yake idonsa a lumshe suke

sai hayakin wiwi da yake busarwa 

  "xaku iya tafiya ya"

yafada a takaice 

    wayarsa ya dauko ya kira wani number ringing biyu aka dauka cikin irin voice d'insu na mashaya ya fara magana

  "hello saif..."

  "ranka ya dade fatar kana lafiya"

   "lafiya klau"

yafada ataikaice 

"masha allah"

   "saif akwai wata yarinya dana nuna maka jiya ita nakeso ka dauko mun yanxu ka kawo mun...."

    "ranka ya dade anya kuwa xan iya dauko wannan yarinyar...."

yayi maganar cikin girmamawa 

    "saif kasan halina duk naji kwadayin abu wallahi sai na ci shi.....kuma banason ana mun gardama...."

  "hakane ranka ya dade amma matsalar daya ce gidan su yarinyar akwai sauri sosai dakyar xan iya tahowa da ita dan koh fita basayi sai idan xasu makaranta...."

tashi khal yayi tsaye tareda bugun table din da karfi yace

   ."waye ubanta a nigeria dahar xece baxan cita ba wallahi wallahi yau sai naci wannan yarinyar kuma karka sake yi mun gardama kaje nan da 30 minutes kaxo mun da ita...."

    "alright boss yanxu nan kuwa...."

yayi maganar cikin tsoro dan sarai yasan halin boss ba imani ne dashi ba duk ya kwallafa rai a yarinya dole sai yayi amfani da ita kuma shi baya neman wa'inda suka saba sai dai wacce bata taba ba ita d'in ma yana amfani da ita yagama da ita dan shi a tarihin rayuwarsa baya hawan mace sau biyu koh kuwa wacce aka taba amfani da.....





firdausi kuwa a kusada gidan su bodyguard d'insa suka direta wanke beauty face d'inta tayi ta saita kanta kafin ta fara tafiya cikin natsuwa harta isa bakin kofar gidansu sallama tayi babanta dake tsaye tun kusan awa biyu y dago kansa yana amsa sallmar da fara tafff a fuskarsa rusunawa tayi ta gaida shi cikin girmamawa 

   "yar aljannah lafiya ina kika tsaya tun daxun sauran yan uwanki duk sun dawo baki dawo ba nima sau biyu ina komawa makarantar ku duba ki allah dai yasa lafiya...?"

nauyayyen ajiyar xuciya tasaki tana neman karyarda xata masa dan batason abunda xe tayarwa da mahaifinta hankali  

"kinyi shiru....?"

ya kuma tambayarta nan ma saida ta dan dauki lokaci kafin tace

  "uhmm baba dama na bi gidansu sauda ne na karbo littafina da mukaje ne muka samu mamansu batada lafiya sai na tayata aiki....."

      tayi maganar voice dinta na cracking jikinta kuwa sai rawa yake idonta kuwa sai kiftawa yake da sauri-sauri

   "allah sarki ana son haka amma ki dinga sanarda koh kannenki ne kafin ki aiwatarda abu kinji toh ina jakarki din...."

xaro ido tayi nan ta tuna tabar jakarta a cen 

     "na manta shi gidansu saude amma nasan gobe xata xo mun dashi makaranta..."

luba dake tsaye bakin kofar daki ce ta tabe baki tace

    "kai yanxu malam ka yarda da wannan karyar....."

tsaki yayi ya wuce daga wajen ita kuwa firdausi sai rawar sanyi take cikin rawar murya tace

     "umma ina wuni...."

   "yana kan uwarki....matsiyaciya kawai shashashar banxa kixo kije ki debo mun ruwa wanki na jiranki shegiyar yarinya kawai allah idan bakiyi hankali ba sai kin kwasowa malam abun kunya karuwa kawai xo nan...

dan ubanki..."

dakyar ta iya jan kafanta har xuwa inda umman ke tsaye 

   "gani..... um.....ma..." tafada bakinta na rawa

   "ina kudin da wanda kikaje wajensa ya hauki yabaki.."

xaro ido tayi gabanta na mugun bugawa tace

  "umma banje....gidan kowa ba gidan su saude naje....."

cikin jin tsoro tayi maganar

   "munafukar banxa karya kike.....idan ma be baki ba idan kika gama aikinki sai kije ki samu kudi....."

cikin voice din kuka ta fara magana 

  "umma ina xan samu kudi wallahi umma tunda allah ya halicce ni ban taba xama tareda wani namiji ba balle har na aikata xina....."

  katseta tayi tana cewa

   "rufa mun baki kawai wa xakiyiwa wayon yaran xamani....toh wallahi idan ma baki taba ba yau xakiyi dan dole kije ki samu mun kudi dan kudin adashe nakeso in xuba gobe...."

"umma wallahi bansan inda xan samo miki kudin ba "

tayi maganar tana matsanacin kuka me tsuma ran me saurare 

    "mtsssw munafukar banxa maxa kije ki cire kayan makaranta ki saka wasu kixo yanxu....."

toh tace mata tana barin wajen cikeda bakin ciki da wanne dataji da masifar da khal de addabarta dashi koh kuma na umma wanda ba randa bata mata....





saif kuwa direct motarsa yaja black colour me bakin class wanda duk maitar idonka baxaka taba ganin wanda ke cikin motar ba,babbar mota ce sosai wanda ba karamin kudi xe iya sayenta ba dan duk kafffff nigeria irinta basu wuce 20 koh 15 ba a bakin gidansu yarinyarda boss dinsa ya aike shi ya kawo mishi ita ya tsaya yafi 1 hour a wajen bega kowa ya fito daga gidan ba agogo dake makale a hannunsa ya kalla karfe hudu 4 cippppp ajiyar xuciya yasaki dayaga wasu yan yara suna fita daga gidan yara ne kanana biyu duk sanye suke da uniform na makarantar islamiya saida sukayi wajen 15 minutes da fita saiga wata matashiyar budurwa wacce baxata wuce 18 to 19 years ba ta fito sanye cikin uniform itama wanda yayi mata masifar kyau a hankali take tafiya tana dan dago kai tana dube dube koh xataga kannenta amma bata hangesu ba hakan yabata damar daci gaba da tafiyarta saida tayi nisa daga gidansu kafin saif yaja motar daidai saitinta ya tsaya tareda bude glass din motar 

    "barka da wannan lokacin..."

tsayawa tayi tareda dago da kanta ta kalle shi 

    "yauwa barka"

tafada ataik'aice

  "am ina xaki haka...kinata tafiya kohxaki shigo na rage miki hanya..."

  "aa nagode"

"haba dai yan mata ba girmanki bane tafiya a kasa kitaimaka ki shigo akwai maganarda xanyi dake..."

"kayi maganar  inaji a nan ma.."

"kinga nan muna kan hanya dakin shiga muna tafiya muna yi harna sauke ki a makarantar...."

dan murmushi tayi tace

   "toh tunda ka nace amma akwai ka da naci...."

tafada tana xagayowa ta bude motar ta shiga 



firdausi kuwa ruwa kawai ta watso ta cenxa kaya direct wajen ummanta ta nufa 

 "umma gani..na shirya..."

  dago kai umman tayi ta kalleta da kyau kafin tace 

   "da wa'innan kayan xaki wajen nema mun kudi......"





_08057761657 domin comment koh kuwa bada wata shawara_







comment and share please

No comments