Breaking News

MY UNCLE 43-44

Page:-43/44


Hahahahhahaha dolene nadara masoyana domin kunyi matukar sani nishadi da farin ciki wlh kun mugun birgeni kuma kunkaramin karfin gwuiwa nagode masoyana nima zancigaba da faranta muku insha Allah kudai kawai kucigaba da bibiyar littafina masoyana kuma akwai sabon albishir  insha Allah kwananan akwai wani zazzafan book dina mai zuwa nagode masoyana nima inasonku sosai sosai dinnanfa


Masu zuwa sunan yan ukku aliyu da iman sunce agaya muku su marhaban da kowa da kowa Allah yakawo lfy saikunzo 



Ana cikin tsabtace yaran kuma aka gano akwai sauran wani aikuwa likitoci suka rufu akanta takara santalo kyakykyawar yarta tareda sakin wani irin numfashi aliyu kam rasa inda zai tsoma kansa yayi sabida farin ciki saida yayi sujjada yagodewa Allah


Bayan ankammala gyarasu itada yaran aka mikasu hannun su momy familyn gabadaya wayanda suke agarin sungama hallara saikace wani babban taro ake a asibitin 


Ana fitowa dayaran kuwa kowa sai murna yake yanmatan familyn dama matan auren kowa sai rige rigen daukan baby's din ake yaran kyawawa gwanin ban sha'awa namijin sak aliyu hatta da yatsun kafarsu da hannu iri dayane sai matan da sukuwa su ka dauko aliyu tawani gafen kuma iman aikuwa sunbala in yin kyau gwanin birgewa saiyaba kyan yaran ake

 aliyu kam  ji yake kamar yakwace yaransa ahannunsu domin gani yake kamar za ajiwa yaran ciyo ranar gaba daya aliyu ajiye miskilancinshi yayi sai sakin murmushi yake kallo daya zakayi mishi kagano yana cikin tsantsar farin ciki 


Iman kuwa tuni aka kaita dakin Hutu bayan angama kammala shiryata 

Aliyu kam tunanin matarshi kawai yake duk da likitoci sun tabbatar mishi tana cikin koshi lfy 


Aikuwa tuni ummah tatura wasu gida domin aje afara shirye shiyen tarbon  sabon mijin nata da kuma kishiyoyinta kasancewar ummah (mahaifiyar aliyu )tace awurinta zata zauna 


Kowa nazaune adakin aliyune rungume da yayan nashi sai dariya ake mishi ummah kuwa harara kawai take zabga mishi ganin Sam aliyu kunyar kowa bayaji Yakama yayanshi yarike amma da yadago suka hada ido da ummah tazabga mishi harara saidai kawai yaduka yayi kissing din yayanshi


Ummah da talura aliyu yamaida ita kamar wata kakarshi tagaji tadauke kanta 


Ganin iman tafara alamun tashi yayi saurin mikewa yamikawa salima ya ron ya isa wurinta da ta macen da namijin 


Aikuwa tana bude idonta taga aliyu yawani zuba mata ido murmushi yasakar mata itama kuwa batayi kasa agwuiwaba tamayar masa da wani lallausan murmushi ajiye yaran yayi agefenta yatai maka mata ta tashi zaune sai alokacin talura da wayanda suke adakin aikuwa taji matukar kunya 


Suma tasowa sukayi kowa yanayi mata sannu 


Aliyu kuwa kallo kowai yake binta dashi jiyake inama ace awannan lokacin agidansu suke da matarshi da yayanshi sunga tarairaya da soyayya amma inah 

Sanda  momy tataimaka mata tayi brush sannan aliyu yahada mata shayi mai kauri yadawo kusa da ita kamar zai maidata ciki ganin haka Dakin suka shiga sulalewa da daidaya sai salma datazo wucewa domin dayar yarimyar tana hannunta 


Yakirata salma kawo tanan itakam mamakin uncle din nata take domin taga tsananin son yayanshi yau aikuwa yadawo tadaurata akan godon tare da yan uwanta Sanda tayiwa iman signal sannan tabar Dakin tanafita yajuyo yakalli matarshi sa'annan yarungumeta tsam ajikinshi tareda sakar mata kiss a kumatu da dai dai yadauko yaran cikin tsananin farin ciki yadaura mata namijin akan kafa 

Baby Kinga kyautar da Allah yamana ko ahankali yashiga nuna mata yaran sai ido take binsu dashi tana mai godiya ga Allah daya azirtasu da wayannan kyawawan yaran har guda uku batace komaiba Dan haka aliyu yadauki tamacen daya yadaura mata akan dayan cinyarta  still batayi magana a sai idon data zuba musu Suda masoyin mijin nata ganin taki tayi magana yasashi kama kunnenshi yace sorry mummy munsan mun wahaladdake nida baby's dina kiyi hakuri


Ita dariyama yabataw yanda yayi kamar zai mata kuka aikuwa tashiga dariya shikuwa shagala yayi da kallonta yanda dariyar tayi bala'in yimata kyau sa'annan beauty piont dinta yawani lotsa gata tayi wani fayau da ita 


Sanda tagama dariyar talura yashagala akallonta tahura masa iska tare da fadin

Hey guy kallonta na miye 

Murmushi yayi yalumshe ido yabudd

Sannan yarungumeta tareda furta mata inasonku dayawa yanmata I love you so much 


Bude kofan da akayi yasanyashi saurin sakinta ummahce tashigo aikuwa wata irin harara ta harba mishi 


Amma aliyu Sam ko ajikinsa murmushi kawai yayi 


Kayansu ummah tashiga hadawa Sannan yagayawa aliyu an sallamesu  


Hakadai suka tarkata sukabar asibitin 


**********

Agida kuwa suna komawa alokacin har andaura ruwan zafi momy ce (abokiyar Zaman mahaifiyar iman) tashiga yiwa iman wunka alokacin aliyu nadakin aikuwa ana farawa iman takwalla Kara aliyu kamay zaiyi kuka yacewa aunty Wai wannan wunkan dolene nikam jinkarar iman yakara daga mishi hankali........... 


Kuyi manage pls


I love you all my fans

💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋

No comments