Breaking News

JAMI'IN DAN SANDA 7

 👨🏻‍🔧  *JAMI'IN 'DAN SANDA*.  👨🏻‍🔧

7

...................da k'yar suka samu tarin ya lafa mashi , ruwa yaya sulaiman ya d'auko ya bashi ya sha sannan ya d'auko magungunan shi yabashi ya sha , da yake akwai mai sa bacci aciki baijima bacci yayi awon gaba dashi , 

Ajiyar zuciya suka sauke dukkansu yayinda suka tsurawa Baban nasu idanu kowanensu zuciyarshi kamar zata fashe saboda k'uncin da suke ji a zukatan nasu,


Baba Inno tana daga gefe ta zuba uban tagumi cikin matukar damuwa , tarasa yadda zatayi da malam don ganin ya cire wannan damuwar a ranshi amma abun ya faskara , tanajin tsoron ta koma rasa mijinta bayan rashin 'yarta da tayi, saboda abun ya ta'ba malam sosai fiye da tunani gashi har damuwar tana barazana ga lafiyar shi,


Tashi Hadiza tayi tafara yan aikace aikacen gidan inda tayi shara sannan ta dora masu girki ,shama'u kuma ta had'a kwanikansu tafara wanke wa , yayinda yaya sulaiman ya tashi ya fita shagonshi , 

Sulaiman yana sana'ar dinkin tela Kuma Alhamdulillah yana samun abunda yarufawa kansu asiri dashi don shi yake dauke da nauyin gidan gaba daya , rashin lafiyar Baba ne yasa yanzu yarage fita shago saboda shi yake kula da Baban don jikin nashi yy tsanani sosai,



...........................................


"Hello Alhaji "

" Wai kina ina ne tun d'azu ina nemanki "

"Alhaji muna asibiti fa"

"Ke da wa kenan"?


Wasu yawu ta had'iye kamun cikin rawar murya tace "Alhaji Amna na kawo fa ,na gayamaka jikinta  yayi tsanani sosai"

"Da izinin wa kika fita " 

"Haba Alhaji wai mi kakeyi hakane , *Amna* fa nake gayamaka batada lafiya , ya kake abu kamar wanda baya cikin hayyacinshi , to ina asibiti kuma Ni zan tsayawa 'yata har tasamu lafiya , " tana gama fadin hakan ta kashe wayarta ranta na k'una , tunani take anya mutuwar Zayyan bata taɓa kwakwalwar mijin nata ba kuwa , duk irin tsananin son da yakewa Amna yau itace kwance rai a hannun Allah amma ko a jikinshi, .......



Alhaji Saminu sulaiman kuwa k'asak'e yayi yana kallon wayar , shi Hindatu ta kashewa waya ,lallai ta aikata babban kuskure kuwa ,daga haka ya fito daga ɓangaren yanufi harabar gidan , yana fita securityn shi suka taso aguje suka bude mashi mota shiga yayi gidan baya yayinda suma suka shiga motocinsu suka bar gidan aguje,



...........................................


Zaune yake cikin wani k'asurgumin daji ,dajine mai yawan yalwan tsaunika wanda suka k'awata wajan yayinda suka yiwa wajan wata irin rumfa mai ban sha'awa ga iska mai matuk'ar dad'i na kadawa , 

Zaune yake yayi tagumi yanajin wani irin rad'ad'i na zaga karkashin zuciyarshi abubuwa da yawa na dawo mashi acikin kanshi banda burin daukar fansa ba abinda yake cikin zuciyarshi, 


kamar daga sama ya hangeta tana nufo inda yake ,kallo Daya zaka Mata ka hango tsananin damuwa da tsananin tausayinshi aciki idanunta,


Da sauri ya mike tsaye yana zaro idanunshi yayinda yake nunata da yatsa a hankali ya furta *Momma* 

Murmushinta Mai kyau tayi mashi kamun ta kira sunan da take kiranshi dashi tace *"shalele* "

Da sauri yayi nufin d'aga k'afarshi don zuwa inda take amma abun mamaki sai yakasa koda motsi ne haka ya zuba mata idanu yanason yin magana amma yakasa ,


A hankali tafara magana tana cewa " kayi hakuri Hisham kayi hakuri Allah yana son masu hakuri kuma yana tare da masu hakuri, kabarwa Allah dukkanin al'amarinka shi zai maka sakayya , amma inason kacire burin daukar fansa aranka , ka kula da 'yarka ka kula da 'yarka ka kula da 'yarka.......daga haka tafara ja da baya tana murmushi tare da  daga mashi hannu ,

Yanason yy magana amma yakasa yanason yabi bayanta kar ta koma 'bace mashi amma yakasa yanaji yana gani har ya daina hangota yayinda idanunshi ke zubar da hawayen bakinciki, ..... Kamar an sakar mashi baki haka yaji a firgice ya kwala kiran sunanta "Mommaaaaaa" 

Afirgice ya farka daga dogon bacci da yakeyi  , tuni ya had'a zufa sai maida numfashi yake kamar wanda yayi gudu yajima a haka har yadan yara samun nutuwa a zuciyarshi , 

Yau kwana hudu kenan da yake irin wannan mafarkin , tabbas yazama doli ya kauda idonshi daga mak'iyan  shi ya hakura da daukar fansar , duk da kuwa bashida wani buri da yawuce hakan , zai nisanta kanshi da duk wani abun da zai sa ya tuna baya zai dauki yarshi ya nisanta ta da mak'iyanshi,  wad'an da yasan cewa matuk'ar suka san cewa Muneeba tana raye to tabbas zasuyi k'ok'arin ganin bayanta , zai tsaya mata zai inganta rayuwarta zai k'yalesu badon yana tsoronsu ba sai don ganin ya tseratar da rayuwar gudan jininshi, yajima a haka yana sak'a da warwara yayinda wani irin fushi mai tsanani ya bayyana akan fuskarshi yayinda manyan idonshi suka k'ank'ance suka shige ciki sosai jijiyoyin kanshi suka tashi yayinda mak'ogoronshi ke kaiwa da komowa yana had'iyar wasu yawu masu matuk'ar d'aci , yanajin numfashi shi nayin sama sosai a hankali bakinshi ya bude yafara karanta _innalillahi wa Inna ilaihin raji'un_ ya dauki akalla 30mnt a haka kamun yafara samun sassauci acikin zuciyarshi, 

 duba tsadadden agogon hannunshi yayi yaga k'arfe 3:30 na dare tashi yayi ya fito waje ,tsaye yayi Yana k'arewa wajan kallo , fili ne fetal sai bukkokin fulanin da zaka gani tsili-tsili garin yayi tsit , bakajin komai sai tashin kukan tsuntsaye , alwala yayi yakoma cikin bukkar ya tayar da Sallah , haka yarinka jera nafilfili har akayi asuba ,bayan yayi sallar asuba ne ya koma ya kwanta zuciyarshi cike da tunanin ta inda zai fara,



*Washe gari*


Misalin k'arfe 8:30 ya tashi daga nauyayyen baccin da ya dauke shi , wajen da aka dan zagaye mashi da sunan ban d'aki nan ya shiga ya kama ruwa sannan ya fito ya wanke bakinshi da fuskarshi sannan ya nufi wajan su Baffah,



Suna zaune a filin gidan suna karyawa yayinda Baffa yake gefe yana hada wasu magunguna Hajar na gefe itada Muneeba tana bata d'umamen tuwon da suke karyawa dashi , sai faman wasa take mata suna dariya, 


A hankali yayi sallama ya shigo gidan jikinsa duk a sanyaye , amsa mashi sukayi , har k'asa ya duk'a ya gayar da Baffah da Inna , amsawa sukayi cike da farinciki don Allah ya gani suna matuk'ar kaunar Hisham da tausayinshi , sun fahimci mutun ne mai nutsuwa da hankali ga girmama na gaba dashi sannan a d'an zaman da sukayi sun fahimci mutum ne mai gaskiya da rikon amana ga uwa uba Addini,


"Hamma Hisham ina kwana " cewar Habu da Halliru , amsawa yayi tare da tambayar su aikin da suka tafi yi jiya cikin gari , nan suka shaida mashi komai lafiya qalau, 


Juyawa yayi ya mayar da kallonshi wajan da Hajar da Muneeba suke wadda yana lura da ita tunda yarinyar taji muryarshi take ta zillo tanason ta rarrafo inda yake amma Hajar ta hanata sai faman matseta Take a jikinta tana 'yan harare harare ,  


Yana yin arba da kwanon tuwon da take d'urawa 'yarshi ya had'e fuska cikin tsawa yace 


"keeee wai bana hanaki d'urawa yarinyar nan tuwo ba tunda sassafe sai kinsa tayi k'aton ciki ne, sau nawa zan gayamaki bata isa cin abinci ba , ina madarar da ake bata ne"?


Turo bakinta tayi tace to ai itace takeson cin tuwon nikuma 'ya ta tanason abu bazan hanamata ba ta k'arasa maganar tana murgud'a Dan k'aramun bakinta , 


"Ke Ni kike murgudawa baki lallai bakisan waye Hisham ba ina tausayinki ne wallahi da tuni na 'ballaki oya kuma maza ki saketa tun d'azu takeson zuwa wajena amma kin hanata tsabar kin rainani, ko ?"


Shiru tayi batace komai ba sannan kuma bata saki Muneeba ba duk kuwa da irin yadda yarinyar keson k'wacewa taje wajan babanta don ta saba da Hisham sosai tun bata kai haka ba tafara shaida shi, 


Ganin batada niyar sakinta yasa Inna d'agowa daga gyaran waken da takeyi cikin harshen fillanci tace 

"Wai ke Hajar wace irin yarinya ce miyasa bakyajin magana ne bazaki saketa ba taje wajan Babanta , 


Cikin shagwa'ba kamar zatayi kuka tace 

"Innarmu kina gani fa duk abunda nake ma yarinyar nan bata gani kullum tafinson taje wajan Babanta a kaina to wallahi wataran sai na boyeta ma inda bazai koma ganinta , 


Baffa kam dasu Habu  Banda dariyar diramarsu ba abunda sukeyi don in da sabo yanzu sun saba da diramar Hajar da Hammanta kusan kullum sai sun raba hali akan Muneeba , saboda Hajar tana kishin Muneeba sosai ko kadan batason taga yarinyar na kula wani indai ba itaba shikuma Hisham yana jin haushin yadda take kanainaye mashi yarinya wani lokacin ma ganinta sai yamashi wahala sai ya zare mata ido sannan take sararawa duk da haka kwana biyu zata dawo da halinta ,


Hakanan badon taso ba ta saki Muneeba aikuwa da sauri ta rarrafa sai wajan Abbanta sai faman washe mashi baki takeyi irin na yara ,

D'aukarta yayi ya rungumeta yana bata kiss a goshi yace *sweet heart* kina lafiya ? dariya kawai take mashi , 


Hajar kuwa sai faman hararar Muneeba take tanajin haushin yadda takema Hisham dariya harda kyalkyatawa,


Wajan da Baffa yake zaune ya nufa ya zauna kusa  dashi yace 

"Baffah magana nakeson muyi kuma don Allah inason ka fahimceni Baffah , "


"To Hisham Ina saurarenka" 

Cewar Baffah bayan ya mayar da hankali shi ga Hisham din, 


Sunkuyar da kanshi yayi a hankali yace 

"Dama Baffah na yanke shawarar zan bar wannan jejin ne zan koma cikin gari da zama saboda wasu dalilai nawa , ada naso na zauna anan saboda wani kudiri nawa to amma izuwa yanzu na hakura da duk wani burina inason inyi nesa da idon sani ta ko ina don ganin nabawa 'yata ingantacciyar rayuwa, saboda haka nakeson ka fahimceni Baffah ,


Shiru ne ya ratsa wajan da yake duk suna jin abunda yake fada , Habu da Halliru duk sunyi tsuru tsuru jikinsu a sanyaye don sukam harga Allah basa son rabuwarsu da Hamma Hisham don su murna suke sun samu babban Yaya ,


Kamar daga sama sukaji ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya mai saurare cikin siririyar muryarta mai kama da sarewa tafara fadin 

"Wallahi Allah sai dai ka tafi kai kadai ,haka kawai kullum burinka ka rabani da 'ya ta ai nariga na ganoka  wallahi Allah Baffah saboda Ni kawai yakeson yayi tafiyarshi don baya sona , tayi maganar tana bubbuga k'afafunta a k'asa cike da  shagwa'ba wanda gefe daya Kuma take cike da tashin hankali kar Hisham yarabata da Muneeba ,


Inna ce ta harareta kamun tace wallahi in nak'ara jin maganar ki anan saina tattakaki , shashashar kawai , zumbura bakinta tayi tareda kara fashewa da kuka , azuciye ta juya ta shige cikin bukkarsu ,


Duk abunda take Hisham harararta kawai yake ta k'asan ido , yarinyar tana shige mashi hanci da yadawa ,in banda darajar iyayenta da tuni ya Sa'ba mata kamanni don shi ya tsani yaro sagartacce kuma marakunya to ita kuma yakula anan tafi auki ,


Baffah ne yayi gyaran murya ya dubi Hisham yace .........................✍🏼




Wai wacece mariya???


Wacece kuma Amna 


Wanene zayyan mi akama zayyan da mahaifinshi ke aikata wasu abubuwan kanshi 


Mi ya fito da Hisham daga gidane ???


Su waye mak'iyanshi da suke neman ran 'yarshi 



Hmmmmmmm akwaifa cakwakiya mai girma anan gaba kudai ku kasance tare da Ni don jin yadda zata kaya😍😍😍😍😍


*Aslm sister fatan kuna lafiya , ina matan aure yan mata masu shirin yin aure harma da zawarawa masu shirin shiga daki to ku garzayo nesa tazo kuma nazo maku da ingantattun kayan mata masu kyau da inganci irin wadan da baku saba gani ba , sayen dai dai ko sari ina Sokoto ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah, don neman kafin bayani ku tuntubeni ta wannan number 09035027743 mmn Yusuf Mai kayan mata yar mutan Sokoto sakkwatawa masu maida k'asari zuma*💃🏻👍🏼💃🏻👍🏼


*KARKU MANTA KASAITACCIYAR MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI*👍🏼👍🏼👍🏼👍🏼

No comments