Breaking News

MATAN HAFIZ 18

 18.

Isarsu hospital din keda wuya emargancy aka shiga da hema, a qalla manyan likitoci kusan 5 ne kewaye da ita suna dubata dan yanda jinin nata keta qara cigaba da 6ul6ulowa. Hafiz kuwa banda sintiri babu abinda yakeyi hankalinsa tashe dudda likitoci 'yan mata na hospital din nata neman shisshige masa da rangwada kodan yaje ya wanke jinin dayai fata fata da rigarsa Amman Sam baida wnn nutsuwar

"it's OK tanz" 

abinda ke rabasu dashi knn haka suka gaji suka bar wajen gwiyoyi a sace, dan matuqa Hafiz ke matuqar firgitasu da tsantsar kyaun da Allah ya haliccesa dashi kamarshi ya tsarawa kansa shi, babu macen dazatai arba da handsome army man din nan bata firgita da bugun zuciyan soyayayrsa farad daya ba, saidai rashin ganin fuska ne yasasu basu iya bayyana masa soyayarsu a fili saidai a aikace, hakan na daya daga cikin abinda yasa Hafiz bai cika ziyartar asibitin dadyn nasa ba domin dazarar sun qyalla ido sun gansa zasuyita masa zarya aka da tambyar miyakeso akawo masa ne.


dan qaramin tsoki yaja bayan bin bayan doctor hafsa dayai da harara data bar gun musamman da ita tafi takura masa acikinsu, haushinta yaji yaqara mamaye masa zuciya gani dayai mutum na cikin tension suzo su qara masa wani, a qalla Hafiz ya sake share kusan 3 hours snn yasamu ya zuqunna akan qafafunsa idanunsa a lumshe red lips dinsa  na motsawa alamun addu'a yake a ciki .

dan har yagaji da trying number dady Amman bata shiga may be ko wani uzurin ne yanasa isowa asibiti a lokacin, dasauri ya miqe ganin doctor blessing mele  ta fito daga dakin da aka shiga da heema sauran doctors din na biye da ita a baya, har office dinta tajasa taimasa nuni da have a st, bayan yazauna gaba daya hankalinsa na gareta, babbar likitace qwararriya ata fannin matsalar mata Wanda shekarunta zasukai 55 a yanzun Amman tsabar hutu yasa bazakai tunanin takai hakan ba zasuyi kusan sa'a da momynsa.


Hafiz yakad'u matuqa dayaji tana sheda masa zubewar cikin dake jikin heema dudda sunyi iya qoqarinsu amman Allah bai yarda ba,

wanda dole suka ida yi mata wankin ciki ynzun tanacan tana barci sakamakon alluran da suka samata a drip   kuma sun bata bedrest na tsawon sati guda domin samun nutsuwar mahaifarta. 

sosai idanun Hafiz suka kad'a jajir kawai sadda kansa yai a jikin table din gabansa zuciyarsa na fat-fat, har ga Allah ya qwallafa rai a cikin jikin heema domin yanada son yara a rayuwarsa matuqa, jin ynda doctor din keta tausarsa yasashi lumshe ido gamida had'iye wani busassan miyau.

 tunowa dayai Allahn daya basa wnn din shi zai sake bashi wani, sosai yake jan adduo'in tausan zuciya a ransa snn yasamu qarfin gwiwan Barin office din  bayn yasamu excuse din shiga room din da aka kwantar da heema din, sosai yake cigaba da tausar zuciyarsa ahankali yake takunsa uwa wani patient  don idanunsa na qasa kawai da zuciyarsa yake nakaltar inda zai dosa zuciyarsa babu cikakken dad'i.

babu zato yaji sunyi karo da juna kamin ya dag'o yaji an furta sautin 

"washhh Allah na abbu"!!!

dasauri yakai dubansa gabansa dudda baiga fuskarta ba dan a lkcn durqushe take a gabansa sakamon turo qofan da yayi zai fito daga office din doctor blessing ita kuma ta zo shigowa kowanensu Yakama handlng din kofan Amman shi yarigata fara turowa  mafarin knn gegen for head dinta ya dan bugu da qofan harta duqe qasa tana cigaba da furta wash idanunta a runtse tana yarfe hannnu lkc daya hawaye nabin kuncinta batareda ta sanma suna zubowa ba, zuba mata sanyayyun idanuwansa yai dake saqe da damuwa still gamida dan duqowa gareta tana furta "sorry bansan akwai wani a wajen bane.. dasauri ta miqe tunowa da halin da mahaifinta keciki tuni zafin ciwon ya dauke mata lokaci daya suka dubi juna.


wani irin mummunan bugu zuciyar Hafiz tai lokaci 1 yaji numfashinsa na masa seizing dan cin karo da asalin kyakkyawr fuskar yarinyar dayai wacce kalarta yayi kama da usulin Fulani camaron..kasa cigaba da mgnr dayakeyi yai ya tsaya can yana binta da kallo..

siraran labbanta yaga sun motsa a hankali daqyar yaji ta furta"bkm nayafe maka"

ganin datai yayi tsaye a hnya yakasa wani kyakkywan motsi sai binta da kallo yake uwa maison gano wani abun a jikin baby face dinta, aikam da sauri zagaye sa tawuce zuwa office din doctor blessing tana shiga tayi kneeling a gabanta murya na rawa ta fara furta

"dan Allah doctor ki taimaka aiwa babana aikin nan wlh kuwa da zarar kawuna yadawo zamu biya kudin, please doctor kitaimaki rayuwar abbuna,

wlh ko aikin sharar asibitin nan naku ne zanyi muku koda kawuna baidawo ba da wuri har mu biyaku kudin ku barema nasan yayana zai dawo n...daka mata tsawa doctor blessing tayi gamida furta "hey stop girl, oya get out ko angaya miki nan wajen wasa ne?, to bari kiji I swear to Jesus nan da 1 hour in baku kawu dubu 300 nanba ba aikin babanki zamu tarkataku ne muyi plshing naku a waje dan nan ba asibitin mahaukata bane...nonsense girl   I say get out"!!!!





*By 4 writer's*😍

No comments