Breaking News

JAMI'IN DAN SANDA 28

 👨🏻‍🔧  *JAMI'IN 'DAN SANDA*.  👨🏻‍🔧

🅿️-28

........................."Ke banason shashanci wani irin zai kashe ki kuma , ? "

"Wallahi momy kasheni zaiyi haka fa yace .....saikuma takasa k'arasawa tuno da gargad'in da yayi mata," uhumm ina jinki yace mi " momy ta tambayeta , "Bakomai momy nidai kawai bana sonshi , " cikin mamaki momy ta tsareta da ido ganin ita ta nace akan tanason Hisham tun ganin farko da tayi masa lokacin da suka kaima hajiya maryam ziyara, wannan yasa cikin hikima ta janyo hankalin hajiya maryam akan su had'a yaran nasu aure don k'ara dank'on zumunci , ta 'boye cewa Samra CE Ke son Hisham din, _anya kuwa yarinyar nan batada aljanu_ ta raya a ranta batare da tasake cewa komai ba ta juya ta fita daga d'akin, direct saman Daddynsu tayi ,


Da sallama ta shiga falon nashi yana zaune akan wani kyakyawan kafen ya kishingid'a da waya a hannunshi yana daddanawa da gani wani yake nema a wayar, zamanta yayi daidai da kara wayar da yayi a kunnenshi , nan yafara magana da Wanda yake kan layin sunjima suna waya kamun suyi sallama ya katse kiran , juyowa yayi ya kalleta da kulawa yace " yadai madam lafiya kuwa na ganki kamar kina cikin damuwa?"

"Hmmm ba doli ka ganni cikin damuwa ba Daddyn samra al'amarin yarinyar nan ne yafara bani tsoro , wai tanacan tana kuka akan batason Hisham bazata aureshi ba , bayan kuma ita tanace akan tana sonshi ,tunani nake  anya kuwa yarinyar nan batada aljanu duba da yadda kwata kwata batada mashinshini ban ta'ba ganin wani saurayi ya biyota yace yana sonta ba, tun bata damuwa har tazo tafara damuwa har kuka takeyi akan hakan, to yanzu daga sama tasamu yaro kamar Hisham amma wai tace bata sonshi gaskiya da walakin goro a miya inaga yakamata a nema mata magani in ba aljanu ne suka aureta ba,tayi maganar cike da damuwa,


Nisawa Daddyn samra yayi yace " wannan ai iskanci ne taya zata maidamu kananun mutane bawani aljanu iskanci ne da ta'bara ni nagaji da zamanta a gidan nan don haka bazan bari wannan yaron ya su'buce mata ba tunda ita batasan inda yake mata ciyo ba" yafada cikin jin haushi , 


Mommy ma batace komai ba don Allah yagani itama batason yarta ta rasa wannan Damar ,wannan yasa ta yanke shawarar tunkarar momma da maganar don Susa lokacin auren anan kusa,


__________________________


"Subuhanallahi ita samra CE tace hakan ? To amma mi yake faruwa naga kamar tana farinciki a lokacin sai kuma yanzu daga baya tabamu matsala ,?"

Daga can aka amsa da cewa " wallahi kuwa hajiya maryam gatanan duk ta rame kullum cikin kuka tun ina daukar abun a wasa har tafara bani tsoro batada aiki sai kuka da damuwa shine nace ko zamusa lokacin auren nan kusa kila in taga an daura auren ta hakura ?"

"Aa hajiya bazamuyi hakan ba ai yanzu andaina yayi auren doli kidai kara lallabata har kisamu ta yarda zaifi yaran yanzu in basason Abu to ba'a tirsasamasu don in aka sasu doli to abun bazaiyi kyau ba," 

"To shikenan zank'ara lalla'bata insha Allah," nan sukaci gaba da tattaunawa kamun sukayi sallama suka ajiye wayar,


Hisham da yake zaune a gefe yana cin abinci tuni ya zubama Momma manyan idanunshi don tuni ya fahimci inda zaican ya dosa , kallonta yake cike da damuwa a fuskarshi kamar gaske acikin zuciyarshi kuwa ji yake kamar ya taka rawa sai dariyar mugunta yakeyi , cikin marairaicewa kamar gaske yace " Momma mi naji kuna fad'a ne ? Badai my samra CE tace batasona ba to amma ni miye abun k'i ajikina Momma , dama irin wannan nake gudu shiyasa banason wannan tallan nawa da kikeyi yanzu gashinan kin jamun zasu wulakantani bayan kuma na kamu da son yarinyar yanzu ya zanyi kenan , yafada kamar zakiyi kuka, 


Dafashi momma tayi tace "karka damu shalele insha Allah komai zaizo da sauki tunda iyayenta naso nasan zasu shawo kanta, (ba doli su so ba tunda zasu yimun shak'e inba shiba wane namijin ne zai kwashi wannan yarinyar da gabad'aya babu kayan wasa a jikinta) ya fad'a a ransa , Sam baisan cewa a fili yafad'a ba saida yaji momna tace " mi kake cewa ,?" Dan daburcewa yayi yace aa Momma cewa nayi akwai abarta tunda tace banyi mata ba kar a tsaurara bincike Ku kyaleta kawai don ni nayi alk'awarin bazan ta'ba auren yarinyar da ta furta cewa bata so na ba , kuma nasan girman alk'awari don haka bazan karya shi ba taje can Allah ya had'a kowa da rabonsa amma tabbas bazan aureta ba tunda har ta furta da bakinta bata sona ,yayi maganar yana had'e fuska sosai ,Momma zatayi magana ya tareta da cewa " don Allah Momma kibar maganar nan Sanin kanki ne bazan taba karya alk'awari ba duk alkawarin da nayi to sai na cikashi kawai kiyi hakuri , "

Cikin sanyi Momma tace to shikenan Shalele dama kai nakeji gashi ka fad'awa soyayyarta karkazo abun yana damunka , Mahaifiyarta kuwa banida matsala dasu tunda ta 'bangarensu ne aka samu matsala," wani shu'umin murmushi yayi tareda cewa " karki damu Momma acin watan nan zan kawo maki yarinyar da zan aura. Nayi maki alk'awari, nan da nan Momma ta washe baki tana cewa to alhamdulillah shalele nasan zaka kawo tunda kace kayimun alkawari Allah yabaka ta gari " yace "amin"



__________________________

Agurguje take shiryawa ta fito tsaf cikin uniform dinta a tsaitsaye ta dauki kunun da inna Inno ta jiye mata tafara sha , batasha da yawa ba ta ajiye ta juyo tana kallon iyayenta tace "Baba Inna ni zan tafi makaranta sai na dawo , "

Atare sukace "to Mariya adawo lafiya Allah ya tsare, cikin jin dadi ta furta "amin amin , " kallonta ta mayar ga Yayanta Sulaiman tace " Yaya na shirya muje ko ," karkacewa yayi ya sanya hannunshi a aljihu ya dauko kudi Dari ukku yabata yace " yau ilyasu baya nan wani uzuri yasa  yafita da mashin din nasa bare na amso na kaiki gadai wannan ki hau nafef kuma ki saye wani Abu kici in antashi insha Allah zanzo na daukoki nasan kamun sannan ya dawo, " 

"To shikenan yaya nagode sai na dawo" tajuya tanufi hanyar fita daga gidan, "anty ki sayomun awara in zaki dawo kinji ," cewar Asmau yar autar Inna inno , cikin murmushi da kaunar 'yan uwan nata tace " to Asmaun inna zan kawo maki insha Allah , daga haka ta fice daga gidan tana sauri don yau ta makara sosai , 

Asmau da khadija ma bayan sungama karyawa makarantar suka wuce inda sukabar Yaya sulaiman sai Baba , Inno tana kicin tana shara yayinda Baba yake gefe shida yaya sulaiman suna tattaunawa , cikin jimamai Baba yace , " to yanzu kai sulaiman ya kakeganin zamuyi nidai banida kudin nan wallahi kasani kaikuma abubuwa sunyi maka yawa naso Mariya ta canza karatun nan amma ta kafe ita sai karatun aikin jinya takeso to ni Ina naga kudin da zanyi mata laluran makarantar dashi , " 

Nisawa yaya sulaiman yayi yace " karka damu Baba insha Allah komai bazai gagaraba , kaga Mariya tanata kokari sosai banason kokarinta yatashi a banza sannan wannan karatun ne kawai zatayi kaga tasamu aiki kai tsaye yanzu ni ba gashi nan ba shekara ta ukku da hada degree na amma aiki ya gagareni sai dinki doli nakeyi , to ita in Allah ya taimakemu tana gamawa zakaga tasamu aikin nan kuma albashinau yanada tsoka kaga  shikenan abubuwa zasuyi mana sauki sosai ,akwai wasu kudi da nake Tarawa acikin asusuna zan fasashi nayi mata laluran makarantar nasan insha Allah zasu isa Allah dai ya shige mana gaba, daga Inna har Baba murna suka farayi don sunason cikar burin 'yar tasu sosai wadda ta taso da wannan ra'ayin ne tun tana k'arama , nan sukaci gaba da Sanya mashi albarka da yi mashi addu'o'in samun nasara a rayuwa yadda yake dawainiya da kannenshi batare da gajiyawa ba yanasa iyayen farinciki da alfahari dashi,


____________________________


Zaune suke a office din Hisham , Baban Safiya ne da k'aninshi sai Babban yaronshi Zakari , nan suka koro mashi bayanin abunda yake tafe dasu da kuma yadda akayi suka zo wajanshi don an tabbatar masu da zasu samu adalci a wajanshi shiyasa direct  sukazo wajanshi, 


Tunda suka fara magana ido kawai ya zuba masu cikin tafasar zuciya ,ba k'aramun bak'inciki yaji ba da suka gaya mashi bayanin da likitan yayi masu na cewa ba mutum d'aya ne yayi mata fyad'e ba ,tunanin yakeyi irin azabar da zai ganama wad'an nan azaluman idan yakamasu , ga tausayin mahaifin yarinyar ganin yadda yake zubar da hawaye da tsufanshi da komai cikin k'wafa da takaicin abun  yace  , Inason Ku kawomun yarinyar da abun yafaru agabanta yanzu sannan samarin da sukace sunga lokacin da aka dawo da ita suma inason ganinsu , nan da 40mnt , nuna zakari yayi yace "kai zan hadaka da yaranmu biyu kaje ka kaisu inda abun yafaru daga nan kuzomun da samarin da yarinyar , kaikuma Baba inason ka kaini asibitin yanzu inason ganin yarinyar da kuma likitan da ya dubata , " cikin farinciki duk suka mik'e ganin yadda ya kar'bi k'orafinsu hannu bibbiyu ba zancan wulakanci ko yawo da hankali , wani sanyi sukaji acikin zukatansu don suna ganin kamar ma an kama masu laifin angama,


Lokacin da Hisham yaga Halin da safiya take ciki saida yaji kamar ya zubarmata da hawaye har lokacin bata cikin hayyacinta don data farka da bige bige da ihu da sambatu take farkawa wannan yasa suke banka mata alluran bacci , yaso yasameta acikin hankalinta don doli akwai tambayoyin da yakeson ta amsa mashi , haka dai ya hak'ura doli ya nufi office din likitan, 

Likitan na ganinshi ya mik'e tsaye tare da bashi hannu suka gaisa cikin mutuntawa , nan yayi wa likitan bayanin abunda yake tafe dashi,

Murmushi likitan yayi yace " nasani yalla'bai hasalima ni nabasu shawarar su damk'a case  din a hannunka ko zasu samu adalci Don wallahi an cutar da yarinyar nan cuta mai yawa Wanda sai tsananin rabo ne in zata rayu sunyi mata raga-raga da mutuncinta cikin rashin imani , wallahi na tausayawa iyayenta sosai , zan baka sakamakon binciken da akayi mata ka gani , nan ya dauko wani file ya mik'awa Hisham yana kara yi mashi bayanin abunda Ke ciki, 

Hisham gyad'a kai kawai yakeyi idanun nan nashi sun kad'a sunyi jawur fuskarshi ma tayi ja sosai kallo daya zakayi mashi kasan cewa yana cikin tsananin fushi da tafasar zuciya, Yajima a office din kamun yayi ma likitan sallama yabar office din , nan yabar su Baban akan zai nemesu in bukatar hakan ta taso,


______________________________


Daga asibitin ofishinsu ya koma ,koda yaje har Zakari yazo da yarinyar nan maisuna haulatu k'awar safiya dakuma su iro mai shago, da hannu kawai yayi masu alamar da su biyoshi , da sauri suka mik'e tsaye sukabi bayanshi , yana shiga ya d'ane kujerarshi yana jiran shigowarsu ,


Jiki a sanyaye suka fara shigowa bakinsu dauke da sallama Don sun tsorata da yanayin shi sosai kallo d'aya sukayi mashi suka tabbatar da ba wasa acikin al'amarinshi,  a hankali ya amsa sallamar tasu batare da ko su sunjishi ba , tsaye sukayi suna jiran suji abunda zaice , jikinsu sai k'yarman tsoro yakeyi musamman ma Haulatu , gyara zamanshi yayi tare da sassauta fushinshi Don ya kula sun tsorata dashi yace " Ku zauna tambayarku zanyi kuma Ku tabbatar kun sanar dani abunda kuka sani, Da sauri suka gyada Kansu alamar amsawa , ta kan Haulatu yafara , kallonta yayi yace "ki gayamun abunda yafaru daki-daki a wancan ranar , sannan ki gayamun abunda zaki iya shaidawa agame da mutanen , "

Cikin hawaye tafara bashi labarin abunda yafaru tun daga farko tashinsu daga makaranta har kawo sanda suka dauke safiya, jinjina kanshi yayi yace " to zaki gane samarin su nawa ne ?? Sannan zaki iya gane mutanen in kika gansu ? "

Cikin rawar murya tace " aa bansan kosu nawa bane amma zan iya gane d'aya daga cikinsu Wanda shine ya fito ya janyota motar , jinjina kanshi yayi yace " to bayan wannan ba abunda zaki iya tunawa , ? Cikin tabbatarwa tace " *narik'e number motarsu yalla'bai* " 

Cikin jin dadi yace wow good yan mata kinyi kokari maza rubutamun number anan , kindai tabbatar da itace ko ?" 

"Eh yalkabai ", to da kyau maza rubutamun , saida ta rubuta ya dauka ya duba sannan Yakoma kan samarin suma dai tambayoyin yayi masu kamun ya sallamesu su tafi , zakari sai dadi yakeji gani yake kamar ma ankama mai laifinnan sai jinjinama Haulatu yakeyi da har tayi kokarin rik'e number motar,


Wunin yau gaba daya Hisham akan wannan case din yayi shi sai misalin goma na dare sannan Yakoma gida bayan yagama duk wani bincikenshi kuma yagano ko suwaye masu laifin jira kawai yake gari ya waye ya kaddamar masu don sai ya gurfanar dasu agaban koto saidai duk abunda zai faru yafaru, 

Wanka yafarayi bayan yaje gida sannan ya ci abinci kamun yayi shirin kwanciya , kamar daga sama tunaninta ta ya fad'o mashi sai kyakkyawar fuskarta keyi mashi gizo ,wani sanyayyan murmushi ya saki Wanda baimasan lokacin da yayi ba a hankali ya furta Preety kinada kyau, 

Tunawa da yayi cewa yanada number ta yasa ya dauko wayarshi yafara kiran layinta ba tare da yasan abunda zai CE mata ba, a hankali wayar tashiga kuma duk bugun da zatayi dai dai yake tafiya da bugun zuciyarsa, a dai dai wannan lokacin kuwa Laurat na zaune adakinta abun duniya ya dameta ko yau saida Abbansu ya titsiyeta akan ta fito da mijin aure inba haka ba lokacin da ya diba mata ya cika to zai bayar da ita ga Wanda yaga dama ba ruwanshi, tayi zurfi cikin tunani kamar daga sama taji ringing din wayarta , a hankali ta dauko wayar ganin bak'uwar number yasa ta share wayar har ta katse sai da aka sake kira sannan ta dauka , cikin sanyin muryarta ta furta " *Assalamu Alaikum*" wani luuuuu yayi da idanunshi jin muryarta har tsakkiyar kanshi....................nagaji tunda ko comment bana samu😼😼😼😼😼




*wlh nakusa mayar da book dina na kudi akan rashin comment dinku musamman yan GRP din *Jami'i fans 2  da maman Yusuf fans da sauran grps saidai duk Wanda yakemun comment to zancigaba da bashi a kyauta Don dama banyishi da niyar siyarwa ba amma da biyu babu gara daya*


____________________________


Mmn Yusuf Dr mata sokoto




💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 *ASLM GANI FA NA SAKE DANNOWA DA SABBIN KAYA MASU SABON SALO*💃🏻💃🏻💃🏻


*takuce mmn Yusuf Dr mata mai gyaran mata ciki da wake*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻


Ina uwargida da Amarya ina masu shirin yin aure budare da zawarawa , ina masu son su zama taurari ✨🌟ababen alfaharin mazajensu , ina mata masu kishiyoyi da ake ci masu zarafi ake wulakantasu akan kishiyoyin su ina wacce keshan wulakancin namiji , ina matan da sukeson burge mazajensu da zallan ni'ima da dandano ??? Ina matan fake fama da rashin ni'ima , budewar gaba wadan da suka faru sanadin ciyon sanyi kokuma haihuwa , ko wadda Ke fama da k'arancin ni'ima da karancin sha'awa , ??  To saurara kiji✋🏻✋🏻✋🏻


Ko kinsan Maman Yusuf Dr mata kuwa ?? Hmmm akace in bakasan gari ba to ka saurari daka,💃🏻💃🏻

*Namu na dabanne kamar yadda salonmu yake daban ingantattun kaya ne da basuda wata illa ajiki sannan ba boka ba malam zaki mallaki mijinki da dandanonki sai yadda kikayi dashi*


Duk abunda kk so a bangaren kayan mata zaki samu hajiyata daga gyaran ciki harma Dana waje 


Munada ingantaccen maganin sanyi na maza Dana mata hakama maganin Basir 


Maganin nono Dana hips 

Maganin kiba dakuma maganin rage tumbi da kibar, 

Maganin gashi 

Maganin hawan jini

Maganin sugar


Sabulun wanka na gyaran jiki

Sabulun dilka na amare

Dilkar amare


Kwallin mallaka (daga ni sai kai)

Maltinar mata

Bobintan mata

Set na lalata gindin kiahiya

Set na ukku bala'i

Set na rantse bakida kishiya,


Kalolin gumba

Kalolin gari

Kalolin matsi

Kalolin sabulan tsarki

Zumar mata

Zumar ridi 

Zumar goron tula

Tsumin mallaka

Tsumin jaraba

Tsumin sabon budurci

Tsumin kankana

Tsumin tabaje

Tsumin makalemata 

Shayin mata 

Sirrikan mallaka

Dan goshi da mahadinshi 

Dan goshi na Mara

Kyallen al'ajabu

Rakumi da akala

Bita zai zai

Dahuwar kalolin kaza zabo zakara 

Dahuwar zuciya

Dahuwar ciccibi

Dahuwar zuciya

Dambun nama

Dahuwar yan shila

Yajin mata 

Yajin maza domin Karin karfi



*Hmmmmmm in nace sai na lissafamuku zafafan kayan nan sai in wuni ina typing shawara daya zan baki uwargida in har baki jaraba kayan mmn Yusuf ba to ki garzaya ki saya da kanki zakizo kina godiya , 😉😉😉😉😉😍 wadan da suka San ya kayan suke kuwa. Basa bukatar wani Karin bayani , 

Domin Neman Karin bayani kokuma ganin kayan da nake dasu Ku tuntubeni ta wannan number 07069711327 call or WhatsApp mmn Yusuf mai kayan mata🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰


Ina bada sari ina sokoto ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah , 

Don Allah in baki shirya siyaba to kibari sai kin shirya sai muyi magana🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 07069711327

No comments