Breaking News

MATAN HAFIZ 19

 19.

Cikin gigicewa da tsoron tsawar da doctor blessing take mata yasata sake fashewa da kuka ta na durqushe sosai kan qafanta, ta furta 

"to doctor na amince amman dan Allah kimana haqurin zuwa safiya inbamu kawo kudinba saiki koremu kinga yanzun inmun dauki abbun mu mun tafi dare ne qarfe biyu da mintoci fa nasan ko abin hawa wuya zai mana"!.


hararta doctor blessing tai tace " jinyi s'a ni mace ce mai son abu mai matuqar kyau dan haka kije kinci albarkacin tsantsar kyawunki yarinya, amman kisani gobe 11:nasafe inbaku kawo kudin aikin nanba nazo kada kuyi mamakin wulaqancin dazan muku, mtsww mutane HK kuke kodan kunga mai asibitin na tausaya muku yanawa wasunku aiki har kyauta?! to shidin bainan ni kuma daidai nake da kowane qaramin dan iskan talaka, talakawa kunada kudi kuki fiddowa ayi muku magani Amman said ku tsaya kunai musu dogon buri, mtsww dalla bacemin da gani 


"dasauri ko ta miqe tabar wajen ko ganin gabanta batayi, can wajen asibitin ta nufa tazauna qasan wata baranda ta had'e kai tana kuka, gaba daya duniyar jitake tana mata yawo a idanunta, dudda dare ne harya raba alokacin amman Sam ko alamun bacci babu a idanunta.


daqyar ta samu ta rarrashi kanta ta lumshe idanunta tana hadiyar kukan nata kanta jingine da wall din gun tana karanta kowace addua tazo bakinta ta samun nutsuwa. 

jitai an dafata gamida furta


"basmah"


dasauri ta bude idanunta jin muryan amminta, cikin dabara ta goge hawayenta gamida qaqaro myrmushi. 


zuba mata idanuwa amminta tai tace"basmah bazaki daina kukan nan haka ba ko? ciwo fa ba mutuwa ake bane tun jia da muka zo asibitun nan kike faman kuka yakamata ki sarara wa zuciyanki kinji dan Allah, insha Allah jikina yana bani malam zai tashi kiyi haquri,

ajiyan zuciya basma ta sauke gamida furta kiyi haquri ammuna wlh bansan snda kukan ke zuwa ba, sosai nake tausayan abbun mu, ammuna cutan  nan na matuqar wahalar dashi kiduba fa ammu ko numfashi daqyar abbu yake saukewa ga zubar jini a jikinsa ammu shiba mace ba komi ba, kuma Yaya tunda yatafi bai dawo ba naje wajen doctor na roqeta suyi masa aikin nan inyaso kodaga baya ma biya ko ma ni su riqeni anan din harsai mun biyasu amman sunqiya ammi..kasa ida mgnr tai ta rushe da wani sabon kukan mai jijjiga jiki.

zama ammun tayi kusa da 'yar tata takasa furta komi gaba dayansu suka shiga zurfaffan tunani rayuwarsu ma.


*Suwaye Ammu da Abbu da Yaya da basmah ne?*


Mlm Muhammad Osama ladan haifaffen qasar Cameron ne gaba da baya uwa da uba da 'yan uwa suna can, koda Mlm Muhammad Osama ladan yatashi mutum ne mai matuqar nacin neman karatun addini hakane yasa yatashi cikin tsantsar ilimin islama wanda kankacemi a shekarunsa a aduniya kusan 58 yazama babban malamin da duk yankinsu babu Wanda bai sansa ba a fannin ilimin Islam, tafsir tafsir wa'azuzzuka dasauransu shima ba'a barsa a baya ba, matarsa guda daya mai suna maryamu, wacce yaranta ke kiranta da ammu, sosai yake gudanar da koyawar sa makarantu2.

saidai akwai wani cuta da Mlm Muhammad Osama ke fama da ita tun tashinsa  Amman bata ta'azzara ba saida girma ya fara shigarsa snn.


to koda ya ankara da ita saiya fara ziyartar asibitoci karbar magani cikin ikon Allah saigashi dayasha magungunan shiknn yakan samu sauqi, musamamn wani doctor Hussain daya daurasa kan magunguna masu dausashe cutar.

Yaran mlm Muhammad osama 2, namijin shine mus'ab sai macen basmah, Mlm Muhammad nazuwa  cikin yankaunan garuruwa domin gudanar da kasuwancin sa, 

sai yai yan kwanaki snn yadawo gida.

cikin ikon Allah sai gashi yasami uban gida suna siyar da hatsi a nan kano, dawasa da wasa har abokin Mlm Muhammad Osama ladan wato Alhj muttaqa yajawo ra'ayinsa kan yadawo nan da iyalansa a garin kano din da zama,a memakon jeka kadawo dazai tayi kusan kullum Inda kasuwancin nasa yafi qarfi anan kano din.


saigashi Mlm Muhammad Osama ladan baisami Marsala ta fannin iyayensa ba suna samusu albarka adawowarsu kano din. 

Ahj muttaqa mutumin kirki ne matuqa kowa ya rabesa saiya ji dadi, dan haka ganin aminin nasa mlm Muhammad osama ladan yadawo kusa dashi, shida kansa ya basa kyautar wani gidansa mai dakuna hudu da girman tsakan gida da qatuwar baranda ga famfo a cikinsa haddda rijiya , daga wajen gidan kuma akwai baranda mai girma, Mlm Muhammad Osama ladan yayi godiya sosai haka suka cigaba da zama cikin aminci.


ahaka suka kwashe kusan shekara yayinda Mlm Muhammad Osama ladan ya bud'e makaranta dud bayan sallar isha'e kullum shi Mlm Muhammad Osama ladan ke koyarda mutane manya nan a kofar gidan nasa hadda Alhj muttaqa kuwa cikin daliban, 

wato yanda kasuwancin Alhj muttaqa da Mlm Muhammad Osama ladan ke tafiya shine ,shi Alhj muttaqa ke kawo kaya shikuma Mlm Muhammad Osama ladan ya karba ya rabawa abokan kasuwancin su in an siyar saiya basa nashi kason, sai gashi da kudaden da yake samu a wajen Alhj muttaqa dana hannunsa shima saiya kama qaramin shago ya saka kwanikan hatsi wato su gero dawa alkama,


 shi kuma alhj muttaqa saiya qara masa da kyutar buhu 2 na masara 1 na  ridi daya na wake, shima ya fara cin gabn kansa dud shekara kuma yana komawa Cameron yayi noma snn yadawo wajen iyalinsa.


 ashekar 2020 ne Allah ya amshi ran iyayen Mlm Muhammad Osama ladan Wanda suka rasu ata hanyar 'yan fashi da makami da suka dirarwa yankin shiyyarsu sukai kashe kashe suka kwashi dukiyoyi sukai gaba.


sunji mutuwan abbu har suma yai lkcn da lbrn ya iske su SBD tsabar firgici,amman haka aka share makoki watansu guda da dawowa kano shida iyalinsa bayan rasuwar iyayen nasu sai kuma babban amininsa Alhj muttaqa shima ya amsa kiran mahaliccinsa ta hnyar hatsarin mota a hanyarsa ta dawowa daga fatauci a birnin gwari, sosai mutuwar ya girgiza Mlm Muhammad Osama ladan dan har rashin lfy saida ya kwanta ta kwana 2, haqiqa yayi babban rashi na aminin qwarai dud duniya baida amini na  qut da qut kamrsa, yayi kuka yayi masa addua da fatan halinsa na gari ya bisa dan haqiqa bashi kadai ba ya sheda alherin Alhj muttaqa garesa kowa ma ya sheda, kowa kaji yabuda baki yabon sa ake.


(damn ance shedun duniya sune ba qiyama Allah kadatar damu amin)


wata 5 da mutuwar Alhj muttaqa tsohon ciwon Mlm Muhammad Osama ladan ya taso gadan gadan Wanda har saida suka dangana da babban asibiti dadyn Hafiz, likitoci sun sheda aiki za'ayi masa a fidda masa cutar dake cikinsa wacce take sashi zubda jini kuma kudin aikin zai kama dubu 300 gashi basuda gaba basuda baya, dan d'an jarin Mlm Muhammad Osama ladan din baifi dubu 100 ba a yanzun, hidimar rayuwa ga dawainiyar karatun iyali da sauransu sai dai godiyan Allah, mus'ab babban dan Mlm Muhammad Osama ladan Wanda shekarunsa 31  yana mataki na qarshe a karatunsa na digree yayinda maibi masa itace basman a shekarunta ynzu 19 tana matakin qarshe na secondary school wnn knn.


a yanzun haka tun jia da likitan yasheda musu kudin aikin mahaifinsu sukai yanke Shawara shi mus'ab da mamansa kan yaje can gida Cameron ayiwa gonar ta kudi wacce ta gada a wajen babnta konawa yakama asiyar yakawo kudin saisu biya, to tun jia da azhur yatafi amman har yanzun washe garin ranar har gashi dare ya qara shigowa amman shiru kakeji bai dawo ba, kuma cikin awannin da aka dauka za'aiwa Mlm Muhammad Osama ladan aiki saura awa daya shi baccin da aka qara musu lkc zuwa safiyan gobe da basusan ynda zasuyi ba.


*cigaban labarin*

 

ammi da basma sun yi jugum jigum bayanda basmah ta shedawa ummun ynda sukayi da doctor blessing ynz suna

jiran hukuncin Allah,

 gashi babu mai waya a cikinsu bare a kirasa aji lfy( Dan ita basmah babnta yahanata amfani dawaya yace saita gama karatu zai siya mata)

daqyar ammi tashawo kan basma suka tashi daga bakin darbejian sukayo alwala gamida gabatar da salla kan wata baranda da majinyata ke hutawa a wajen sunyi addu'a sosai kan samun lfyn abbu.

sunanan har saida sukayi sallan asuba gari ya waye basma tasiyo musu kalaci wajen asibitin sukayi snn

suka wuce  dakin da aka kwantar da Mlm Muhammad Osama ladan danasa a hannunsu, har lkcn kwance yake komotsawa bayayi sosai, saidai yakalli wnn ya kalli wnn saikuma ya rufe ido, cikin boyewa basma ke share hawayenta da dogon hijab dinta kanta a qasa.


cikin dabara ammi take basa kalacin , luddai  3 yai na koko daqyar snn ya koma ya kwanta2


Wuzin 10 na safe nan daliban Mlm fa sukaita zuwa musu yamai jiki da dan alherinsu, sam basuji labarin kudin da ake nema ba tabbas da sai sunyi masa karo karo to ba'asin shine sam ahalin Mlm din basuda tabi'ar roqo shiyasa ammi bata d'aga mgnr ba bare basma.

su daliban sunzata rashin lfy ne daine ke damun Mlm din nasu, fatan samun lfy da addu'@ sukai ta masa dud Wanda yazo, basmah kuwa kadan kadan zata dubi agogon hannunta tana kallon lkc fashewa tai da kuka sanda taga saura 1 hour qa'idan korarsu asibitin ya cika.

 


a can gidan Hafiz kuwa daqyar yakirasu yashe musu halinda aje ciki, jin dasukayi heema ta farfado amamn babu labarin ciki yabi ruwa, murna kawai zee keyi yadda sufa a kan gado, dasauri fateema tanufi shashin zee domin ta kai mata guman heema(dan a zatonta ita kadai Hafiz yakira ya sheds wa)


nan taji zee nata dariya hadda kyakkyatawa ga alama waya ma take, labewa fateema tayi tan sauraronta, nataji zee nabawa qawarta lamra labarin  wato haqarta ta cimma ruwa na ruwan kilin dataje ta watsa a matakalan bene sanda taji Heeman naqoqarin fitowa daga dakinta, dankomi gabn ta akai tundaga sulmiyowanta a bene kawo shigowan Hafiz a gidan, danhaka ranta wasai tashiga zuba zance hadda mgnr dataiwa fatiman na qarya cewa Hafiz baison haihuwa.

ba tabar gunba saida taji zee ta gama wayan, sosai Fatima ta shiga kidima, da tashin hankali,lallaima wato ita wnn muguwar matar zata yaudara, gashi ta riga ta banbanka ma cikinta kwayoyin hana haihuwa, 


"tab to wlh saidai ayi mutuwar kasko na rashin haihuwa agidan nan, yadda ban haihu ba ba shegiyar da zata haihu kuwa daga wnn lkcn".

abinda Fatima ta furta knn tabar gun.

fateeam kuwa  daman Hafiz ya bata umarni ta shiryo wa heema abinda zataci dan  haka tai amfani da wnn damar  cikin kakkauran tea din data hadawa heema hadda wasu mugayen qwayoyin lalata mahaifa gaba 1 ta saka  mata a ciki tana dariya a fili take furta

"yanda nasha kwayan nan nima  babu wata shegiyar dazan bari ta dauki ciki a gidan nan( in Baku mnta ba masu karatu sanda zee keyin wayan qarya kwanki ai fateema tajita tana fadar cewa Hafiz baison haihuwa to tun daga lokacin ita fatiman tazata da gske ne tajetasha wasu magunguna Nasu na likitocin wanda haihuwa sai illa masha 'Allah, to daga baya sai ta  fahimci anya ba qarya Zee takeyi mata ba, duba da ynda taga yake tarairayan yaransa sultan da sultana, sai ynz dataji gskian zance a bakin zee zarginda tk mata ya tabbata.

qutawa tai tana share qwallan baqinciki dan haka data gama girkin a yanzun tafakaici idon zee tajuye mata nata maganin a abinci wato cikin miya,

dayake tuwon shinkafa da miyan agushi tayi musu hadda asibitin, danhaka qwayar ma datasawa zee irinta heeama ce, daukan abincin tai har daki takaiwa zee uwa basune sukai fada dazun ba,zee kuwa ta yatsine fuska uwa bataji dadin ganin   abincinba, nankuwa noqewa tai dan cikinta fall yunwa, dan haka fatema na fita ta hau zaqar abincin nan ba ko bismilla uwa Allah ya aikota, saida ta cinye tas nan tayi gyatsa tamaida kayan kicin ta dawo tai kwanciyarta tana charts hankali kwance., 


Fatima ta shirya tsab ta dukar basket din abincin ta fito tashige motarta direct tanufo asibiti zuciyarta cikeda mugun quduri.


Hafi kuwa tun bayan daya samu yajanye qafansa daga Inda suka hadu da yarinyar nan yanufi dakin da aka kwantar da heema zuciyarsa kwata2 kamanin yarinyar taqi goge masa, sai yaji ma yana kwadayin sake son ganin baby face din nan nata da sound dinta  


"bkm nayafe maka" 


abinda yatuno knn a mgnrta  dashi 1, 

samun kansa da d'an sakin murmushin kasan lebe yai,

 ga alama yarinyar nada sauqin hali,


 ahaka yashiga dakin da heema ke ciki yanayi yana waiwayan ko Allah zaisa yasake *gamdakatar* da ganin yarinyar amman shiru dan HK jiki a matuqar sake sanyaye ya qaraso bakin gadon da heema ke kai, kallonsa heema tai kawai sai ta fashe da kuka danta tabbata babu cikin jikinta kuwa dudda qwallafa rai datai dashi itama,....

zama Hafiz yai gamida kamota zaune ya rungumeta tsam a jikinsa yana d'an bubbuga bayanta alamun rarrashi...karar wayarsa yasashi dan janyewa daga gareta, ganin hajiyarsa CE yasadhi saurin barin gun, waje ya fita ya daga wayar nan take cemasa taga missed Cull dinsa ynz lfy? Nan yasheda mata hinda heema take ciki, sosai hjyn taji tausayin heema dan haka tacewa Hafiz gatana zuwa asibitin ta dudata, dan a lokacin ma yakeji daga bakinta ashe dadynsa yayi tafia Egypt. Ajiye wayan yai yana shirin juyowa ya koma dakin heema idanunsa suka sake hango masa yarinyar dayake mararin sake gani a rayuwarsa, sosai yayi mamkin yanda ya hangeta tawuce tana share qwalla, kan yayi wani motsi sai gashi Fatima ta 6ullo a gabansa hannunta dauke da basket din kalacin su, saida ta gaishesa hadda masa yamai jiki snn tawuce dakin da take tunanin heema na ciki, yayinda shi kuma yajuya Inda yarinyar take bai ganta ba, aqalla yayi 3 mnt yana dube dube bai hange ta ba, d'an tabe baki yai gamida daga kafafunda alamun oho harzai juya kmr ance ya kalli setin wata darbejiya, aiko canya hangota  ta hade kai da  qafa alamun kukan takeyi, tsura mata ido yai sosai daga nan Inda yake tsaye yana hangota, 


lumshe idanunsa yai lkc daya yaji shigowan text message a wayansa, zaro wayan ya duba, major general dinsu ne me Neman sa a barrack ynx, abinda saqon ya qunsa knn,


motsa red Lip's sa yai gamida shafar kwantaccen sajen fuskarsa Wanda keta sheqi. 

fararen idanunsa ya sake saukewa a kanta daga nan Inda yk tsaye bacin maida wayansa a aljihun jeans din jikinsa na kakin sojoji dayai had'da rigarsa da facing cab dinsu,


"mike da munta to?!!!"


 tanbayr dayaiwa zuciyarsa knn a farko. 

zuciyarsa na tunanin shin yaqarsa gunta yaji damuwarta koko Yakoma wajen heema dan qara rarrashinta akan rashin da sukayi???




*To readers insha Allah nan zamu tsaya a labarin Matan hafix sai Allah yakaimu angama azumi snn zaku sake jinmu insha Allah mun dawo gareku.*


*Allan datar damu albarkar dake cikin watan Ramadan amin ya karbi adduo'inmu ya yafe mana yabiya mana buqatanmu na alhreri amin*👏🏼


*Bissalam🤝🏻*




*By 4 writer's😍*

No comments