Breaking News

DUK NISAN JIFA 21

                           21

Yace "Yanzu na bugota, ka san kuwa du irin kud'in da du daya ta kama min? Sannan na yi postern news d'in cewa ga ranar d'aurin aurenka a dukan grups na manyanmu, haka kuma na turawa abokananka da kuka yi karatu tare suma sun ce suna ta neman layinka wai ko baya shiga ko me, harma da wanda ya ce ko amarya ta rik'e wayar." Ya k'arashe yana yar dariar shakiyanci du burinsa ya kular da shi.


Sai dai abin mamaki sai ya ga Ya yi masa dan murmushi yana ajiye ambulope din yace "Ka yi k'ok'ari sannu."


Kader ya yi sakayau da baki yana kallonsa, da sauri yace "Ka kuwa ji me na ce? Takardun gayatar aurenka na bugo fa?"


A hankali Hisham ya dafe gaban goshinsa , muryarsa a sanyaye ya ce" Eh na gane Kader, bana son hayaniya ne ya sa ban karanta ba aman na san ai zaka rubuta komai yanda ya dace."


Kader ya ringa kallonsa, cen ya ce "Hala wani abu kake shirya yi mana ranar auren da zaka saka mu sakankancewa kan ka yarda da auren dolen?"


Shi har ga Allah sai abin na Kader ya fara bashi daria, sarai ya san so yake ya kula shi su yi ta zuba hauka bayan shi a yanzun karfinsa ya kare a tunane tunanen da ya aurawa kansa, yau kwana uku kennan ruwa a jalo nemansa ake a asibiti aman ya yiwa sakatariarsa kwakwaran kashedin cewa baya nan, kar ta yarda ya ga wani ya zo gidansu nemansa, hakan ya sa takr cikin tsaka mai wuya domin ita ke tatare masu neman nasa.


Komawa ya yi zai kwonta hakan ya sa jikin Kader ya mugun mutuwa, dama karfin hali ne yake so yake ya saka shi sakin jikinsa ta wannan hanyar, sai gashi ya ki yarda ya bashi damar da yake so.


A sanyaye ya sauka kasa ya zauna yana kallonsa, muryarsa sanyaye yace "Ka ce ka hak'ura, ka ce ka barwa Allah komai , kuma sai kake wannan yannayin da bana so? Dan Allah ka mike , Hisham bayan Aisha fa kana iya kara mace uku domin hudu aka halasta maka, a kan me zaka ringa haka a gabana a gabansu ka ringa shuka masu iya shege? Yanzu dai a gidan nan ba wanda baya tsoron ta hado ku dan ka zama fitsararen karfi da yaji, sakin magana kawai kake son ranka, haba Hisham Bilkisu idan rabonka ce ko bayan Aisha bayan wasu matan zaka malaketa, kar ka shiga hakkin Aishar nan dan na kula tana da sanyin hali, kai maimakun ka ringa murna zaka rabu da kayar kwana rabin ido a bude rabi a rufe da nauyin mara, zaka samu falalar ladan mai aure, kuma shine kake irin haka?"


Hisham ya bade fuskarsa ya juya bayansa da hoton nan a hannunsa ya ki bashi amsa


Tun Kader na sa tan zai waiwayo shi har ya mike ya juya ya fice a dakin jikinsa a mace


Direct baban falo ya shiga, ya gaishe da mai aikin dake goge goge sannan ya nemi da ta masa magana da Mama


Mama cikin hijab dinta har kasa ta fito ta karaso wajensa da kulawa take amsa gaisuwarsa


Sannin cewa Tati da sabuwar kawarta kuma sarakuwarta sun tafi kasuwa ya saka shi zama a kasa ya sada kansa


Muryarsa a sanyaye ya ce" Walahi du yanda na so ya kula ni mu yi rigima ta gagara, Mama kina kallo za'a ilata maki yaro dan kawaici? "


Da mamaki Mama ke kallonsa, a sanyaye ta ce" sai nake gannin kalamanka basu dace da wanda kake yiwa furucin ba, dan zai yi aure shine ila a tare da shi ko dan zai yiwa mahaifiyarsa biyaya? Shin Aishar dauke take da wata cuta ko wata nakasu a tare da ita da zai saka ya ringa haka? Idan baya so ya gudu mana irin yanda yan mata ke yi idan za'ai masu auren dole sai na ga karshen rashin kunya, Haba Kader, yaya kuke so na yi ne? Rashin fara'arsa sarai ya san tana ilata ni, aman sai ya ringa wani shasha min kanshi? Wai idan ina da ikon hanna abin nan da ba tuni na hanna ba? Yaya kuke tunanin ina iya yin kokowa da abinda ya fi karfina? "


Zata ci gaba da magana wayarta ta dauki kuka


Tana dubawa ta ga sunnan mahaifin Bilkisu


Dagawa ta yi ta yi salama sannan ta dan saurara tana sauraron sa


A sanyaye ta ce" Ita Bilkisun ce ta ce zata zauna har a kusa auren yayanta? Auren fa sauran sati biyu fa , makarantarta fa? Yayan nata zai yarda ne? "


Dukan tambayoyin nan da ta yi na nuni da hankalinra ba a kwonce yake ba, hakan ya saka Mahaifin na Bilkisu kallonta a hankali ya ce" Asma'u ko da wata matsala dake faruwa da Balkina ne? "


Da sauri Bilkisu ta kalli mahaifinta, hakama Mama da dan sauri ta ce" Aa, aa fa ba komai ba abinda yake faruwa "



Aban su Bilkisu ya ce" To gani na yi kamar kin manta inda ta zo ne Asma'u "  


Mama ta sauke ajiyar zuciya ta ringa motsa bakinta tana son cewa ya bata Bilkisun aman ta gaza


Bilkisu ce ta ce" Abana bani maman "


Abanta ya bata wayar yana kallonta


Mikewa ta yi ta matsa gefe ta zauna ta sanyayar da muryarta ta ce" Mama "


Mamanta ta ce" Ya maki kyau, na ce ya maki kyau, ahine zaki ce wani zaki zauna a cen me yake baki da ya wanda nake baki? Bilkisu am meye hakan? So kike karara a gane dan auren yayanki kika yi gudu daga gidan nan ko me? Shine zaki ringa hadani da wancen yana wani yi min dogon bayani kou? To ba ruwana zan fadawa yayanki idan ya zo ya taho da ke ai shikenan!"


Bilkisu ta sanyaya muryarta sosai ta ce" Mamana, ba haka bane, mama walahi ina samun nutsuwar zuciyata sosai tare da Mami da Abana da Hamana na nan gidan, mama kin ga mu yi karatun sade mu yi da yama, mu zauna mu yi hira da Abanmu, mama zan dawo aman so nake sai auren ya kusa sai mu zo da Mamina a yi bikin da ita, ta ce zata zo ta kwana har mu yi shagalin bikin, Mama itama aurenta saura sati uku yanzun aman haka ta ce zata biyo ni, dan Allah mamana kar ki ce aa "


Mama ta sada kanta a hankali ta ce" To karatunki fa? "


Bilkisu zata yi magana mahaifinta ya janye wayar domin dama biyota ya yi ya kara a kunnansa ya ce" Kin ji kunya, haihuwarki ta farki kina  irin haka da yarki ta farko Asma'u, to karki manta nine ubanta kuma karatun nima na yi, abin alfaharina ne ta zama likitan nan domin tun yanzu da ina ciwon kai ita ta rubuta magani aka siyo kuma na warke, ki fita a harkar y'ata da ni ko na amshe abata ai kin san na maki kara, kuma dama dama ni ba marar kunya bane "


Mama ta yiwa wayar kit tana zaro ido, 

Ido hudu suka yi da Kader da komai a kan kunnayensa ya wani yi mata kuri 


Fuska ta kara hadewa tana cije lebenta ta ce" Tashi ka tafi ka ji? Allah ua maku albarka baki daya "


Kader ya sada kai yana murmushin mama ya mike ya fita


Yana fita Aisha dake jiran ya tafi ta fito ta tsuguna gaban mama kanta sade ta ce" Dan Allah mama ki yafe min, walahi ni dai ba ruwana a cikin maganar auren nan, mama dan Allah ki yafe min ki hanna auren nan, walahi kina iya hannawa domin idan kika ce kar ya yarda ba zai yarda da maganar auren ba, du da kika ga ana wani ja'in ja dan kin hana shi bijirewa ne "


Mama ta kara dafe kanta tana kallon Aisha ta ce" Aisha bakya son yarona ne? "


Aisha ta dago ta kalli mama, da sauri ta sada kanta, dan Allah yana ganni idan kunya ce ta sarakunta ita ta mama take ji, hakan ya saka bata iya sakewa da ita


Mama ta yi murmushi ta ce" Tashi ki je ki sha maganin zahin da na dafa maki kin ji? ki yi ta adu'a domin wani baya auren matar wani"


Aisha ta gyada kanta itama jiki a sanyaye ta koma dakinta


Kwonci tashi kwana nesa

Wasa wasa auren Hisham har ya rage saura kwana biyu kawai

Yau tun da safe su Bilkisu suka zo ita da yar uwarta, tun da suka zo kuwa ta aniya lalaba mama har sai da ta bata ky din motarta nan ta dauki Mami da Atm cart dinta suka fita

Basu zame ko'ina ba sai shagon Elhaji Ayuba lhabille, 

Zama suka yi Bilkisu ta ringa daukan masu rantsatsun lesuka da shadoji da mayafai yan madaidaita da takalma da jaka, 

Aun cashi kudi a shagon nan wanda sai da Mami ta ringa rafka tagumi tana kallonta domin sai da ta hanna aman ta kiya


Daga nan suka mikawa tela Abdu da yake tsalake, ya kuwa zuga masu kudi aman ta tabata zai gama a kan lokaci sannan dinkin Abdu ba na yarwa


Daga nan gidan su laila suka wuce direct, wajen kwanar rahama


Laila ta girgiza jin jibi jibi Hisham ke daura aure, harda hawayenta, sai dai abin mamaki Bilkisu murmushi kawai ta yi ta ce" Haka Allah ya so Laila, ki daina damun kanki na barwa Allah komai"


Mami ta ringa murmushi tana jin kaunar yar uwarta har cikin ranta.


A hanyarsu ta komawa gida ne Mami ta ringa jajen jikinta du ciwo yake sosai, hakan ya sa Bilkisu zuwa asibiti da ita duda ta nuna aa kar su je zai wuce aman Bilkisu ta kiya ta karkata ta kaita, an bata magani irin nasu sannan suka wuce gida.


Duda abin ba a shirya masa ba, ba'a yi wani lamari na bidi'a ba kasancewar kakan amaryar na kwonce asibiti angon kuwa ba wanda ya san inda yake, aman gidan ya cika da manyan bakin da suka yi tataki tun daga garin Niamey dan halartar taron d'aurin auren.


Ana gobe daurin auren gidan ya cika kowa da gayarsa ana ta shagulgula ciki kuwa harda Su bilkisu da kawayenta sun dinke a dakin tsakar gida sunna ta kunshi da kitso abinsu sunna shan daria domin akoy wace ta saka ado gwonja masu zaburi taka sai juyi suke abinsu.


Sai kusan magariba kawayenta suka watse ya rage sai su biyu, an masu kunshi ya yi kyau sosai duda Bilkisu sai da ta hanna a yiwa Mami ta ce ita da aurenta saura sati daya tak ta bari a gwongwaje mata na aure aman fir ta kiya itama sai da akai mata harda kitso masu kyau.


Suna yar hira a gajiye bayan sun gama cin abinci Aisha ta shigo.


Jikinta a mace ta samu waje ta zauna ta rakub'e jikin kujera.


Bilkisu dake kallonta ta lumshe idannuwanta tana jin Mami na fad'in "A'a, har an gama shafa lalen amarsunmu? Wai ina hamman yake?"


Aisha ta kaleta sai kuma ta dan saki murmushi bata bata amsa ba.


Bilkisu ta sauko ta zauna a saman cafet din itama ta turo mata abinci a sanyayye tace "Aisha ci abinci mana?"


Aisha ta d'ago ta tsatsare Bilkisu da kallo, kawai sai ji suka yi ta fashe da kuka mai cin rai.


Bilkisu ta rintse idanuwanta lokaci daya ta mike ta yi waje da sauri har tana had'a hanya.


Karon da suka ci da mutun ne ya sakata yin baya zata fad'i, aman bata kai ga faduwar ba ta ji an wani irrin rikota, rik'o irin na zafi zafin naman nan.


Baki daya ta rintse idanuwanta a lokacin da suka yi ido hud'u sakamakon fad'uwar da gabanta ya yi.


Kallonta yake, jelar kitson da akai mata duda manya ne a bayane sai kunshin da ta sha ja wanda ya fitar da ainahin kyanta.


A hankali yace "Kwaliya kike a aurena?"


Bilkisu ta tsurawa fuskarsa ido, hawayen da take na k'ara bin kumatunta.


Wani irin haushinsa take ji na haka kawai, hakan ya sa ta tsatsare shi da idanuwanta tanai masa kallon eh d'in yi abinda zaka yi!


A hankali ya saketa ya raba gefenta ya wuce ciki hakan ya sakata nufar wani daki ta bude ta shige ta kwonta.


Yanda ta ga rana haka ta ga dare, har kusan k'arfe taran dare idanuwanta bud'e suke a saman abin sallah tana kallon gabas.


Shelar sunnan burinta hade da na watanta ana maimaita d'aurin aurensu ya sakata kwontawa a hankali tana sauke ajiyar zuciya.


Wani murmushi mai ciwo ne ya kwace mata, a hankali ta kara gyara kwonciyarta kanta na sarawa tana jan carbi har baci mai nauyi ya kwasheta.


Mami kawai ke kai kawo a d'akin da take kwonce bayan ta samota da kyar, har sai da ta kusan wuni tana bacin nan kafin ta farka , Mami ta tsatsareta ta yi wanka ta saka shadar da suka yi iri d'aya.


Mami ta sakata kimtsa fuskarta sannan ta kamata ta mike tsaye tana kallonta tace "Bamu yi haka da ke ba Balkisa."


Bilkisu ta yi murmushi tace "Nima ban yi haka da zuciyata ba, aman yanzun da na yi bacin nan komqi ya warware, na ji sauk'i sosai a zuciyata."


Mami ta yi murmushi tace "Kin ga cenjin da muka yi na kyautar da zaki ba amarya, kina tunanin zaki iya wannan jarumtar kuwa? "


Bilkisu tace "Idan kina gefena, ina mai tabatar maki har rawa sai na taka dan kuwa ina ji ana kidan larabawa kin san na iya kada kugu kuwa?"


Dariya Mami ta yi tace "Ba ruwana mara kunya kawai."


Haka suka fito yan matan biyu, duk da Mami bata da jiki sosai rashin lafiarta baya tab'a barinta yin gwab'i haka ta yi kyau cikin d'inkinta domin sai da ya auna su ya masu rantsatsun d'inkunnan su.


Bilkisu kam abin ba'a cewa komai, du irin yanda gurbin idanuwanta suka kunkumbura bai hanna mata zama wata tauraruwa ba

Walwal take walwali , haskenta yana cika ido.


Marok.a na ganinka suka shiga yi mata kirari, makadan da suka zo dan shafa lalen angon da har yanzu ba'a shafa ba  domin wai yana asibiti tiyata yake da har uku suma suka shiga tarbota da kid'a da busa irin na barebari kasancewar damagaram gari ne na yawancin barebari.


Murmushi ta yi ta k'arasa wajen Tati dake tsaye tana ta yi mata dariyar oyoyo babyna tace "Tati bani mayafin naki na gani?"


Tati ta kuwa bata dan tana son gannin abinda zata yi sai kirarin ga kanwar docter, ga kanwar likita, ga yar shalele ake mata.


Ai kau kamar da almara Bilkisu ta shiga taka rawar barebari wace suke yi da mayafin nan cikin k'warewa da juyi a hankali.


Mama ta zaro ido da sauri ta lab'e cikin mutane tsabar kunya.


Tati kam me zata yi banda daria da murna, ba shiri wajen ya kaure da kari domin kawayen maman Aisha da maman aisha da tati gaba daya suka shiga suka rufeta da karin mik'ak'un manyan yayan banki masu maik'o.


Sai da Mami ta gaji da daria tana girgiza kai ta shiga ta fitar da k'anwarta tana dungure mata kai tace "Ba kya jin magana auta, rawa ko? "


Bilkisu na dariya tace " kema sai kin taka, wai ina uwar ango take bata taka ba."


Mama na ganinta ta k'ara guduwa ciki, dan ita kam yanzun daga Hisham har Bilkisu ta kula sun karo wulak'anci bata cikin abin kunya ba da ita ba!



Haka aka gama tarron biki aka watse, ango tun wajen d'aurin aure ya fece wai yana da aiki daga nan ba wanda ya kuma ganinsa domin baya asibitin kuma baya gidan da akaiwa Aisha jere


          .....................  



            *Auren Mami*

No comments