JAMI'IN DAN SANDA 17
👨🏻🔧 *JAMI'IN 'DAN SANDA*. 👨🏻🔧
🅿️_17
_*BAYAN WANI LOKACI*_
.......................... Cikin ikon Allah da iyawarsa yau Hisham Allah ya cika mashi burinshi kuma burin mahaifinshi , yasamu tsananin horo da sanin makamar aiki wanda duk wadanda sukayi aikin tare gaba daya yasha kansu ya zage ya koyi komai da dukkan zuciya wannan yasa yazama gagara badau kuma zakaran gwajin dafi ,inda ya fito a matsayin *babban Sifeta* na wannan yakin ,
Kyakkyawan matashi dan shekara 28 fari ne tas mai cikar zati yanada tsayi sosai da siffar k'arfi , kallo Daya zaka mashi kasan cewa wannan majiyin k'arfi ne saboda yadda yanayin jikinshi ya nuna , gaba daya jikinshi a murd'e yake irin na Jaruman maza , ba k'aramun kyau yakeyi ba acikin *Kakinsu na 'yan sanda* ga wani irin k'warjini da haiba da suke k'ara mashi ,
Lokacin da Hisham ya shigo gidan sanye da kakinshi na *yan sanda* tsaye kawai Momma tayi tana kallonshi ,yayinda idonta suka cicciko da hawayen farinciki , tsawon lokaci kenan bata danya tilon d'anta a idonta ba , saidai tana mamakin irin yadda yak'ara girma da zama cikakken namiji adan k'ank'anin lokaci irin wannan , gaba d'aya takasa wani motsi ganin yadda Hisham ya rikid'e yakoma sak Abbanshi komai da komai musamman da ya saka wannan kakin,
Shima idon ya tsura mata yana murmushi wanda ya k'ara fito da kyaunsa , ganin halin da Momma tashiga ne yasashi k'arasowa da sassarfa ya rungumeta tareda da sauke ajiyar zuciya , itama ajiyar zuciyan tayi tare da saka duka hannayenta ta rungumeshi ta fashe da kuka , don gaba daya takasa rik'e kukanta Hisham ya tuna mata da mijinta tanajin tamkar mijinta ne ya dawo , gefe daya kuma cike take da farinciki Allah ya cikawa mijinta burinshi sannan d'anta yadawo kusa da ita , jan hannunta Hisham yayi sukashiga cikin dakin wanda har lokacin Momma bata daina zubarda hawayen farinciki ba,
"To miye kuma na kuka Momma ? Inace farinciki zakiyi Allah Yasa na dawo gareki kuma da d'umbin nasarori , "
"Doli nayi kuka Hisham narasa mahaifinka kaikuma kayimun nisa , Inna Indo wata biyu kenan da ta koma gida bayan tayi tayi dani akan nabita can gida amma nakasa yin hakan saboda kai , nikad'ai nake rayuwata agidan nan kewa tayimun yawa sosai yanzu kuwa kuka farinciki nakeyi da Allah ya nunamun wannan rana ka gama lafiya , ina rokon Allah da yayi maka jagora akan wannan aiki naka ka kasance mai nasara akan mak'iyanka ,"
"Amin Amin Momma na" yafad'a cike da shagwa'ba , murmushi Momma tayi tana maijin farinciki ,
"Momma nifa yunwa nakeji wallahi don yanzu sam bana jimirin yunwa " yafad'a Yana wani karya wuya,
"To ai laifinka ne shalele da kayi mana zuwan bazata , da ka fad'a ai da yanzu ancika gabanka da kalolin abinci sai wanda ka za'ba, "
"To ai Momma inason inbaki mamaki ne shiyasa , "
"To naji bari naje na samamaka abunda zakaci kafin nan kayi wanka ka huta sai kabani labarin irin nasarar da ka samu ,
"To shikenan Momma Bari naje nayi wanka nazo,"
Wanka yayi ya shirya cikin farar riga da bak'in wando takalminshi ma bakake sai sumar kanshi da ta kwanta luf-luf kamar ya kafa hula tasha gyara sosai sai kyalli takeyi don ba karamin kudi yake kashewa sumarshi ba, in ka gamshi kamar wani Balarabe ko ba'indiye saboda yadda yakeda cikar suma da sil'bi irin ta fulanin asali,
Zamansa babu wuya sai ga Ibrahim ya shigo gidan aguje jin cewar babban Abokinshi ya dawo , aikuwa nan suka rungume juna cike da tsantsar farinciki da kewar juna, nan suka zauna suna firar yaushe gamo ,
"
"Abokina kaga yadda ka koma kuwa sai kace wanda yake rayuwa a cikin k'ank'ara gaba daya yanayinka da komai ya canza , anya kuwa ka maida hankali kayi abunda ya kaika kuwa , yafad'a Yana dariya"
"A'a banyi abunda ya kaini ba dan rainin hankali , kana kallona kasan ba haka na tafiba duk na rame nayi duhu saboda wahala shine zaka wani ce wai nayi kyau "
"Allah abokina bakaga yadda ka koma ga wata irin murdewa da jikinka yayi irin na asalin jaruman maza gaskiya ina tayaka murna don nasan ba k'aramun rububi zakasha ba wajan yan mata yafad'a Yana dariya ,
"Kai mata suka dama" cewar Hisham , suna haka Momma ta fito masu da daddad'an abinci data girkama Hisham sai k'amshi ke tashi , nan suka zauna sukaci suka k'oshi sannan sukaci gaba da fira ,sunjima anan sannan suka yiwa Momma sallam akan zasuje majalisarsu inda abikansu su gaisa ,
A wannan rana daga Hisham har Momma Basu runtsaba kwana sukayi suna firan yaushe gamo yayinda Hisham ya gayamata irin gwagwarmayar da yasha tareda nasarorin da ya damu da kuma irin matsayin da yake a yanzu , sannan nan da sati Daya zai fara zuwa aiki,
Fatan alkhairi sosai tamashi tareda yi mashi nasihohi masu shiga jiki akan duk halin da gaishiga to ya tsare gaskiyarsa ,
*******************
Har wannan lokacin ba abunda ya canza akan muguwar sana'ar da su Alhaji Musa keyi , komai yana tafiyarmasu yadda suke so don ta kowane fanni sunada yaran dake masu aiki, jami'an tsaron dake masu aiki kuwa bazasu k'irguba , shiyasa suke abunda sukeso alokacin da sukeso , duk wanda yayi yunk'urin shiga gabansu kuwa to tabbas zasu kaudashi ko wanene kuwa , ana wannan yanayin ne aka canza D P O Hamza khamis wanda ya kasance yana daya daga cikin wad'an da suke bawa su Alhaji Musa goyon baya akan mugun abunda suke aikatawa , saboda mahaukatan kudin da suke damk'a mashi , wanda shima dasa hannunshi a kisan Jami'i Abdurahaman , wato Abban Hisham ,
Da farko sam basu wani damu ba tunda suna ganin duk wanda za'a kawo shima zasu siyeshi in yaso sai ya d'ora daga inda Sir Hamza ya tsaya , sai dai mi lokacin da aka gabatar da sabon D P O *sir Huzaifa Umar Abdullahi,* sai kallo ya koma sama don sam wannan ba irin wanda suke tunani bane mutum ne tsayayye mai gaskiya da amana uwa uba tsaye yake akan aikinshi sam ko waye kai ka yarda kashiga komarshi tofa sai kasan ka ta'bowa kanka tsuliyar dodo , mutum ne marar tsoro kuma dan kasada ,
Mutum na farko da suka fara tura masa da nufin ya janyo ra'ayinshi alokacin saida ya karya k'afar mutumin sannan yasa aka rufeshi tsawon sati biyu sannan yasa aka sakeshi zuwa lokacin kuwa tuni ƙafarsa ta ru'be banda fitar da ruwa mai doyi ba abunda takeyi ,
Wannan al'amari fa ya tsoratasu matuk'a saidai sun sha alwashin sai sunga bayanshi kota halin k'ak'a kamar yadda sukema duk wani k'aramun k'waron da yace zai kawo masu wargi a harkansu,
*********************,,
Kwance yake gala gala duk ya fita hayyacinshi ,ya rame sosai ba komai ajikinshi sai jijiya da k'ashi gaba daya ciyo ya cinyeshi sai kanshi da yayi wani irin k'ato , idan ka kalleshi doli yabaka tausayi ,
Da k'yar muryarshi ke fita , tun d'azu sai faman k'walawa matarshi kira yake Amma tanajinshi tayi biris dashi sai ma faman jan tsaki takeyi irin ya matsa mata dinan,
Hawayene masu zafi suka zobo mashi ,fitsari yakeji tun d'azu amma matarshi Amina tanajin yana kwala mata kira amma tayi masa banza , bayan duk abinda ya sameshi sanadinta ne , don duk abunda yake samu kanta yake k'arewa duk abunda tagani ko bashida halin siya matashi haka zata yi tsaye tace sai ya siyamata , haka zaije duk yadda zaiyi sai yayi don ganin yasamo kudi yayi mata abunda takeso , don Allah ya dora mashi sonta mai tsanani da wannan take amfani tana juyashi son ranta duk abunda yasamu a gindinta dana yan uwanta yake k'arewa amma shine yanzu don Allah ya jarabceshi take wulakantashi yadda taga dama , bata tausayinshi kokadan ,
Gashi kullum ciyon kanshi k'aruwa yakeyi anyi magani har angaji anzubama sarautar Allah ido , don takai yanzu ko abincin da za'aci a gidan wuya yake masu bare wani kudin magani ,
Kusan kullum sai yayi kuka mai yawa idan ya tuna ya gamu da wannan ciyon ne alokacin da yaci amanar abokinsa , tabbas yasan wannan ciyo nashi *Alhakine* sakayya ce kawai Allah yayiwa Abdurahaman tun ba'aje ko'ina ba , gashi nan shi ya huta ya tafiyarshi shikuma yabarshi cikin tarin sark'ak'k'iya da wahalhalu na rayuwa tareda d'umbin nadama marar iyaka , tunda abun yafaru baikoma lafiya ba inda ciyon yafara yawa ne aka sallame shi awaja aiki acewarsu sai yaji sauki ya dawo to maimakon dauki a'a saima abunda yayi gaba ga matarshi gaba daya ta juya mashi baya ,haka yayita kuka mai ban tausayi , yana tausayin kansa sosai amma yasha alwashin. Sai yasa an nemo mashi iyalan Abdurahaman ya fayyace masu komai tareda neman gafarar su...............✍🏼
😣😣 *yau dai abun bawani armashi wallahi yau banajin typing din sam amma kuyi hkr mutara a page na gaba*😉😉
*SANARWA*🗣️🗣️👇👇👇
*Ina matan da suke fama da butsarin namiji wato namiji marar sakin fuska namiji masifaffe namijin mai wuyar sha'ani , murdadden namiji dakuma namijin dake wulakanta matarshi ko namijin da kikeso amma baya sonki*
*Ko wanda kishiya tasha gabanki sam mijin baya ganinki sai dai kishiyarki to ku garzayo wajen Mmn yusup mai kayan mata domin samun wani taimako wanda ya kasance ingantacce ne wanda ba bokanci acikinshi sai dai tarin taimako ,idan har aka baki wannan taimakon to insha Allah kekam matsarki tazo karshe zaki samu mijinki a tafin hannunki zai kasance baya ganin kowace mace agabanki zai kasance mai tausayi da jin kai a wajanki , zai kasance mai sauraranki da baki* *lokacinshi akoda yaushe zuciyarshi zatayi laushi akanki duk wani zafin kai nashi to zai sauka da izinin Allah , wannan taimakon 3000 ake badashi wadda ta shirya to tamun magana ta pc ko kuma akira numbar kai tsaye , duk wadda takeso zatamun magana ne sai na mata cikakken bayani akan abun don wannan bayanin nayishi ne kawai a tak'aice, don* *Allah in baki shirya ba karkimun magana mu batawa juna lokaci kibari kin shirya sannan*🙌🏻🙌🏻
09035027743 call or Whatsapp mmn yusup sokoto,*
*Karku manta ba tsibbu ko bokanci acin harkarmu Ayar Allah ce kawai*🥰🥰
*Maison taci gaba da samun wanna littafin akan lokaci ga link Nan tayi join Amma don Allah in baki karantawa karkishi inkuma kinsan bakya iyayin comment nanma karkishiga don Allah*
No comments