Breaking News

MY UNCLE 20

 الحمدلله   الحمدالله  الحمدالله

abokanai,dakuma masoya ina godiya sosai da addu o inku nagode sosai Allah yasaka da alkhairi nagode nagode ! Nagode!! Allah yabar zumunci da kauna ameen🙏🙏


Insha Allah my uncle yadawo muku kuma zaicigaba dazuwa muku akowacce rana 🥰🥰🥰


Page 20

Tana tafiya suhaila tafashe da dariya 


Iman kenan ai wlh idan kinsan wata bakisan wataba uncle inatayaka murna tafada rana kara fashewa da dariya 


Kaima uncle insha Allah sai munyi maganin wannan jiji dakan naka suhaila takara fada tana murmushi 


*********** 

Iman kam bayan takoma gida saitashiga tunanin ta inda zatafara  amma kuma wannan abun da suhaila tafadamin indai har uncle zai kyaleni in aure Abdul dina dolene inyi yanda suhaila tafada 


Aikuwa Iman tundaga ranar tashiga lissafin ranar da Aliyu zai dawo 


Domin aunty ma tatambaya wai yaushe uncle zaidawo aunty kuwa tashiga murna domin atunaninta ko Iman yanzu tafara son Aliyu ne (wannan yanadaga cikin shawarar suhaila cewa kada Iman takara barin wani daga cikin yan uwa  yasan cewa bata son Aliyu tanuna cewa yes tanasonshi sabida koda yasaketa bawanda zai Dora mata laifi za ace laifin Aliyu ne domin ita Iman tanasonshi)aikuwa Iman tashiga lissafi 


********** 

Kwanaki sunja har lojacin dawowar Aliyu yayi domin gobe zasu dawo imankam duk wani shirye shiryenta ankammala mata  aunty har mai kitso da lalle tadauko tayiwa iman aikuwa iman tafito Amarya sak sai sheki take da kyalli 


Umarnin abbane cewa da Aliyu yadawo amika mishi matarshi suwuce gidansu shiyasa komai angama har Jere anyi idan har zaka kalle iman bazaka taba cewa bagidan Wanda takeso yakesonta za akaitaba domin yanda take kamar ba abunda yadameta 


Aliyu kam yarasa awani yanayi yake ciki tun lokacinda akakirashi akashaida mishi daya dawo  matarshi zata tare  gidanshi 


Shiyasa kodaukin dawowar bayayi jibril kam sai rawar kai yake yakusa zama ango 


***********

Damusalin karfe 5:57pm  motocinda suka dauko Aliyu daga airport suka gama daidaita parking dinsu aharabar gidansu Aliyu domin yau baima sauka Gidan aunty ba yadauki akalla mintuna 15 kafinyafara sauko da kafarshi yafito daga motar wow masha Allah wani irin fresh Aliyu yakara dawani irin kyau  kamar bawanda yaje filin dagaba saidai yadanyi rama ita yakara fito mishi da ainahin samartakarshi kamar kasaceshi kagudu sanye yake da wandon sojoji dakuma farar riga Wanda tadan kama mishi jiki takara fiddo mishi da faffadan kirjinshi sai ridar sojinshi tasama wacce baisanyaba yarikota kawai ahannu bazakayiwa Aliyu kallo daya,bakayi sha awar kara kallonshiba sexy ayes dinshi yalumshe yanabin Gidannadu da kallo kasan cewar lokacin daminane akwai yiywar kayaushe ruwa zasu iya saukowa shiyasa wani irin iska ake mai hade da sanyayar sanyi maisanya nishadi

Shima Aliyu hakance takasance dashi wani irin nishadi yakeji Wanda yarasa konamenene


Rungumar da Dan karamin yaron yakaimishi tana cewa oyoyooo uncle ita tamayardashi daga duniyar dayaje yayi Saurin daga yaron yana sakar masa murmushi shima yanafadin oyoyooo my son yaushe kukazo Aliyu namasifar son yara duk muskilancinshi idan kaganshi tareda yara bazaka zata shibane yanason yara sosai 

Shiyasa jininsu yahadu da manir Dan yayar aliyune shima yaron yanason Aliyu sosai


Uncle dazu mukazo wai naji mamana tana cewa aunty iman zata koma gidanka nima Dan Allah uncle zanbita  yaron yafada yana langabarda kanshi kan kafadar Aliyu. 


 murmushi  aliyu yay yanacewa my son kaima kashirya kayanka kacewa aunty iman zaka bita kaji


Murmushi manir yayi yanacewa dagaske uncle kai yagyada mishi yana murmushi ahaka suka karasa,cikin falon 


Falon cike yake da yayyen Aliyu maza da mata aikuwa suna ganin aliyu sukadauki kuwwa suna cewa sannu dazuwa ango awurin iman 


Gabadaya dakin ya dauki hayaniya Aliyu kam gaisawa,yayi dasu daya bayan daya yana rike da hannun munir Maman munirce ta janyo hannun munir tanacewa zo kabari uncle dinka yahuta yashirya haka sukayita tsarguwar Aliyu shidai murmushi kawai yake 


*********

9:30pm Abba dakainai sai aunty suka dauki iman izuwa Gidan Aliyu iman saikuka take  bayan sunkaita saida Abba yayimata huduba da nasiha mai Shiva jiki sannan yabargidan tareda tabbatar mata tabi mijinta saudakafa tayi mishi biyayya kuma tayi hakuri aikuwa takara sakin kuka


Auntyma nasiha tayi mata tareda kara koyamata mata yanda ake zama da miji 


Hmmmm iman kam jinsu kawai take domin ita tasan ko sati daya bazatayi agidan aluyuba zai saketa idan dai hartayi amfani da shawarar suhaila 


Saida safe sukayi mata bayan aunty takira Aliyu yatabbatar mata yana kan hanyar zuwa yanzu tana kuka tana rike aunty haka suka tafi suka barta 


*********

Aliyukam fir yahana salim yarakoshi wai acewarshi aiwannan zubarda kimane wannan karamar yarinyar aisaita rainani idan taga wai harrakiyar ango akayimin 

Salim kam dariya yayi yana mikamishi ledojin kajin dayasiya mishi yanacewa wlh yaro kakusa shiga hannu zakabani labari


Da sallama tashiga Gidan dakinda yake tunin na akabarmishi yashiga iman kam daga wurinda take zaune  harbacci barawo yayi awon gaba da Ita tana bude Kofar ya hangota yayi saurin rufe Kofar yajuya dayan dakin 


 Kajinshi yaci yakoshi bayan yayi wanka sannan yaje yakwanta bayan yasha wahala kafin baccin yadaukeshi 


Saidai muce asuba tagari Amarya da ango 


************

Aliyu kam tunda safe yabar Gidan Dan baya mason abunda zai hadashi da yarinyar har tayi mishi kallon miji shiyasa tunda safe yabar Gidan


Iman kam sanda tatashi bataga aliyuba bata dumuba saidai tsoronda tarinka ji itakadai awannan katon Gidan daga baya kuma yanmatan family dinsu sukazo haddasu salma sai tsokanar iman suke wai yanzukam tagirma ko domin sunsan jiya uncle kam yasha bidiri aikuwa iman tace yawwa gama motarshonan naji hon dinshi bari yashigo intambaya mukushi aikuwa sukashiga bawa iman hakuri ta kyalkyale da dariya tana cewa ohooo nikuka raina ko to wlh yanzu nimatar yayankuce adinga bani respect tafada tanayi musu gwalo nankuwa suka shiga tsigarta daga mai cewa tamatsu uncle yakashe bakin tsiwa sai mai cewa ai wlh jiya taso uncle yakashe arna haka sukacigaba da fira


Jin iman tace zatagayamai idan yadawo suka tattara sukace wlh sukan sunwuce bazata jaza musu shan kashi abanzaba duk yanda iman taso su tsaya amma suka ki 


Haka suka tafi suka barta ita kadai bayan sun gama girki sunjere 


Iman kam wunka tashiga domin so take ayau tafara gudanarda shirinta


Wani irin wunka tayi Wanda ko awurin wankan sanda tabata lokaci maiyawa sabida turarukkan wunkan datayi amfani dasu wani mai tashafa mai laushi da dadin kamshi tashafa powder da man baki tayi kyau sosai sai sheki take kamar wata Dan Daren goma sha hudu wata arniyar Riga tasanya mai karamin hannu iyakar rigar guiwa tayi mata kyau sosai kuma tafitar mata da shape dinta kallon kanta tayi amadubi aikuwa ta zaro ido tana girgiza kanta tana fadin wlh Allah bazan iya ba infita da wannan rigar agaban uncle hmmmm anya kuwa zan iya bin yanda suhaila tace tafada tana kara kallon kanta tatuna da maganar suhaila kindaisan uncle bayason kunasa kananun kaya hasalima yatsanesu da alama ta kicigaba da sanyawa irin wa yanda ada bazaki iya zama dasuba ko falo tokisanya kifito agabanshi hakan zai tunzurashi yaji so yake yasakeki tu idan kingama wannan. Roll din kikirani zangaya miki Abu nagaba anya kuwa zan iya iman tafada bayan tagama tuna yanda sukayi da suhaila gaskiya bazan iyaba zandai kira suhaila ta gayamin abunda zanyi nabiyu inji idan zan iya hijabb dinta tasanya kan kayanta tafito domin yanason tadan zaga gidan dakin dayake kusa danata tashiga wow dakin yayi mata kyau sosai domin komai nadakin farine kan bed din takwanta tanajin nushadi acikin ranta talumshe  idonta 


Aliyu da tubdazu yadawo Gidan yashiga wunka yafito daure da towel akugunshi Sam bailura da mutum akan gadonshiba yazare towel dinnanshi saidai iman tabude idonta jin motsi adakin datake tunanin bakowa idonta baisauka ko inaba sai akan Aliyu dayake tsaye bakomai ajikinshi 


Wata irin kuwwa tabuga Wanda tasnya Aliyu kallon gadon nashi 


Tsananin tashin gankalin da Aliyu yashiga yasanya Aliyu nufar wurinta batareda yadauki towel din yakare jikinshiba iman kuwa ganin yanufo wurinta ahaka yasanyata mikewa dagudu zatabar dakin taku daya yadamkota damin shi Sam yama manta da bai maida towel dinba....... 


Kaka kara kaka 

I love you all my fans

💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋

No comments