Breaking News

MY UNCLE 16

 Page 16

Aliyu dabaibawa maganar ta salim wani mahimmanciba yace, Malam idan zaka rubuta mana magani karubuta mana , Zan ruhuta mana amma kasani akwai lokacinda maganin bazaiyi amfaniba ,Saidai kaidin karan kanka!!


Wannnan kuma zance kakeyi Aliyu yafada 


Hakadai salim yaruhuta musu maganin ciyon marar  atarema sukaje suka siyo sanda suka dawo har ankaita dakin Hutu babu jimawa tafalka dai2 su Aliyu sundawo Dr salim yaruhuta musu sallama suka wuce gida


Basu jima da isaba bakon nata ya iso😄dama kuma tana dan ciyon Mara amma  na wannan watan saiyasha banban da sauran 

 

Wannan kenan

****************

Kwanaki sundan ja har bakon nata yayi mata sallama yafece tacigaba da al amurranta domin ita har mantawa takeyi wai akwai igiyar auren Aliyu akanta 


Aliyu kuwa ciyonshi sai abunda yakaru amma sabida taurinkai yaki ya nemi iman asasanta sai kara jida kaima dayakeyi 

Ko sakar mata fuska bayayi yayi tafiya abuja wurin aiki yakai sau biyu acikin watannan


******************

Yau saura wata daya iman ta tare Gidan Aliyu sai kara gyaranta aunty keyi domin wani irin shu'umin turare aunty tasa aka kawo mata daga Niger turaren wani irin sirrine dashi domin gudun matsala ma aunty bata bata turarenba ta ajiye ahannunta sai ranar daza akai iman Gidan Aliyu shima idan tashiga Gidan kafin Aliyu yashigo zata shafa 


Drawer aunty ta janyo tasanyashi sabida tsaro badan tsoroba 😜


***************

Yau Saturday bamakaranta su iman nagida gashi islamiyyarma sunyi Hutu aunty batanan tafita imance kawai sai salma 


Ganin komai nagidan sun kammala iman taci wani mayen wanka na English Wear kayan sunyi matukar karbar jikinta 


Riga da wandone wandon yabi fatar jikinta saika rantse da Allah ajikinta akayishi sai rigar itama tayi mata kyau kasancewarta mai karamin hannu powder kawai tashafa da Dan kwalli sai man baki amma masu karatu kuzo kuga wani masha hurin kyau datayi masha Allah ko hula bata sanyaba kawaidai ta taje kanta tayi parking dinshi tasakoshi har gadon bayanta kayan nata maroon ne shiyasa kalar ta amshe jikinta sosai abunka ga farin mutum


Sanin Dan masifa bayanan kanta tsaye tafito falon salma naganinta tace


Wow masha Allah wlh mom kinyi kyau (haka take kiranta wani lokacin idan nakwaran na kanta)

Masha Allah irin wannan kyan haka ai sai kirikitamin uncle takarasa fada cikin zolaya 


Iman kam tabe baki tayi tana cewa kanki akeji 


Har kuma tazauna tatuna ba agyara dakin aunty ba Dan haka tanufi dakin tafara tsabtaceshi tagyara gado tana kan gayaran gadon taga dan kunnen aunty dan haka tadakko tajanyo drawer aunty tasanya harzata rufe idonta yakai kan wani turare dayayi matukar daukar hankalinta dan haka ta janyoshi takaranta sunan dake jiki bata fahimci ruhutunba sai kawai tashiga feshe jikinta dashi domin kamshin yayi mata sosai Wanda tagama wanka da turaren lungu da sako najikinta sannan tamayar tanajin wani irin nishadi nashigarta 


Tafito falon salma batanan tashiga daki tana fitowa wazata gani uncle nan danan kuwa tanemi natsuwarta tarasa 


Bakinta narawa tace uncle inawuni kallonta yakeyi from up to down sa annan yatabe baki ke maza kawo ruwa kintsaya kina kollona kinsamu TV agabanki sususu tawuce yabi hips dinta dakallo yanajin yanayin jikinshi nacanjawa gawani fitinannen kamshi dayake kara tada mishi da hankali yarasa ta ina kamshin ke fitowa ruwan takawo mishi aikuwa fitinannen kamshin yakara yo mishi sallama har zata juwa yakirata ke zonan 


Bamusu kuwa tajiyo amma kuma bata daga daga wurin datake ba 


Kobaki jiba 


Ahankali take matsowa kusa dashi kamshin nakara kai mishi ziyara aikuwa yayi saurin fizgo hannunta akan tsautsayi bata dire ko inama sai akan faffadan kirjinshi wani irin shock gaba daya yakaimusu ziyara iman tashiga kokarin barin jikin nashi 


Aliyu dagaba daya kamshin yabirgita mishi kwakwalwa yakuma rikita mishi lissafi yayi saurin sanya hannayenshi ya kara rungumota jikinshi kamar zai tsaga jikinshi yasanyata 


Iman dataga abunda yafi karfinta tashiga kokawar kwatar kanta amma ina takasa


Jikinshi har rawa yake unexpected yayi saurin hada bakinshi da nata


Salma data fito falon danjin iman shuru tayi mugun gani tayi saurin komawa inda tafito


INA MAIBAKU HAKURI MASOYA LITTAFIN MY UNCLE KUNJINI SHURU KWANA BIYU MUNDANYI BIKINE AMMA YANZU KOMAI NORMAL ZAKU DINGA JINA KULLUM 


I love you all my fans

No comments