MY UNCLE 9
Page 9
Hips dinta yabi dakallo yanda take tafiya iman yakira sunanta batareda yasan abunda zaice mataba, Na'am uncle tajuyo , Ok kibarshima jeki kawai yafada duk yarude, Tana fita yasauke ajiyar zuciya yana cewa Allah yakiyaye, wannan karamar yarinyar inaa bazaiyuba
Tana shiga daki salma tashiga tsokanarta
Tana cewa har angama shan soyayyar wlh iman harnaji nima aure nakeso
Iman takaimata duka tana cewa soyayyar me ai bazakiga soyayyaba sai na aure Abdul dina alokacin zakiga miye love
Kice astagafurillah iman salma tafada
Sabida me iman ta tambaya
Saboda ke matar wanice amma kina kiran sunan wani kato
So what iman tafada tana daga kafada ba'alamun damuwa atattare da ita
Haka suka cigaba da hirarsu
*********
Yau kimanin sati biyu da tafiyar Aliyu
Yasake aikinshi kawai yakeyi dan wani daji akaturasu inda ake zargin akwai masu garkuwa da mutane
Aliyu jarumine ko afagen daga shiyasa komai za ayi shine agaba
Agida kuwa iman ma tasake sai karatunta takeyi hankali kwance tama manta da wata maganar anyi mata aure
Harda gargadi tayi ma salma kancewa karta kuskura tagayawa yan class dinsu wai ammata aure shiyasa ko a group dinsu bawanda yasani
*********
Kasan cewar hankalin Aliyu ba akwance yakeba sai ciyon nashi yakwanta Yadan dena tashi koyatashi amma baya mishi sosai
*********
Acan gida kuwa da wayo ummah tashiga gyaran matar dan nata lokacinda yarage saura wata daya Aliyu yadawo momy taroke alfarmar dan Allah tanaso abata iman akwai shirin datakeso tayi mata
Dama iman Yar dakin momy ce momy na bala'in sonta kamar ita tahaifeta
Momy takudiri aniyar saitasa Aliyu kuka da hawayensa akan son iman sannan zata karya masa wannan dokar tashi narashin son yara yan kasa da 20yrs
Dan haka takanas tadauko wata daga Niger domin gyaran yar tata iman nata tambaya miye wannan ake mata amma momy tacemata kawai dai za agyara mata jikinta ne
Iman tace to meyasa ba'ayiwa salma ba momy tace da angama da ita sai salma dakyar dai akasamu akayimata wayo
Aikuwa aunty luba dan haka suke kiran matar Yar Niger tashiga gyaran iman ba kaukautawa
Aikuwa kwana biyu fatar iman ta fara murjewa idan kakalleta sau daya saika kara kallonta
Gyara akemata ba kama hannun yaro dilka kan kalala tashata saida aka dauki sati uku ana mata gyaran jiki
Wow ya subhanallah masu karatu dama kunsan yanda iman take ga mugun kyau da kyan jiki balle yanzu datakara shan gyara
Wani irin kyau da kyalkyali takeyi tahadu matuka idan kakalleta sau daya bazaka iya dauke ido akanta ba
Jikinta yawani irin murje kamar ka kwanta jini yafito
Kayan fruit kawai momy ke dirka mata
Hmmmm masu karatu nabarku kucigaba da kissima yanda iman tayi kyau domin idan nace zantsaya bayyana muku haduwarta to shafinnan danagaba ma bazai isheniba kuyi imagining dakanku😀
A sati na ukkune satin da Aliyu zai dawo aka fara gyaran kai mayuka kala kala akashiga samata dama gashi kam akwaishi dama saigashi yakara santsi dalaushi sai walwali yakeyi
Masu karatu just kuyi imagining kawai
Iman tazama ko'aina tazauna sai tabar kamshi domin irin turarukka masu sanyi da laushi da'aka rikayi mata anfani dasu sai suka zama duk inda tabi saitabar kamshi
Ana gobe aliyu zai dawo aka kira mai kunshi ta tsantsaramata lalle mai daukar hankali baki daja yayi matukar kyau dama abunka da fara sai yakara mata wani siririn kyau
Iman kanta saida taji canji ajikinta
Muje zuwa masu karatu yanzu aka fara yanxu labarin zaifara
I love you all my fans
No comments